Fadar Shugaban Kasa Ta Samu Abin Magana bayan Dakatar da El Rufai daga SDP

Fadar Shugaban Kasa Ta Samu Abin Magana bayan Dakatar da El Rufai daga SDP

  • Fadar shugaban kasa ta yi martani kan dakatarwar da aka yi wa Nasir Ahmad El-Rufai daga jam'iyyar adawa ta SDP
  • Hadimin mai girma Bola Tinubu ya yi wa tsohon gwamnan na jihar Kaduna shagube bayan ya fuskanci kansa cikin wata matsala ta siyasa
  • Jam'iyyar SDP dai ta dauki matakin ladabtar da El-Rufai bayan ta zarge shi da sabawa wasu ka'idojin da take da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi shagube mai zafi kan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bayan da aka kore shi daga jam’iyyar SDP.

Shaguben dai na zuwa ne bayan El-Rufai ya tsinci kansa cikin matsala sakamakon dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar SDP.

An yi wa El-Rufai shagube daga fadar shugaban kasa
Fadar shugaban kasa ta yi wa El-Rufai shagube Hoto: @DOlusegun, @elrufai
Source: Twitter

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa Bola Tinubu shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, ne ya yi shaguben ga El-Rufai a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Za mu shiga Aso Rock': Atiku ya fadi babban shirin ADC na karbar mulki a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin na Shugaba Tinubu ya mayar da martani kan labarin dakatar da El-Rufai daga SDP na tsawon shekaru 30.

Jam'iyyar SDP ta ladabtar da Nasir El-Rufai

Idan ba a manta ba dai kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar SDP ya sanar da dakatar El-Rufai a ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025.

An dai zargi tsohon gwamnan ne na jihar Kaduna da yin karya ta hanyar bayyana kansa a matsayin ɗan jam’iyyar ba tare da cikakkiyar rajista ba.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na kasa na SDP, Araba Rufus Aiyenigba, ya fitar, jam’iyyar ta bayyana cewa El-Rufai bai taɓa yin rajista da ita ba yadda kundin tsarin mulkinta ya tanada ba, amma duk da haka yana ta bayyana kansa a bainar jama’a a matsayin mamba.

Jam’iyyar ta jaddada cewa El-Rufai ya kasa yin rajista a matakin gunduma, wanda shi ne sharadi na farko da ya wajaba kafin a ɗauki mutum a matsayin sahihin ɗan jam’iyyar, amma duk da haka yana ta iƙirarin kasancewa cikin SDP.

Kara karanta wannan

SDP ta jikawa Nasir El Rufa'i aiki, ta jefa shi matsalar siyasa ta shekara 30

Wane martani fadar shugaban kasa ta yi?

A martanin da Bayo Onanuga ya yi, ya nuna cewa El-Rufai ya kara zama ba shi ga tsuntsu ba shi ga tarko.

Fadar shugaban kasa ta taso El-Rufai a gaba
El-Rufai ya gamu da matsala a jam'iyyar SDP Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Ya bayyana cewa El-Rufai ya sake zama dan gudun hijirar siyasa.Ya bayyana cewa El-Rufai ya sake zama dan gudun hijirar siyasa.

"Ya sake zama dan gudun hijira"

- Bayo Onanuga

Wannan kalmar da Onanuga ya furta tana nuna yadda siyasar El-Rufai ke kara shiga tsaka mai wuya, ganin yadda kwanan nan ya bar jam’iyyar APC mai mulki ya koma SDP.

SDP ta nesanta kanta da El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar SDP ta fito ta nesanta kanta da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

SDP ta bayyana cewa El-Rufai ba mamba ba ne a cikinta kuma bai da wani iko a kan harkokinta.

Sakataren SDP na yankin Arewa maso Yamma ya bayyana cewa El-Rufai ba mamba ba ne a jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng