Abba Ya Kai Ziyarar Gaggawa Makarantar Sakandaren Kano bayan Bidiyon Ɗan Bello
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci Kano Day Science College bayan bidiyon Ɗan Bello da ya bayyana matsalolin makarantar
- A cikin bidiyon da Ɗan Bello ya fitar, ya kutsa lungu da saƙo na makarantar inda ya riƙa nuna muhimman wuraren da ke da nakasu
- Ziyarar gwamnan ta ja hankalin al'ummar Kano, daga ciki har da fitaccen lauya, Abba Hikima da ya yaba da salon mulkin Abba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya kai ziyarar aiki ta gaggawa zuwa makarantar Kano Day Science College da ke jihar a ranar Litinin, 29 ga Yuli, 2025.
Ziyarar gwamnan na zuwa ne kasa da kwana guda bayan da fitaccen ɗan gwagwarmaya a kafafen sada zumunta, Ɗan Bello, ya fitar da wani bidiyo.

Kara karanta wannan
Belin dilan ƙwaya: Gwamna Abba Kabir ya kafa kwamiti game da kwamishinansa a Kano

Source: Facebook
Bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna mummunan yanayin da makarantar ke ciki da suka haɗa da rashin kujeru zama da isassun kayan koyo da koyarwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin bidiyon, Ɗan Bello ya zagaya lungu da sako na makarantar, inda ya bayyana matsalolin da suka hada da: rashin ruwa, da kuma tsananin datti da rashin tsafta a banɗaki.
Gwamnan Kano ya ja hankalin jama'a
Ziyarar gwamna Abba ta ja hankalin jama'a, musamman ma wadanda ke bibiyar ci gaban makarantun gwamnati da ƴan gwagwarmaya.
Fitaccen lauya, Abba Hikima, ya nuna farin cikinsa da matakin da gwamnan ya dauka, kamar ya yadda ya wallafa a shafin Facebook.
A cewarsa:
"Gwamna ya kai ziyarar aiki kafa-da-kafa makarantar da niyyar gyarawa."
"Wannan shine shugabanci. Shugabanci a aikace. Shi Gwamna bai kalli abin a matsayin adawa ba. Ya kalle shi a gyara kayanka. Kuma ya amsa kira."
"Zan iya baku misalai kusan biyar irin wadannan da mukayi kira ko korafi a wannan kafar, kuma gwamna ya amsa kiran cikin abin da bai wuce awanni 48 ba."
Gwamna Abba ya burge jama'a a Kano
Matakin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauka na kai ziyarar gani da ido zuwa makarantar ya burge jama'a da dama, daga cikinsu har da Abba Hikima da Ɗan Bello.

Source: Facebook
A saƙon da Abba Hikima ya wallafa, ya ce:
"To gaskiya wannan ya yi matukar burge ni. Kuma akwai abun koyi ga mabiya a irin wannan dabi’a. Gwamnatin Kano ba ta wasu ba ce. Ta kowa da kowa ce."
"Lallai wannan yayi matukar kayatar da ni kuma ina fatan ganin Kano Day Science College, a matsayinta na babbar makarantar da jihar Kano ba tada irinta, kuma makarantar da ni kaina ita na gama, ta dawo cikin hayyacinta."
Abba ya sa a binciki kwamishinansa
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya dauki mataki mai tsauri dangane da yaki da safarar miyagun kwayoyi a jihar.
Ya yi umarnin kafa kwamitin bincike kan rawar da Kwamishinan Sufuri, Alhaji Ibrahim Namadi, ya taka a wajen belin wani da ake zargi da safarar kwayoyi.
A watan Mayun 2025 ne hukumar NDLEA ta gurfanar da Sulaiman Danwawu a gaban wata kotun tarayya da ke Kano bisa zargin mallakar miyagun kwayoyi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

