Sojojin Sama Sun Yi Barin Wuta kan 'Yan Ta'addan ISWAP, an Tura Kwamandoji zuwa Lahira
- Rundunar sojojin saman Najeriya (NAF) ta bayyana cewa dakarunta sun samu nasarar rage mugun iri na 'yan ta'adda a Borno
- NAF ta bayyana cewa an kai wani hari ta sama kan maboyar 'yan ta'addan kungiyar ISWAP mai kai hare-haren ta'addanci
- Harin da aka kai mafakar miyagun ya yi sanadiyyar hallaka manyan kwamandoji da mayakan kungiyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF), da ke aiki ƙarƙashin Operation Hadin Kai (OPHK), ta hallaka wasu manyan kwamandoji da mayaƙan kungiyar ISWAP.
Rundunar sojojin ta hallaka kwamandojin na ISWAP ne a wani harin sama da aka kai cikin kwarewa a jihar Borno.

Source: Getty Images
Mai magana da yawun sojojin sama, Air Commodore Ehimen Ejodame, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce an kai harin ne a ranar 27 ga Yuli, 2025, inda aka mayar da hankali kan Arina Woje, wani sansanin ISWAP mai haɗari da ke Kudancin yankin Tumbuns na jihar Borno, wurin da ke matsayin mafaka ga shugabannin 'yan ta'adda.
An yi ruwan wuta kan ƴan ta'addan ISWAP
Ejodame ya ce harin saman ya biyo bayan wasu jerin bincike na leƙen asiri, sa ido da gano abubuwa da suka tabbatar da cewa wasu 'yan ta'adda sun koma yankin bayan rikice-rikicen cikin gida da suka faru tsakanin ɓangarorinsu daban-daban.
A cewarsa, bayanan binciken sun gano motsin mayaƙa, farfado da gine-gine da kuma ɓoye sansanonin umarni da na ajiyar kayan aiki a ƙarƙashin dazuka masu cike da ganye.
Saboda haka, bisa sahihan bayanan leƙen asiri, an aika jiragen yakin sojoji domin kai harin da aka shirya.
"Da isowar matukan jirgin, sun gano wuraren da aka hango tuni, sannan suka kai hari ta hanyar amfani da makamai masu zuwa inda aka tura su, inda suka yi gagarumar barna."
- Air Commodore Ehimen Ejodame
Sojojin sama sun yi wa ƴan ta'adda rugu-rugu
Ya ƙara da cewa binciken farko kan barnar da aka yi wa makiyan, ya nuna cewa an lalata gine-gine da dama da ke ɗauke da shugabannin ISWAP, mayaƙa da ma'ajiyar kayan aiki.

Source: Original
Ya ce harin ya tarwatsa tsarin su na shirya farmaki da samun kayan tallafi a yankin, rahoton TVC News ya tabbatar.
Wannan aikin ya nuna kokarin NAF wajen kawar da 'yan ta'adda, hana su ƴancin motsawa da kuma tallafawa dakarun kasa wajen maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin Najeriya.
Sojoji sun hallaka jagororin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu jagororin ƴan bindiga uku a jihar Sokoto.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma ne dai suka samu nasarar bayan sun yi musu kwanton ɓauna.
Nasarar ta samu ne lokacin da jagororin ƴan bindigan ke ƙoƙarin karɓar kuɗin fansa na wasu mutane da suka sace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

