Daga Litinin: Akwai Yiwuwar Ruwan Sama Ya Jawo Ambaliya a Kano da Jihohin Arewa 5

Daga Litinin: Akwai Yiwuwar Ruwan Sama Ya Jawo Ambaliya a Kano da Jihohin Arewa 5

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai karfi daga Litinin zuwa Laraba a sassa daban-daban na kasar nan
  • Wasu jihohin Arewa za su fuskanci ruwa da iska mai karfi, wanda zai iya haddasa ambaliya a Bauchi, Filato da wasu jihohi hudu
  • NiMet ta bukaci jihohin da ta lissafa a jerin wadanda za su iya fuskantar ambaliyar ruwan da su dauki matakan kariya tun da wuri

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta bayyana cewa za a samu ruwan sama da iska mai karfi a sassan kasar nan daga Litinin zuwa Laraba.

NiMet ta kuma nuna fargabar cewa, mamakon ruwan sama da za a samu na iya jawo ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa shida.

Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ambaliyar ruwa a wasu jihohin Arewa daga Litinin, 28 ga Yulin 2025
Ruwan sama kamar da bakin kwarya na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar hasashen yanayin ta fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Yulin 2025 a Abuja, inji rahoton TVC News.

Kara karanta wannan

Yayyafi ranar Juma'a: NiMet ta lissafa Kano da jihohin da za su samu ruwan sama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi na ranar Litinin

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu iska da ruwan sama mai matsakaicin karfi da safe a yankunan Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe da Katsina a ranar Litinin.

"Ragowar sassan yankin Arewa za su fuskanci yanayin rana da dan hadari kadan," in ji sanarwar.

NiMet ta kara da cewa za a samu ruwan sama da yammaci zuwa dare a yankunan Jigawa, Zamfara, Kano, Kaduna, Bauchi, Yobe, Katsina, Kebbi, Adamawa da Taraba.

Sai dai ta yi gargadi cewa akwai yiwuwar ambaliyar ruwa a sassan Bauchi, Jigawa, Katsina, Kaduna da Kano a wannan rana ta Litinin.

A yankin Arewa ta Tsakiya, za a samu hadari da safe tare da ruwan sama a wasu sassan Abuja da jihohin Neja, Binuwai, Filato da Nasarawa.

“Daga baya kuma, za a samu ruwan sama a Abuja da jihohin Filato, Nasarawa, Kogi, Binuwai da Neja.”

Kara karanta wannan

'Kwankwaso na tsaka mai wuya a siyasa tsakanin shiga APC, PDP ko ADC,'

NiMet ta bayyana cewa akwai yiwar jihar Filato ta fuskanci ambaliyar ruwa a wannan lokaci.

A Kudu, za a fuskanci hadari da safe, sai kuma a samu ruwan sama da yamma a jihohin Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Edo, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Hasashen yanayin NiMet na ranar Talata

A ranar Talata, za a samu rana da dan hadari a wasu yankunan Arewa da safe, kamar yadda rahoton jaridar Vanguard ya nuna.

Amma NiMet ta ce za a samu hadari da ruwan sama da safiyar a sassan Adamawa, Taraba, Yobe, Kaduna, Bauchi, Gombe, Jigawa, Katsina da Kano.

Da yammacin ranar kuwa, za a samu iska da ruwan sama a Adamawa, Taraba, Jigawa, Kano, Kaduna, Katsina, Sokoto da Kebbi.

A Arewa ta Tsakiya, ruwan sama zai sauka da safe a Abuja da jihohin Neja, Binuwai, Kogi, Filato da Nasarawa, yayin da za a kara samun ruwan sama da yamma a Abuja, Filato, Neja, Kwara, Kogi da Nasarawa.

Kara karanta wannan

Ana sa ran ruwan sama zai sauka a Katsina, Kano da jihohin Arewa 17 ranar Alhamis

A Kudu, hadari zai fara haduwa da safe, inda ake sa ran ruwan sama a Akwa Ibom da Cross River, sai kuma a samu ruwan sama mai karfi daga baya a jihohin Abia, Delta, Rivers, Cross River, Akwa Ibom da Bayelsa.

NiMet na fargabar cewa jihohin Arewa za su iya fuskantar ambaliya yayin da ruwa na kwanaki 3 zai sauka daga Litinin
NiMet ta yi hasashen saukar ruwan sama da iska mai karfi na kwana 3 a jihohin Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Hasashen yanayi na ranar Laraba

A ranar Laraba kuwa, za a fuskanci rana da dan hadari a wasu sassan Arewa, amma NiMet ta ce:

“Za a samu hadari mai hade da tsawa tare da ruwan sama da safe a Kaduna, Kebbi, Taraba, Sokoto, Zamfara, Yobe, Jigawa, Kano da Katsina.
"Daga bisani kuma, za a kara samun ruwan sama a Borno, Jigawa, Kaduna, Taraba, Adamawa, Bauchi, Yobe, Gombe, Zamfara da Kebbi."

A Arewa ta tsakiya kuwa, NiMet ta ce za a samu hadari da safiyar Laraba tare da yiwuwar ruwa a Abuja da jihohin Filato, Neja da Nasarawa; sai kuma ruwan sama da yamma a Abuja, Filato, Neja, Binuwai da Nasarawa.

A Kudu, ruwan sama da safe zai zuba a jihohin Ebonyi, Akwa Ibom, Rivers da Cross River, yayin da ake sa ran hadari a sauran jihohin.

Da yamma kuma, za a samu ruwan sama mai karfi a Ebonyi, Abia, Enugu, Imo, Anambra, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Janar Tukur Buratai ya tsage gaskiya, ya fadi abin da ke shigar da matasa ta'addanci

NiMet ta gargadi jihohin da ke fuskantar barazanar ambaliya da su sanya matakan gaggawa na kare lafiyar al’umma da dukiyoyinsu.

Ambaliya a jihohin Najeriya a watan Yuli

Tun da fari, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi gargaɗi cewa jihohi 20 na cikin haɗarin ambaliyar ruwa a watan Yuli 2025, inda jihar Sokoto take kan gaba.

Kaduna, Zamfara, Yobe da wasu jihohi 16 na daga cikin yankunan da za su iya fuskantar ambaliya a cikin wannan wata na Yulin 2025.

Hukumar hasashen yanayin ta bukaci a tsaftace magudanan ruwa, a guji tuki yayin ruwan sama, tare da kaura daga wuraren da ambaliya ke iya shafawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com