An Fara Zanga Zangar Fatattakar Ƴan Najeriya a Ghana, an Faɗi Laifuffukan da Suke Aikatawa

An Fara Zanga Zangar Fatattakar Ƴan Najeriya a Ghana, an Faɗi Laifuffukan da Suke Aikatawa

  • Wasu yan kasar Ghana sun fara gudanar da zanga-zanga, suna zargin wasu 'yan Najeriya da tsafi da kuma lalata da 'yan mata
  • Masu zanga-zangar suna dauke da alluna, suna cewa yan Najeriya na jawo sace yara, barna a kasuwanni da kuma cin zarafin 'yan kasa
  • Wata mata da ta yi magana a bidiyon ta ce 'ba za ku zo ƙasarmu ku dinga aikata komai ba', 'Yan Najeriya dole su tafi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - An fara zanga-zanga a kasar Ghana domin fatattakar wasu yan Najeriya da ke aikata laifuffuka.

Wasu yan Ghana sun gudanar da zanga-zanga game da 'yan Najeriya da ake zargi da shiga harkar karuwanci da kuma amfani da mutane don tsafi.

Ana zanga-zanga a Ghana game da yan Najeriya
Yan Ghana suna zanga-zanga domin fatattakar yan Najeriya. Hoto: TikTok/Ghanablog.
Source: TikTok

Ghana: Musabbabin zanga-zangar korar yan Najeriya

A cikin wani bidiyo da ya karade intanet ranar Talata, an ga masu zanga-zangar dauke da alluna masu rubuce-rubuce iri-iri, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun fafata da ƴan bindiga, an cafke wani baƙon ɗan ta'adda a Yobe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu daga cikin allunan sun ce dole a dakatar da fashi da kai farmaki haka, karuwanci da barazana ga lafiyar mutane.

Sauran sakonnin sun hada da:

“’Yan Najeriya na sace mutane suna amfani da su wajen al’amuran sihiri, 'ya’yanmu na bacewa saboda ƙabilar Igbo.”

Sun kuma nuna hoto na wani mutum da ake zargin wani dan Najeriya ya kashe shi a yankin Accra na kasar Ghana.

Wata mata da ta bayyana mai kimanin shekaru 30 ta ce:

"Yan Najeriya dole su tafi saboda halin da suke nunawa, Ba za ka zauna a kasar wani kana aikata komai yadda kake so ba, yan Najeriya dole su bar ƙasar nan."

Wani dan zanga-zanga ya ce:

“Yan Najeriya sun kwace kasuwanninmu kuma suna aikata mummunan abu iri-iri a kasar mu.
"Wadannan Igbo sun mamaye ko’ina kuma sun kwace kasuwanni. Ba Igbo kadai ba, kowane dan Najeriya yana cikin kauyukanmu, doka ba ta amince da baki su rika aikata miyagun laifuka a ƙasar mu.”

Kara karanta wannan

2027: APC ta tsorata da ake shirin kawo sauyi kan zaɓen shugaban ƙasa, gwamnoni

“Har ma suna da Sarki Igbo a Ghana. Sun mamaye filayen mu. Nan ba da dadewa ba za mu kwace kasar mu.”
Yan Ghana suna zanga-zanga kan barnar da yan Najeriya ke yi musu
Yan Ghana suna zanga-zangar fatattakar yan Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ghana: Menene ya faru a Najeriya a 1983?

Za a iya tunawa cewa a shekarar 1983 gwamnatin Najeriya ta kori kimanin baki miliyan biyu ciki har da yan Ghana marasa takardu.

Marigayi tsohon shugaban kasa a wancan lokaci, Shehu Shagari ya ce:

“Idan ba su tafi ba, a kama su, a gurfanar da su, sannan a mayar da su kasashensu.
“Wanda ya shiga kasa ba bisa ka’ida ba bai kamata a ba shi sanarwa ba. Idan ka karya doka, za ka biya diyya.”

Wannan mataki ne ya haifar da yayin “Ghana Must Go” da yan Ghana suka dinga cika jakunkuna da kaya yayin da suke barin Najeriya.

A yayin hada wannan rahoto, gwamnatin Ghana ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin da kuma matsayarsu kan korar ’yan Najeriya ba, cewar The Nation.

Matasa sun yi zanga-zanga a Kano

Kun ji cewa fusatattun matasan Kano sun toshe hanyar Kano zuwa Zaria bayan ayarin motocin banki sun buge adaidaita sahu har ta kife.

Kara karanta wannan

An cakawa jami'ar NSCDC wuƙa a Abuja, asibitoci sun ƙi karɓarta har ta mutu

Shaidu sun ce jami’an tsaron da ke rakiyar motocin bankin sun harba hayaki mai sa hawaye, lokacin da aka tunkare su kan lamarin.

DPO na Na'ibawa ne aka ce ya lallashi matasan, inda ya taimaka aka kwashe wadanda suka jikkata zuwa asibiti don ba su agaji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.