Dattawa Sun Faɗi Dalilan da Suka Jawo Arewa Ta Tsaya Cak, Babu Cigaba a Najeriya

Dattawa Sun Faɗi Dalilan da Suka Jawo Arewa Ta Tsaya Cak, Babu Cigaba a Najeriya

  • Sakataren yaɗa labaran labaran ACF, Farfesa T.A. Muhammad Baba, ya goyi bayan kalaman shugaban riƙo da jam'iyyar ADC, David Mark
  • David Mark, wanda tsohon shugaban majalisar dattawa ne ya zargi Arewacin Najeriya da jefa kanta a cikin matsalolin da ta ke ciki
  • A kalamansa, Farfesa T. A Muhammad ya ce duk da gaskiya shugaban rikon na ADC ya faɗi, amma ya zuzuta lamarin fiye da yadda yake

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), Farfesa T.A. Muhammad Baba, ya yi magana kan koma bayan yankin.

Ya danganta koma baya da rashin ci gaban Arewa da rashin haɗin kai a siyasa da kuma gazawar talakawa wajen tabbatar tuhumar wakilan gwamnati.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Arewa na fama da matsaloli
Sakataren ACF ya ce tabbas akwai matsaloli a Arewa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/Getty
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito Farfesa T.A Muhammad Baba ya yi kalaman ne a matsayin martani kan wasu kalaman tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, dangane da koma baya a Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

David Mark, wanda shi ne shugaban riƙo na ADC, ya yi zargin cewa Arewa ta jefa kanta cikin ƙuncin tattalin arziki da rayuwar yau da kullum.

Sakataren ACF ya gamsu da kalaman ADC

Rahoton ya ƙara da cewa ko da yake ACF ba ta fitar da matsayarta a hukumance a kan batun ba tukuna, Farfesa Baba ya aminta da kalaman Sanata David Mark.

A cewarsa:

"Abin da David Mark ya faɗa ba sabon abu ba ne. Mutane da dama sun sha faɗin hakan tun da daɗewa. Arewa na baya a dukkanin ɓangarori na ci gaba –da suka haɗa da lafiya, ababen more rayuwa, da ilimi."
"Rashin haɗin kanmu a siyasa da gazawar ɗaukar mataki a kan shugabanni su ne suka jefa yankin a cikin wannan hali. David Mark ya fadi gaskiya a wasu fannoni, duk da cewa ya zuzuta da yawa. Matsalolin Arewa sun samo asali ne daga ciki da wajen yankin, amma matsalolin cikin gida sun fi yawa."

Kara karanta wannan

Yilwatda: Muhimman abubuwa game da sabon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa

Sakataren kungiyar ACF ya shawarci ƴan Arewa

Farfesa T.A Muhammad Baba ya kara da cewa yanzu lokaci ne da Arewacin ƙasar nan za ta tashi tsaye domin kawo ƙarshen matsalolin da suka hana ta ci gaba.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Farfesa T.A Muhammad ya ce Arewa za ta iya magance matsalolinta Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Farfesa Baba, wanda ya taba rike matsayin shugaban Sashen Kimiyyar Zamantakewa da Gudanar da Harkokin Jama’a a Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi, ya ce akwai mafita.

Ya shawarci al’ummar Arewa da su fara canji daga kansu, musamman ta hanyar ilimi domin a samu sauyin da zai inganta rayuwar jama'a.

A kalamansa:

Dole a mayar da hankali kan ilimi domin canjin Arewa zai fara ne daga cikinmu."

A ƙarshe, ya bayyana cewa wadannan kalaman nasa ra’ayinsa ne na ƙashin kai, bai yi magana a matsayin sakataren ACF na ƙasa ba.

Audu Ogbeh ya kokawa Arewa

A wata hira da jaridar ta yi da shi a baya, Audu Ogbeh ya bayyana cewa bai kamata Arewa ta dukufa wajen siyasa alhali an yi mata nisa wajen cigaba ba.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya yi murabus daga PDP a zungureriyar wasikar shafi 9

Tsohon ministan ya koka da yadda yankin yake koma baya a bangaren tattalin arziki, ya kuma zargi gwamnoni da danne kananan hukumomi har a yau.

Dattawan Arewa sun faɗi damuwarsu

A baya, kun ji cewa kungiyar Northern Elders Forum (NEF) ta bayyana rashin jin daɗinta game da rikicin siyasa da ya ɓarke a jihar Ribas,

A wata sanarwa da kakakin kungiyar, Farfesa Abubakar Jika Jiddere, ya fitar NEF ta nuna damuwa kan yadda aka dauki matakin dakatar da gwamnatin jihar.

NEF ta yi watsi da matakin da Bola Tinubu, ya ɗauka, inda ta ce babu wani hali na rushewar doka da oda da zai sa a ayyana dokar ta-ɓaci a jihar Ribas..

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng