Iyalan Buhari Sun Bar Gidan da aka Birne Tsohon Shugaban ƙasa a Daura
- Hajiya Aisha Buhari da ’ya’yanta sun koma Kaduna daga Daura bayan kwanaki birne tsohon shugaba Muhammadu Buhari
- Mataimakiyar gwamnan Kaduna, Dr. Hadiza Balarabe ce ta jagoranci tawagar tarbar su a sansanin sojojin sama da ke jihar
- Bayan tarbar ne kuma aka raka su zuwa gidansu da ke Unguwan Rimi GRA cikin girmamawa da mutuntawa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano –Matar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari ta bar Daura a Katsina zuwa jihar Kaduna.
Hajiya Aisha ta koma gidan tsohon shugaban kasar tare da yaranta bayan kwanaki 12 da birne Muhammadu Buhari a a garin Daura.

Source: Twitter
Channels TV ta wallafa cewa an tarbe su ne a sansanin rundunar sojin sama da ke Kaduna a ranar Lahadi, inda mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Hadiza Balarabe, ta jagoranci tawagar tarbarsu.

Kara karanta wannan
Ana kewar Buhari, Tinubu da manyan APC za su yi taron farko na maye gurbin Ganduje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi wa iyalan Buhari tarbar girmamawa
Legit News ta wallafa cewa tare da mataimakiyar gwamnan akwai jagorar masu rinjaye a majalisar dokokin jihar Kaduna, Rt. Hon. Munira Tanimu da wasu manyan jami’an gwamnati.
Daga bisani, Hadiza Balarabe ta raka Hajiya Aisha Buhari da tawagarta zuwa gidansu da ke Unguwan Rimi GRA a cikin birnin Kaduna.

Source: Twitter
Rahotanni sun ce an gudanar da tarbar cikin mutunci da girmamawa, alamar ci gaba da nuna kima ga marigayi tsohon shugaban kasa da gudunmawarsa ga ci gaban Najeriya.
Martanin jama'a da Aisha Buhari ta koma Kaduna
Wasu daga cikin masu bibiyar shafin X sun yi magana bayan iyalin marigayin sun dawo gidansa da ke Daura inda a nan ya fi zama a rayuwarsa.
@Maxajee ya wallafa cewa:
"Maganar gaskiya dama fa zaman Daura ba nata bane."
@OmotayoSolomo10 cewa ya yi:
"Akwai lauje cikin naɗi, me yasa ba ta son ci gaba da zaman Daura?"
@ezekiel05761121 ya yi tambaya cewa:
Yanzu waye zai zauna a gidan da aka birne shi a Daura?"
@BabaInna2 ya ce:
"Allah sarki Duniya. Sun baro Baba Yana kwance daga shi Sai ayyukansa. Allah ka kyautata karshenmu."
@AdesinaAji47706 ya ce:
"Na fahimci halin da iyalin nan ke ciki. Da alama PMB Uba ne na ƙwarai da ya kula da iyalinsa. Zai ɗauki lokaci kafin su iya dangana kan batun rasuwarsa. Ina rokon Allah ya ba tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa ƙarfin zuciya da za ta kula da iyalanta. Allah ya ba su ƙarfi da juriya a wannan lokaci."
Yadda ake biso a addinin Islama
A cikin addinin Musulunci, akwai tsari na musamman da aka shimfida don gudanar da jana’iza da kuma bi da mamaci cikin girmamawa.
Musulunci yana koyar da cewa a hanzarta wanke mamaci, a sa masa likkafani, sannan a yi masa salla kafin a binne shi; duk cikin sauri da tsabta.
Ana bukatar a binne mamaci ba tare da bata lokaci ba, yawanci cikin awanni 24, in babu wani babban cikas.

Kara karanta wannan
Hoton yadda Aisha Buhari ta rungume tutar da aka lulluɓo gawar mijinta ya ja hankali
An fi son a binne mamaci a inda ya rasu ko kusa da shi, kuma ana hana tafiya mai nisa da gawa idan ba lallai ba ne.
Akwai addu’o’i da aka tanada na musamman da ake karantawa a lokacin wanke mamaci da lokacin sallar jana’iza.
Bayan haka, ana binne shi cikin rami da kansa na fuskantar Ka’aba (gabas), ba tare da kayan ado na alfarma ba.
Girman mamaci ko matsayin sa ba ya canza tsarin jana’iza a Musulunci. Kowa daidai yake a gaban Allah – sarki ko talaka.
Girmamawa ta tabbata ne a cikin sauri, tsafta, da kuma yin addu’a da gaskiya ga mamaci, domin neman rahamar Allah a gare shi.
Bello Yabo ya magantu kan yafewa Buhari
A baya, mun wallafa cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Bello Aliyu Yabo, ya bukaci al’umma da su tuba ga Allah kafin ajalinsu ya riske su.
Sheikh Yabo ya ce wannan kira ya fi dacewa da shugabanni da masu rike da madafun iko, inda ya ce yawan tuban shi zai fi masu alheri kafin su gamu da Allah SWT.
Da yake magana kan masu neman a yafewa tsohon shugaban ƙasar, ya ce akwai damuwa a sigar da wasu malamai ke nema wa Muhammadu Buhari afuwar talakan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
