Fitinannen Uban Daba a Kano, Barga Ya Faɗa Komar Ƴan Sanda
- 'Yan sandan Kano sun cafke Mu’azu Barga, wanda ake zargi da jagorantar hare-haren fashi a jihar
- Haka kuma ana zargin Barga na da hannu da tayar da rikice-rikicen daba a tsakanin ɓata-garin ƙungiyoyi a jihar
- An kama Barga tare da wasu mutum 14 a unguwannin Sheka, Ja’oji da Kurna, yayin da ake zurfafa bincike
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta cafke wani da ake zargi da kasancewa kasurgumin ɗan fashi da makami mai suna Mu’azu Barga.
An yi nasarar a wani gagarumin samame da suka kai a sassan birnin Kano domin daƙile ayyukan ‘yan daba da masu tayar da hankulan jama'a.

Source: Facebook
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya tabbatar da kama Barga a shafin Facebook.

Kara karanta wannan
Cakwakiya: Asirin amarya ya tonu, ƴan sanda sun kama ta watanni bayan ɗaura aurenta
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kano: Ƴan sanda sun kama ƴan daba
Bincike rundunar ya nuna cewa Barga na daga cikin waɗanda ke jagorantar hare-haren ‘yan fashi da tashe-tashen hankula a cikin birnin Kano.
An cafke shi tare da wasu mutum 14 yayin wani samame da jami’an rundunar ‘yan sanda suka kai a unguwannin Sheka, Ja'oji da Kurna a ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025.
A cewar sanarwar da SP Kiyawa ya fitar, kama waɗannan bata-garin na cikin shirin Operation Kukan Kura, wanda Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya kaddamar.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“An kama waɗanda ake zargi da aikata laifin, waɗanda shekarunsu ke tsakanin 14 da 28, da wayoyi huɗu da suka sace daga hannun mutane daban-daban. Sun amsa cewa suna aikata laifuffuka irin su fashi da satar wayoyi.”
'Yan sandan Kano sun fara binciken Barga
Rundunar ‘yan sandan ta ce Mu’azu Barga sananne ne wajen jagorantar hare-haren da rikice-rikice tsakanin kungiyoyin ɓata gari a cikin birnin Kano.
Ta ce kama shi na nuna ci gaba a yaki da aikata laifuffuka a jihar, kuma ana sa ran hakan zai dakile ayyukan miyagun mutane.
Rundunar ta ce za a gurfanar da duk waɗanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.

Source: Facebook
A nasa bangaren, CP Ibrahim Bakori ya jaddada kudirin rundunar na yaƙi da duk wani nau’i na laifi a jihar, yana mai cewa:
“Mun ayyana yaki da duk wani nau’in laifi. Rundunar ‘yan sandan Kano za ta ci gaba da tabbatar da zaman lafiya da tsaro a dukkanin fadin jihar.”
Rundunar ta kuma gode wa jama’a bisa haɗin kai, tana mai rokon su da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin taimakawa jami’an tsaro.
An hallaka hatsabibin ɗan daba a Kano
A baya, kun ji cewa rundunar ƴan sandan Kano ta tabbatar da kisan wani shahararren ɗan daba da ake zargi da aikata fashi da makami, mai suna Baba Beru.
Baba Beru ya rasa ransa ne a ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, bayan da ya yunƙura kai hari kan wasu jami’an ‘yan sanda da ke gudanar da sintiri a Gwammaja.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa lokacin da jami’an suka nemi kama Baba Beru, sai ya fusata, ya fito da wuƙa cikin hanzari da niyyar kai wa jami’an hari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
