Rashin Imani: 'Yan Bindiga Sun Kwantar da Mutane Sun Musu Yankan Rago a Zamfara
- Ƴan bindiga sun kashe mutum 38 ta hanyar yankan rago bayan garkuwa da su a ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda
- Rahotanni sun nuna cewa an biya kuɗin fansa da ƴanbindigar suka nema, amma hakan bai hana su kashe mutanen ba
- Legit ta gano cewa shugaban ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda ya ce jami’an tsaro ba sa ba su kulawar da ya kamata a yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun kashe mutum 38 a kauyen Banga da ke ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda, jihar Zamfara, ta hanyar yi musu yankan rago.
Shugaban ƙaramar hukumar, Manniru Haidara Ƙaura, ya bayyana cewa waɗanda aka kashe ɗin na cikin mutum 56 da aka sace kusan wata huɗu da suka gabata.

Source: Original
BBC Hausa ta rahoto ya ce daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, mutum 18 kawai aka sako bayan an biya kuɗin fansar da aka nema.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan bindiga sun yi wa mutane yankan rago
Manniru Ƙaura ya ce an tara kuɗin fansa Naira miliyan 50 kamar yadda ƴan bindigar suka buƙata, amma duk da haka sun kashe mutum 38 cikin waɗanda suka kama.
Ya ce:
“Sun karɓi kuɗin da suka nema kuma suka saki mutum 18 da suka haɗa da mata 17 da ƙaramin yaro. Sai dai sauran 38 din sun yi musu yankan rago.”
Su wanene 'yan bindigan suka yanka?
Shugaban Ƙaramar Hukumar ya ce bayanan da suka iso daga kauyen na nuna cewa mafi yawancin waɗanda aka yanka matasa ne.
“Wannan aiki na nuna rashin imani ne. Sun manta cewa ‘yan’uwansu ne suke kashewa. Kuma babu makawa za mu haɗu da su a gaban Allah,”
- Inji shi
'Jami’an tsaro ba su tallafa mana' — Ƙaura
Dangane da rawar da jami’an tsaro ke takawa, Ƙaura ya bayyana cewa a yankinsa ba sa samun taimakon da ya kamata daga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan
Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum
A cewar shi:
“A gaskiya jami’an tsaro ba sa ba mu goyon bayan da ya dace. Sai dai ‘yan sanda na jihar su kaɗai muke gani suna kokari,”
Ƙaura ya ce daga cikin waɗanda suka dawo da su, mutum 16 suna asibiti yanzu haka ana kula da lafiyarsu, sai dai ba a samu gawarwakin waɗanda aka kashe ba.
“Ƴan bindiga ba sa ba da gawar mutane da suka kashe, kamar yadda suka saba. Wannan ya ƙara tayar mana da hankali a yankinmu,”
- Inji shi cikin takaici.

Source: Facebook
Tuni dai aka fara Allah wadai kan yi wa mutane yankan rago, ciki har da hadimin tsohon shugaban kasa Buhari, Bashir Ahmad.
Bashir ya wallafa a X cewa kisan mutanen ta hanyar yankan rago bayan biyan kudin fansa abin Allah wadai ne.
An kama mai safarar makamai zuwa Kano
A wani rahoton kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane da ake zargi suna safarar makamai.
An kama daya daga cikin mutanen ne a karamar hukumar Kazaure dauke da bindiga yana shirin shiga jihar Kano.
Haka zalika, an kama dayan dauke da bindiga a jihar Kano kuma binciken 'yan sanda ya bayyana cewa daga Filato suke safarar makaman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

