Shugaban Malamai a Izala, Sheikh Shu'aibu Ahmad Ya Rasu a Jihar Gombe

Shugaban Malamai a Izala, Sheikh Shu'aibu Ahmad Ya Rasu a Jihar Gombe

  • Rahotanni sun nuna cewa malamin Izala, Malam Shu’aibu A Ahmad ya rasu a Gombe bayan doguwar jinya da ya yi a asibiti
  • Bayanan sun nuna cewa marigayin yana daga cikin fitattun malaman Izala da suka yi karatu a kasashen waje a jihar Gombe
  • Kungiyar Izala ta tabbatar da yau Litinin, 28 ga Yuli, 2025 za a yi jana’izarsa da misalin karfe 5:00 na yamma a unguwar Jekadafari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Allah ya yiwa malamin addinin Musulunci kuma shugaban majalisar malamai na Jekadafari Kudu a Gombe, Malam Shu’aibu A Ahmad rasuwa.

Rahoto ya nuna cewa malamin ya rasu ne bayan fama da jinya mai tsawo a babban asibitin koyarwa na tarayya a jihar Gombe.

Shugaban malaman Izala na Jekadafari Kudu da ya rasu a Gombe
Shugaban malaman Izala na Jekadafari Kudu da ya rasu a Gombe. Hoto: Jibwis Gombe
Source: Facebook

Kungiyar Izala mai hedkwata a Jos ta tabbatar da labarin rasuwar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

An gano miliyoyin da aka tara domin tallata Tinubu a zaben 2027

Malam Shu’aibu da ya shahara a cikin malaman Izala a Jekadafari Kudu, ya rasu a yau da rana kamar yadda majiyoyi daga mabiyansa suka tabbatar.

Rayuwa da karatun Malam Shua'ibu

Marigayin ya kasance daya daga cikin malaman jihar Gombe da suka samu damar yin karatu a ketare, inda ya halarci jami’ar Musulunci ta kasa da kasa da ke kasar Chadi.

Bayan dawowarsa daga karatu, ya ci gaba da koyar da dalibai a makarantun addini da kuma a masallatai daban-daban cikin karamar hukumar Gombe.

Bayaga karantarwa, marigayin ya kasance daya daga cikin limaman kungiyar Izala na Juma'a a jihar Gombe.

Batun jagorancin Izala a Jekadafari Kudu

Malam Shu’aibu ya karbi jagorancin malamai na Izala Jekadafari Kudu bayan rasuwar Sheikh Abdul Hadi Zubairu Dawood, wanda shi ma ya kasance babban malami a jihar.

A matsayinsa na shugaban malamai, ya jagoranci koyarwa da tsare-tsaren ilimi na kungiyar tare da tafiyar da shirye-shiryen da suka shafi addini da al’umma.

Kara karanta wannan

Musulunci ya yi babban rashi, Sheikh Dalha Konduga ya rasu

Wani ladanin Izala, Malam Adamu Awak, ya zantawa Legit cewa sun yi zaman lafiya da marigayin:

"Bayan rasuwar Malam Abdu Hadi aka ba shi shugabanci.
"Mutum ne mai kokari. Mun yi aiki tare da shi sosai. Ina rokon Allah ya gafarta masa."

Ana jimamin rasuwar Malam Shua'ibu

Rasuwar marigayin ta haifar da alhini a zukatan mutane da dama, musamman daga cikin dalibansa da sauran malamai a jihar Gombe.

Za a gudanar da jana’izar Sheikh Shu’aibu a yau da misalin karfe 5:00 na yamma a unguwar Jekadafari, inda ake sa ran musulmi daga sassa daban-daban na Gombe za su halarta.

Sheikh Dalha Konduga ya rasu a Borno

A wani rahoton, kun ji cewa wani fitaccen malamin Musulunci a jihar Borno, Sheikh Dalha Konduga ya rasu.

Rahotanni da Legit ta samu sun nuna cewa malamin ya rasu ne bayan fama da rashin lafiya mai tsanani.

Malamai da dama a Najeriya sun yi jimamin rasuwar shi, ciki har da tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng