Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'addan Boko Haram a Daji, An Kashe Miyagu

Dakarun Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'addan Boko Haram a Daji, An Kashe Miyagu

  • Dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas sun samu nasara kan 'yan ta'addan Boko Haram
  • Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka 'yan Boko Haram bayan sun yi musu kwanton bauna a wannan karo
  • Hakazalika jami'an tsaron sun kwato kayayyaki masu yawa daga hannun 'yan ta'addan bayan sun fatattake su zuwa cikin daji

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK) sun kashe wasu ‘yan ta’adda biyu na kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun kuma kwato manyan kayayyakin ta’addanci bayan samun nasarar kaddamar da wani kwantan-ɓauna a kauyen Bula Daburu da ke ƙaramar hukumar Bama a jihar Borno.

Dakarun sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Borno
Dakarun sojoji sun hallaka 'yan ta'addan Boko Haram a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Ba dadi: 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun farmaki 'yan Boko Haram

Rahoton ya bayyana cewa wannan samame wani ɓangare ne na Operation Desert Sanity IV, wanda ke da nufin tarwatsa hanyoyin da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen samun kayan laifi.

Majiyoyi sun ce an gudanar da aikin ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025 a wani wuri da ake zargin maboyar ‘yan Boko Haram ne da suke bi don ketarawa.

A yayin artabu da ‘yan ta’addan, dakarun sun yi amfani da ƙarfin da ya fi na abokan gaba, wanda hakan ya tilasta wa ‘yan ta’addan tserewa cikin ruɗani, inda suka bar kayayyakin da suka zo da su.

An kashe ‘yan ta’adda biyu yayin musayar wuta, sannan wasu daga cikinsu suka tsere tare da yiwuwar samun raunukan harbin bindiga.

Sojoji sun kwato kayayyaki masu yawa

Bayan an kammala bincike a yankin, dakarun sun kwato keken hawa guda takwas, buhuna biyu na shinkafa masu nauyin kilo 50, katan na makaroni guda 60, takalman roba guda 60, Injinan fasa ƙarfe guda 10, da tabarma guda 12.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe

Operation Desert Sanity IV wani sabon farmaki ne da rundunar hadin gwiwa kan samar da tsaro a Arewa Maso Gabas ta ƙaddamar, da nufin ƙwace wa ‘yan ta’adda ‘yancin zirga-zirga da katse hanyoyin samun kayan tallafi a duk faɗin yankin.

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram a Borno
Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram a Borno Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojojin sama sun kashe 'yan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'addan ISWAP.

Sojojin saman sun hallaka 'yan ta'adda masu yawa bayan jiragen yakinsu sun yi ruwan wuta kan maboyarsu a jihar Borno.

Daga cikin tsagerun da aka kashe da manyan kwamandoji da mayakan kungiyar ta'addancin wanda ta addabi mutane da kai hare-hare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng