Kwamishinan Uba Sani Ya Yi Murabus, an Maye Gurbinsa da Sabo
- An samu sauyi a majalisar zartarwa ta jihar Kaduna da ke karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani bayan murabus din kwamishina
- Farfesa Muhamad Sani Bello ya ajiye aikinsa a matsayin kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna a cikin farkon makon nan
- Tsohon kwamishinan ya sanar da murabus dinsa ne a cikin wata wasika da ya rubuta, inda ya godewa Gwamna Uba Sani kan damar da aka ba shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani ya rasa daya daga cikin kwamishinoninsa bayan murabus din Farfesa Muhammad Sani Bello daga mukaminsa.
Farfesa Muhammad Sani Bello ya yi murabus ne daga mukaminsa na kwamishinan yada Labarai kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar Kaduna.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa murabus ɗin nasa yana cikin wata wasiƙa ne wadda aka rubuta a ranar 29 ga Yuli, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamishina ya yi murabus a jihar Kaduna
An aika wasikar murabus din ne zuwa ga sakataren gwamnatin jihar, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Wani bangare na wasikar na cewa:
"Tare da duba ga wasiƙar da ke ɗauke da lamba GH/KD/S/171 ta ranar 27 ga Yuli, 2023, wadda aka naɗa ni a matsayin kwamishina kuma mamba a majalisar zartarwa ta jihar Kaduna, ina so na sanar da kai cewa na yanke shawarar yin murabus a karan kaina daga wannan matsayi daga yau ba tare da bata lokaci ba.”
Farfesa Muhammad Sani Bello ya kuma nuna godiyarsa bisa damar da aka ba shi ya yi aiki a ƙarƙashin gwamnatin Gwamna Uba Sani.
Ya dai fara ne a matsayin kwamishinan ilimi, sannan daga baya aka naɗa shi a matsayin kwamishinan yada labarai na farko.
Uba Sani ya nada sabon kwamishina
Biyo bayan murabus ɗinsa, Gwamna Uba Sani ya naɗa Alhaji Ahmed Maiyaki a matsayin sabon kwamishinan yada labarai.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dakatar da hadiminsa, ya kori Ahmed Musa daga shugabancin hukumar EDOFEWMA
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na Gwamna Uba Sani, Malam Ibraheem Musa, ya fitar a ranar Talata ta tabbatar da wannan naɗin.

Source: Facebook
Kafin naɗin nasa, Ahmed Maiyaki shi ne Manajan Darakta na kamfanin watsa labarai na jihar Kaduna (KSMC).
Ana kallon naɗin Ahmed Maiyaki a matsayin wata dabarar ƙarfafa sashen sadarwa na gwamnati domin ci gaba da aiwatar da manufofin "Renewed Hope" a jihar Kaduna.
Farfesa Bello da aka fi sani da Mainan Zazzau yana cikin manyan APC kuma shi ne Darektan yakin neman zaben Uba Sani a 2023.
Karanta wasu labaran kan Gwamna Uba Sani
- Uba Sani ya aika da sako ga gwamnoni bayan kisan 'yan daurin aure a Plateau
- Uba Sani ya yi martani mai zafi kan kisan 'yan daurin aure a Plateau, ya sha alwashi
- Bayan zuwa Kaduna, Uba Sani ya tabo batun barazanar da Tinubu zai fuskanta a 2027
Uba Sani ya magantu kan tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya yi tsokaci kan tazarcen mai girma Bola Ahmed Tinubu a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Gwamna Uba Sani ya bayyana cewa babu wani gwamna da zai fito ya yi adawa da sake zaben Tinubu a shekarar 2027.
Ya nuna cewa Tinubu ya yi zarra wajen ba gwamnoni da jihohin Najeriya dukkanin irin goyon bayan da suke bukata.
Asali: Legit.ng

