‘Dalilin da Ya Sa Tsohon Akanta Janar Ke Kiwon Dabbobi Daji Masu Hatsari a Kano’
- Hukumar kula da dabbobi ta Kano ta tabbatar da cewa Ahmed Idris yana da lasisin kiwon dabbobin dawa a gidansa
- Bayan mesa ta tsere, mazauna Kano sun shiga fargaba, inda aka kwashe sauran dabbobin cikin dare domin tsaron lafiyar jama'a
- Sarkin Kano da 'yan sanda sun gargadi Idris, yayin da ake ci gaba da bincike kan barazanar da dabbobin ke iya kawowa cikin gari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Hukumar kula da namun dawa ta jihar Kano ta yi karin haske kan dalilin da ya sa Ahmed Idris ke ajiye dabbobi a gidansa.
Hukumar ta tabbatar da cewa tsohon Akanta-janar, Ahmed Idris yana da lasisin kiwon dabbobin dawa a gidansa.

Asali: Facebook
An fadi dalilin Idris na kiwon dabbobi a gidansa
Shugaban hukumar, Sadik Kura Muhammad, ya bayyana hakan a wani shirin rediyo wanda jaridar Punch ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sadik Kura ya ce lasisin ya ba shi damar kiwon kada, macizai da dan damisa da sauran dabboobi a gidansa.
Ya ce lasisin yana bisa dokar kiwon dabbobi na Najeriya, amma sai an cika sharuddan tsaro da kula da dabbobin a gidaje.
Muhammad ya kara da cewa akwai dokar da ke ba da dama ga mutum ya rike dabbobin dawa a gida.
Ya ce irin wadannan dabbobi, kamar tsuntsaye ko agwagwi, dole ne su kasance a cikin gidan 'zoo' domin kiyaye rayuwarsu.
Shugaban ya bayyana cewa dabbobin ba su kai matakin barazana ba tukuna, amma aka kwashe su saboda korafe-korafen jama'a.
Ya ce da zarar irin wadannan dabbobi sun girma, dole a maida su gidan 'zoo', saboda haka ake sabunta lasisi duk shekara domin tsaro.
A cewarsa:
"Na tabbatar da lasisin, kuma zakin da ke gidan har yanzu jariri ne. Amma muna sa ido sosai saboda amincin jama'a."

Kara karanta wannan
Kano: An ɗauki mataki a kan dabbobin dawan gidan tsohon Akanta bayan mesa ta tsere

Asali: Original
Yadda batan mesa ya rikita mazauna Kano
Majiyoyi sun ruwaito cewa wata mesa ta tsere daga gidan Idris da ke unguwar Daneji, abin da ya tayar da hankalin mazauna, cewar Premium Times
Wannan mesa ta haddasa firgici a unguwannin Mandawari, Kabara da Soron Dinki, inda jama'a suka daina barin yara su fita waje.
A martaninsu, masu kula gidan namun daji sun gudanar da aikin kwashe dabbobin cikin dare ba tare da hayaniya ba, inda aka mayar da su zuwa gidan kula da dabbobi.
Muhammad ya tabbatar da cewa:
“Mun kammala kwashe dabbobin cikin dare. Yanzu suna karkashin kulawarmu cikin kwanciyar hankali.”
Kungiyoyi da jama’a sun bukaci gwamnati da ta hana kiwon dabbobin dawa a wuraren zama saboda hatsarin da ke tattare da su.
Yanzu haka, lamarin yana kara jawo bincike da muhawara kan irin dabbobin da mutane ke rike da su a unguwanni cikin birane.
Sarki Sanusi II ya fusata da batan mesa a Kano
Kun ji cewa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bukaci 'yan sanda su binciki batan mesa da ake zargi a jihar.
Majiyoyi sun ce mesar ta bata ne da ake zargin mallakin tsohon Akanta-janar, Ahmed Idris ne a jihar Kano.
Al’umma sun kai kuka gaban Sarki, suna korafi kan kiwon dabbobi masu hadari da ake yanka shanu don ciyar da su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng