Gwamna Ya Ɗauki Zafi, Ya Dakatar da Kwamishinoni 25 da Wasu Hadimai 60 a Ebonyi
- Gwamna Francis Nwifuru ya dakatar da kwamishinoni 25, mataimaka 38 da sakatarori 22 saboda rashin halartar taron gwamnati
- An hana duk wanda aka dakatar saka hannu a takardun gwamnati yayin da aka tura su hutu na wata guda ba tare da albashi ba
- Yayin da gwamnan ya saki sunayen mukarraban gwamnatin da abin ya shafa, ya ja kunnen ma’aikatan jihar da su kiyaye ka’idojin aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ebonyi - Gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dakatar da jami’an gwamnati 85 saboda rashin halartar wani taron gwamnati.
Waɗanda aka dakatar sun haɗa da kwamishinoni, manyan mataimaka na musamman, mataimaka na musamman, da kuma manyan sakatarori.

Source: Twitter
Gwamnan Ebonyi ya dakatar da mukarrabai 85
Gwamnan, a cikin wata sanarwa a daren Litinin, ya ce an dakatar da jami’an ne saboda rashin halartar wani muhimmin taron gwamnati kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Gwamna ya dakatar da hadiminsa, ya kori Ahmed Musa daga shugabancin hukumar EDOFEWMA
Mai magana da yawunsa, Monday Uzor, ya ruwaito cewa gwamnan ya yanke hukuncin cewa waɗanda abin ya shafa za su tafi hutun aiki na wata ɗaya ba tare da albashi ba.
Ya lissafo kwamishinoni 25, manyan mataimaka na musamman 14, mataimaka na musamman 24, da kuma manyan sakatarori 22 a matsayin waɗanda aka dakatar.
A cewar sanarwar, dakatarwar ta fara aiki nan take, kuma an hana waɗanda aka dakatar saka hannu kan duk wata takardar gwamnati a tsawon wannan lokacin.
Gwamnan Ebonyi ya kara tsauri kan ma'aikata
An umurci kwamishinonin da su miƙa mulki da dukkanin kadarori ko takardun gwamnati da ke hannunsu zuwa ga manyan sakatarorin ma'aikatunsu.
Sanarwar ta ce:
“Gwamnan jihar Ebonyi, Mai Girma Francis Ogbonna Nwifuru ya ba da umarnin cewa jami’an gwamnati da aka lissafta a ƙasa su tafi hutun aiki na wata ɗaya ba tare da albashi ba saboda rashin halartar wani muhimmin taron gwamnati.”

Kara karanta wannan
Noma: Hadimin Buhari ya goyi bayan Tinubu, ya fadi kuskuren da aka samu a zamaninsu
Jaridar Premium Times ta rahoto Uzor ya jaddada cewa gwamnan ya kasance mai tsauri kan dabi'un jami’an gwamnati da kuma jajircewa wajen yi wa al’ummar jihar Ebonyi hidima.
Kwamishinoni da hadiman da aka dakatar
Ga jerin sunayen jami’an da aka dakatar kamar yadda Malam Uzor ya aika a ƙasa:
Kwamishinoni 25 da aka dakatar
- Injiniya Stanley Lebechi Mbam
- Farfesa Leonard Uguru
- Dokta Mathew Nwobashi
- Farfesa Nwogo Obasi.
- Hon. Victor Chukwu
- Injiniya Jude Okpor
- Barr. Ikeuwa Omebe
- Hon. Chidi Onyia
- Cif Oguzo – Offia Nwali
- Dokta Ben. Uruchi Odo
- Dokta Donatus Ilang
- Dokta Mrs Ngozi Obichukwu
- Dokta Moses Ekuma Ikenna
- Cif Richard Idike
- Barr. Mrs. Felicia Nwankpuma
- Hon. Chinedu Nkah
- Injiniya Ogbonna Obasi Abara
- Mrs Nkechinyere Iyioku
- Injiniya Francis Ori
- Hon. Tochukwu Okorie
- Barr. Valentine Okike Uzo
- Cif Sunday Inyima
- Hon. Ogbonnaya Okorie
- Cif Elechi Elechi
- Hon. Stanley Ogbuewu
Manyan mataimaka na musamman (SSA)
- Hon. Bassey Chukwu
- Mrs. Rose Ofoke
- Mr. Kerian Ofoke
- Hon. Anthony Nwegede
- Hon. Onu Nwonye
- Mrs. Lilian Nwachkwu
- Mr. Fred Nwogbaga
- Hon. Paul Nwogha
- Hon. Pius Nwoga
- Hon. Ali Ikechukwu
- Hon. Nwiboko Chukwuma
- Mrs Esther Nwogha
- Barr. Caleb onwe
- Hon. Chinedu Awo
Mataimaka na musamman (SA)
- Mr Mbam Emmanuel
- Tobias Ogbonna
- Easy Okike Uzo
- Obinna Oko Enyim
- Chima Nnachi Okoro
- Nwali Amechi
- Dr. Sabinus Nwibo
- Okorie Jideofor
- Sunday ogenyi
- Stanley Kamani
- Ikechukwu Jideofor
- Emeka Okpa Onwe
- David Aja
- Frank Uka
- John Nwangbo
- Ogbonna Melford Nwuruku
- Ifeanyi Ujebe
- Chima Ogbuagu
- Kizito Nwenyi
- Uwa Henry Ifeanyi
- Elechi Okechukwu Solomon
- Ibina John Ogbonna
- Mbam Ifeanyi D
- Nwigum Nonso Christian

Source: Twitter
Manyan sakatarori (PS) da aka dakatar
- Dr. Lawrence Ezeogo
- Dr. Isioma C Arunne-Inyang
- Mrs Rose Ibe
- Mrs Ogechi Nwobasi
- Mrs Anwu Theresa
- Dr. Lynda Alo
- Mr Monday Nkwuda
- Mrs Mary Ngozi Otozi
- Mrs Martina Obiya
- Mrs Ogechi Anaso-Kalu
- Barr Emmanuel Onwe
- Mr Henry Nworie
- Mrs Joy Mbam
- Mrs Henrietta Ikechukwu Oruh
- Barr Peter Ede
- Dr. Gabriel Odo
- Mrs Mfon Williamson
- Ms Alusi Felicia
- Mrs Betty Uzoma
- Engr Chukwuma Ojeogu
- Barr Ikechukwu Alobu
- Mr Fidelis Nwankwo
Gwamna Nwifuru ya dakatar da mukarrabansa
A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa, gwamna Francis Nwifuru na jihar Ebonyi ya dakatar da kwamishinoni biyu kan zargin rashin ɗa'a da sakacin aiki.

Kara karanta wannan
Belin dilan ƙwaya: Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamiti game da kwamishinansa a Kano
Kwamishinan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a, Jude Chikadibia-Okpor ya bayyana hakan a sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Abakaliki.
Jude ya ce Gwamna Nwifuru ya kuma dakatar da babban sakataren ma'aikatar lafiya da shugabannin hukumomi biyu na ɓangaren kiwon lafiya.
Asali: Legit.ng
