Ana Neman Hana Majalisar Dattawa Daga Darajar Sarkin Musulmi a Najeriya

Ana Neman Hana Majalisar Dattawa Daga Darajar Sarkin Musulmi a Najeriya

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi tir da kudirin da ke neman bai wa Oonin Ife da Sultan na Sokoto matsayi na musamman
  • Ohanaeze ta bayyana cewa hakan zai tauye hakkokin sauran sarakunan gargajiya daga yankunan kasar nan
  • Ta ce kudirin ya sabawa adalci, daidaito da tsarin raba madafun iko da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Ohanaeze Ndigbo Worldwide ta yi kira ga Majalisar Dattawa da ta janye wani kudiri da ke neman daga darajar Ooni na Ife da Sultan na Sokoto.

Rahotanni sun nuna cewa ana son ba Sarkin Musulmi da Ooni na Ife matsayin shugabanni na dindindin a Majalisar Sarakunan Gargajiya ta kasa.

Mai alfarma Sarkin Musulmi a fadar shi a Sokoto
Mai alfarma Sarkin Musulmi a fadar shi a Sokoto. Hoto: National Moon Sighting Committee
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa kungiyar ta bayyana wannan mataki a matsayin wani yunkuri da zai tauye martaba da matsayin sarakunan gargajiya daga sauran yankuna da kabilu a Najeriya.

Kara karanta wannan

An gano miliyoyin da aka tara domin tallata Tinubu a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata sanarwa da kakakin kungiyar, Ezechi Chukwu, ya fitar a ranar Lahadi a Enugu, Ohanaeze ta nuna damuwa kan yadda Majalisar Dattawa ke tafiyar da lamarin.

Ohanaeze ta soki Majalisar Dattawa

Ohanaeze ta bayyana cewa wannan kudiri ya daure mata kai kuma ya nuna gazawar Majalisar Dattawa wajen kare bukatun kowane yanki da kabila a Najeriya.

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar ta ce:

"Wannan kudiri ba wai kawai rashin adalci ne ba, ya nuna wariya da son kai. Ya saba da tsarin Najeriya a matsayin kasa mai yawan kabilu da addinai."

Kungiyar mai kare muradun Ibo ta bayyana cewa kundin tsarin mulki ya tanadi tsarin raba madafun iko da tabbatar da daidaito tsakanin kabilu da yankuna, wanda wannan kudiri ya bijire masa.

Kiran a janye kudirin a Majalisa

Ohanaeze ta bukaci Majalisar Dattawa da ta gaggauta janye kudirin domin sake duba shi cikin adalci da la'akari da bambancin kabilu da tsarin siyasa a kasar nan.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin limamai da ƴan addinin gargajiya kan birne Sarki

Sanarwar ta ce:

"Ya kamata a gyara wannan kudiri ta yadda zai kunshi wakilci daidai tsakanin kabilu da yankuna, ba wai a mayar da wani yanki ko kabila matsayin fiye da sauran ba."

Kungiyar ta kara da cewa hakan ne kadai zai taimaka wajen gina hadin kai, zaman lafiya da karfafa dangantaka tsakanin sassa daban-daban na kasar nan.

Ooni na Ife tare da shugaba Muhammadu Buhari
Ooni na Ife tare da marigayi shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: Garba Shehu
Source: Twitter

Kudirin ya kai matakin karatu na biyu

Rahotanni sun tabbatar da cewa kudirin ya riga ya kai matakin karatu na biyu a Majalisar Dattawa.

Wannan matakin ya kara tayar da jijiyoyin wuya daga yankuna da dama, musamman daga yankin Kudu maso Gabas.

Ana ganin mutanen yankin na zaton cewa ana yunkurin rage tasirin sarakunan gargajiya daga sauran yankuna.

Ohanaeze ta bukaci sauran kungiyoyi da 'yan Najeriya masu kishin kasa da su tashi tsaye wajen ganin an dakatar da wannan kudiri da ake ganin zai iya kawo rarrabuwar kawuna.

Sarkin Musulmi ya je taro a Igila

Kara karanta wannan

An harbe 'dan bindiga ‘Dan Dari Biyar' da ya shahara da gallazawa Hausawa

A wani rahoton, kun ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya halarci wani taron addini a kasar Ingila.

Rahoto ya bayyana cewa taron ya samu halartar manyan shugabannni daga kasashen Musulmi a fadin duniya.

Sarkin Musulmi da ya wakilci Najeriya ya yi magana kan muhimmancin hadin kai da kawo zaman lafiya a kasashe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng