Ana Zaman Ƙeƙe da Ƙeƙe tsakanin 'Yan Arewa da Jami'an Gwamnatin Tinubu a Kaduna

Ana Zaman Ƙeƙe da Ƙeƙe tsakanin 'Yan Arewa da Jami'an Gwamnatin Tinubu a Kaduna

  • Ana gudanar da taro a Kaduna don tantance yadda gwamnatin Tinubu ke aiwatar da alkawuran da ta dauka tun 2023
  • Ministoci da jami’an gwamnati za su bayyana a gaban wakilan jihohin Arewa 19 don kare nasarorin gwamnatin
  • Gwamnatin Tinubu na fuskantar suka daga 'yan Arewa da ke zargin rashin wakilci a mukamai da ayyukan raya kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - A yau Talata 29 ga watan Yuli, 2025, aka fara babban taron da zai bai wa ministoci da manyan jami'an gwamnatin Bola Tinubu damar bayyana irin ci gaban da suka samar.

Taron, wanda kungiyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation (SAMBF) ta shirya, na gudana a Kaduna kuma zai kunshi wakilai daga jihohin Arewa 19 da sauran jami'an gwamnati daga Abuja.

Kara karanta wannan

Noma: Hadimin Buhari ya goyi bayan Tinubu, ya fadi kuskuren da aka samu a zamaninsu

Dakin da ake taron 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Bola Tinubu
Dakin da ake taron 'yan Arewa da jami'an gwamnatin Bola Tinubu. Hoto: Sunday Dare
Source: Facebook

Ma'aikatar yada labarai da wayar da kan al'umma ta wallafa a X cewa za a shafe kwana biyu ana taron.

Babban manufar taron ita ce tantance yadda gwamnatin Tinubu ke cika alkawuran da ta dauka tun lokacin kamfen a 2023, musamman wadanda suka shafi ci gaban yankin Arewa.

Za a duba ayyukan gwamnati a Arewa

A cewar shugaban SAMBF, Abubakar Umar, wannan taro cigaba ne da tattaunawar da aka fara kafin zaben 2023 tsakanin yan takara da jama’ar Arewa.

Premium Times ta rahoto ya ce:

"Taron zai taimaka wajen kimanta ci gaban da aka samu kan alkawuran da aka dauka, da kuma karfafa hulda tsakanin gwamnati da al’umma."

Kungiyar ta bayyana cewa hakan zai kara wayar da kan jama’a kan manufofin gwamnati tare da wanke shakku da ke tattare da aiwatar da tsare-tsaren gwamnati.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnati na mayar da martani kan sukar Arewa

A ‘yan kwanakin nan, wasu manyan ‘yan siyasa daga Arewa, ciki har da Rabiu Musa Kwankwaso, sun nuna damuwarsu kan yadda suke ganin gwamnatin Tinubu na watsi da Arewa.

Kara karanta wannan

'Yan Zamfara sun huro wuta, suna so Dauda Lawal ya sauka daga kujerar gwamna

Kwankwaso ya ce akwai nuna wariya wajen aiwatar da manyan ayyukan raya kasa. Wannan kalami ya janyo martani daga Ministan Ayyuka, David Umahi, wanda ya ce zargin ba shi da tushe.

Umahi ya ce gwamnati na ci gaba da aiwatar da manyan ayyukan hanya da wasu muhimman tsare-tsare a Arewa kamar yadda ake yi a sauran yankuna.

Ana sa ran bayanai daga jami’an gwamnati

Taron na kwana biyu zai kunshi jawabai daga ministoci da sauran jami'an gwamnati kan fannoni da dama da suka hada da tsaro, tattalin arziki, noma, abinci, da ayyukan more rayuwa.

Rahotanni sun ce gwamnatin tarayya na daukar wannan taro da matukar muhimmanci, ganin yadda ake ta kokawa daga wasu bangarori na Arewa.

Kungiyar SAMBF ta ce tana fatan wannan tattaunawa za ta zama wata kafa ta samun fahimtar juna da inganta alakar gwamnati da jama’a.

Tinubu ya yaba wa 'yan wasan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yaba da kokarin 'yan wasan Najeriya mata na Super Falcons.

Bola Tinubu ya jinjina musu bisa nasarar da suka samu a wasan da suka yi da kasar Morocco kuma suka lashe kofi da ci 3:2.

Shugaban kasar ya ce ya shiga fargabar kallon wasan a karon farko saboda tsoron hawan jini kafin wasu su kunna talabijin a dakin shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng