Babu Sauki: Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga Masu Yawa a Neja

Babu Sauki: Dakarun Sojoji Sun Hallaka 'Yan Bindiga Masu Yawa a Neja

  • Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka 'yan bindiga masu yawa yayin wani artabu da suka yi a jihar Neja
  • Sojojin sun samu galabar ne tare da hadin gwiwar jami'an rundunar Hybrid Forces bayan samun bayanan sirri daga wajen DSS
  • Biyo bayan gumurzun da aka yi, an hallaka 'yan bindiga da dama tare da kona baburan da suke amfani da su masu yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Dakarun Sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami'an rundunar Hybrid Forces sun hallaka 'yan bindiga 45 a jihar Neja.

Dakarun sojojin sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri daga wajen jami'an hukumar DSS.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Neja
Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Neja Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa 'yan bindigan ne da aka kashe sune wadanda suka addabi kauyen Iburu da ke karamar hukumar Shiroro ta jihar Neja.

Sojoji sun samu bayanan sirri kan 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi barin wuta kan 'yan ta'addan ISWAP, an tura kwamandoji zuwa lahira

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa DSS ta samu bayanan sirri cewa 'yan ta'addan wadanda ke kan babura da dama suna kan hanyarsu ta kai hari a kauyen Iburu da wasu kauyuka masu makwabtaka da shi.

Nan da nan DSS ta sanar da sojoji da ke cikin shiri, inda suka ɗauki mataki cikin gaggawa, rahoton da jaridar Leadership ya tabbatar.

A cewar majiyoyin, musayar wuta ta barke tsakanin dakarun da tsagerun a ranar Juma’a, wanda hakan ya haifar da kisan akalla 'yan ta'adda 45.

Yadda sojoji suka hallaka 'yan bindiga

Majiyoyin sun ambato mazauna yankin na cewa sun ga gawarwaki fiye da 40 da ake zargin na 'yan ta'addan ne, kuma sun ƙirga baburan miyagun da dama da aka lalata yayin faɗan.

Sai dai, an rasa rayukan mambobi biyu na rundunar hybrid forces da ke aiki tare da dakarun sojoji.

Hakazalika wasu huɗu daga cikinsu na karɓar magani a asibitin gwamnati da ke babban birnin jihar, sakamakon raunuka masu tsanani da suka samu daga harbin bindiga.

Sojoji sun kashe 'yan bindiga a Neja
Sojoji sun ragargaji 'yan bindiga a Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

A tuna cewa a watan Afrilu da ya gabata, Kwanturola Janar na hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adeniyi, ya koka kan yadda 'yan ta'adda ke ƙara samun karfi a yankin iyakar Babanna da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama bindigogi ana kokarin kai su Kano daga Filato

Adeniyi ya bayyana cewa jami’ansa sun tsallake rijiya da baya daga wani farmakin kwanton-bauna da 'yan ta’adda suka kai musu, sakamakon kwace jarkoki 500 na man fetur da masu fasa ƙwauri ke kokarin kai wa gare su.

Karanta wasu labaran kan sojoji

Sojojin sama sun kashe 'yan ta'addan ISWAP

A wani labarin kuma, kun ji cewa sojojin sama sun samu nasara kan 'yan ta'addan kungiyar ISWAP a jihar Borno.

Sojojin na rundunar Operation Hadin Kai sun hallaka 'yan ta'addan ne bayan kai wani farmaki a maboyarsu da ke cikin daji.

A yayin harin da sojojin suka kai, an hallaka kwamandojin ISWAP tare da mayaka masu yawan gaske, an kuma lalata kayan aikin da suke amfani da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng