Jerin Sunaye: An Miƙa Bukatar Kirkiro Sababbin Jihohi 8 a Arewa maso Yammacin Najeriya

Jerin Sunaye: An Miƙa Bukatar Kirkiro Sababbin Jihohi 8 a Arewa maso Yammacin Najeriya

  • Masu ruwa da tsaki a Arewa maso Yammacin Najeriya sun buƙaci ƙarin jihohi takwas daga cikin bakwai da ake da su a yankin
  • Sun mika wannan buƙata ne a wurin taron sauraron ra'yoyin jama'a da Majalisar Dattawa ta shirya kan gyaran kundin tsarin mulkin ƙasa
  • Kwamitin Majalisar Dattawa kan batun gyaran kundin tsarin mulki ya gudanar da taron jin ra'ayoyin ne a Kano a ƙarshen makon nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Arewa maso Yamma ta nemi a ƙirkiro ƙarin jihohi takwas a yankin yayin da tattaunawa kan gyaran kundin tsarin mulki na 1999 ke ci gaba.

Masu ruwa da tsaki daga wannan yanki ne suka gabatar da wannan buƙata a lokacin wani taron sauraron ra'ayoyi na kwanaki biyu da Kwamitin Majalisar Dattawa ya shirya.

Arewa maso Yamma ta buƙaci ƙarin jihohi.
Masu ruwa da tsaki sun nemi ƙarin jihohi 8 a Arewa maso Yamma Hoto: @Tundunwada_m
Source: Twitter

Kwamitin Majalisar ya shirya taron ne domin karɓar bukatun jama'a game da gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaro da mafarauta sun hada hannu, an yi fata fata da 'yan ta'adda

Majalisar Dattawa ta shirya taro a Kano

Taron ya gudana ne a jihar Kano a ƙarshen makon nan da ya gabata kuma manyan masu ruwa da tsaki a Arewa maso Yamma sun halarta.

A halin yanzu Arewa maso Yamma na da jihohi guda bakwai wato: Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Sokoto, Zamfara da Jigawa, rahoton The Cable.

An ruwaito cewa dubban 'yan Najeriya ne suka halarci taron kwanaki biyu don gabatar da ra’ayoyinsu domin la’akari da su a gyaran kundin mulkin da Majalisar Tarayya ke yi.

Majalisa ta fara aikin gyaran kundin tsarin mulki

Majalisar Dokoki ta 10 ta fara gudanar da tarukan sauraron jama’a a dukkan sassan ƙasar shida don tattara ra’ayoyin jama’a game da gyaran kundin tsarin mulkin 1999.

Kafin haka, kwamitin Majalisar Wakilai kan gyaran kundin tsarin mulki ya riga ya kammala sauraron jama’a a dukkan yankunan Najeriya, ciki har da yankin Arewa maso Yamma wanda aka gudanar a Kaduna.

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Kwankwaso, Sarki Sanusi II ya yi jawabi mai jan hankali a taron Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta gudanar da taro a ranar Alhamis da ta gabata domin daidaita matsayar jihar kafin taron sauraron ra’ayoyin da Majalisar Dattawa ta shirya a ƙarshen mako.

Jihohi 8 da aka nemi ƙaro a Arewa maso Yamma

Jerin sunayen jihohi takwas da aka miƙa bukatar ƙirƙirowa a Arewa maso Yamma ga Majalisar dattawa sune:

1. Jihar Tiga daga Kano

2. Jihar Ghari daga cikin Kano.

3. Haɗeija daga cikIn Jigawa

4. Jihar Karaɗua daga Katsina

5. Sabuwar jihar Kaduna daga Kaduna

6. Jihar Gurara

7. Jihar Bayajida

8. Jihar Kainji.

Majalisar Dattawa ta fara jin ra'ayoyin jama'a.
Kwamitin Majalisar Dattawa ya yi taron sauraron ra'ayoyin jama'a a Kano Hoto: @NGRSenate
Source: Facebook

Majalisa ta amince da ƙirƙiro jihohi 12?

A wani labarin, kun ji cewa Shehu Umar Buba ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa majalisar dattawa ta amince da ƙirƙirar sababbin jihohi 12.

Sanata Buba ya ce majalisar dattawa ba ta yanke wani hukunci ba dangane da ƙirƙirar sababbin jihohi ko ƙananan hukumomi a faɗin ƙasar nan.

Ya bayyana cewaa halin yanzu majalisar dattawa ta kafa kwamitoci na jihohi domin gudanar da sauraron ra'ayin jama'a kan sake duba kundin tsarin mulkin 1999.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262