Ba Kunya ba Tsoron Allah, Matashi Ya Yaudari Surukarsa Ya Caka Mata Adda har Lahira

Ba Kunya ba Tsoron Allah, Matashi Ya Yaudari Surukarsa Ya Caka Mata Adda har Lahira

  • Wani matashin magidanci mai suna, Yayu Musa, ɗan shekara 27 a duniya ya hallaka surukarsa saboda ta yi yunƙurin kashe aurensa a Kogi
  • Jami'an rundunar ƴan sa-kai sun cafke wanda ake zargin bayan ya yaudari mahaifiyar matarsa Ummi, ya daba mata adda har lahira
  • Tuni dai aka miƙawa ƴan sanda mutumin domin gudanar da bincike kuma majiya mai ƙarfi ta ce an tafi da shi hedkwata a Lokoja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kogi - Jami'na tsaro sun cafke wani matashi ɗan shekaru 27 mai suna Yayu Musa, bisa zargin kashe surukarsa a jihar Kogi.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8:00 na dare, a ranar Juma’a, a garin Olla da ke ƙaramar hukumar Omala, Jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya.

Magidanci ya kashe surukarsa a Kogi.
Jami'an tsaro sun kama mutumin da ya yi ajalin surukarsa a jihar Kogi Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda magidancin ya yaudari surukarsa

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe

A rahoton Leadership, wani mazaunin yankin ya ce magidancin ya yaudari surukarsa, ƴar shekaru 50 mai suna Atayi Abdul, da cewa wasu mutane na satar amfanin gonarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matar ta bi shi zuwa gonar domin duba abin da ke faruwa, amma da suka isa gonar sai ya caka mata adda har lahira.

A cikin wani bidiyo da rundunar sa-kai ta yankin ta ɗauka bayan gano gawar matar, an nuna yadda wanda ake zargi ya sassari jikin surukarsa bayan ya kashe ta.

Bayan haka, ƴan sa-kai suka bazama wajen nemansa, inda daga bisani suka kama shi a wani gari da ke makwabtaka da su, wurin da ya gudu bayan aikata laifin.

Wanda ake zargin ya amsa laifin da bakinsa, yana mai cewa ya aikata kisan ne saboda surukarsa ta yi barazanar raba shi da matarsa Ummi Idris, saboda rashin haihuwa.

Ummi: Matashin ya faɗi dalilin kashe surukarsa

A cikin wani bidiyon da aka ɗauka na lokacin da yake bayyana dalilansa, Yayu Musa ya ce:

"Surukata ce ta ba ni ‘yarta Ummi Idris na aura, kuma na kashe kuɗi da yawa wajen kula da ita. Amma sai ta dage cewa za ta raba mu da ba wani saboda kawai matsalar haihuwa.

Kara karanta wannan

Cakwakiya: Asirin amarya ya tonu, ƴan sanda sun kama ta watanni bayan ɗaura aurenta

"Na nemi magani domin ta samu ciki, amma Allah bai ƙaddara ba. Har babur dina na sayar don ganin na samu mafita. Duk da haka, surukata ta ce za ta raba ni da ita, ta ba wani.
"Wannan ne ya sa na fusata domin ina ƙaunar matata, ba zan iya ganin wani ya aurenta alhali ina raye ba.”
Dakarun rundunar ƴan sandan Najeriya.
Yan sanda sun karɓi wanda ake zargi da kisan surukarsa a jihar Kogi Hoto: Nigeria Police Force
Source: Getty Images

Wanda ake zargi ya shiga hannun ƴan sanda

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kogi, SP William Ayah, ba a same shi ba domin jin ta bakinsa kan lamarin, rahoton Guardian.

Wani babban jami’in ‘yan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an tafi da wanda ake zargin zuwa Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Wani ya sari tsohuwar budurwarsa a Borno

Kuna da labarin wani matashi, Abubakar Ijidai ya farmaki tsohohuwar budurwarsa da mahaifiyarta yayin da suke aiki a cikin gona a jihar Borno.

Abubakar ya sari tsohuwat budurwarsa da adda, ya kuma yi ajalin mahaifiyarta a gundumar Dille, da ke jihar Borno ranar Asabar da ta wuce.

Rundunar 'yan sanda dai ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, kuma za ta kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi gaban kuliya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262