Ganduje, Hajiya Zainab da Wasu Mutane 86 da Tinubu Ya ba Manyan Mukamai a 2025
- Shugaba Bola Tinubu ya nada shugabannin hukumomi da manyan jami'ai a dukkanin ma'aikatun gwamnatin tarayya a shekarar 2025
- Daga cikin wadanda aka nada akwai Dr. Abdullahi Ganduje (FAAN), Nasiru Gawuna (FMBN), Muhammad Babangida (BoA), da sauran su
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro jerin sunayen mutane 86 da suka samu mukami a gwamnatin Tinubu da ma'aikatar da suke jagoranta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A shekarar 2025, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada akalla mutane 86 a manyan mukamai na hukumomi da cibiyoyin gwamnati daban daban.
Shugaba Tinubu ya nada shugabannin hukumomi 42, babban sakataren hukumar CDCFIB, da kuma mukamai a hukumar jiragen kasa da ta kula da fasahar zamani ta kasa.

Source: Twitter
Mai taimakawa shugaban kasa ta fuskar kafofin sada zumunta, Olusegun Dada ya sanar da mafi akasarin wadannan nade-nade a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Gwamnonin 1999 sun nemi Tinubu ya ajiye raba tallafi, ya samar da ayyuka ga matasa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nada mukaman ya kunshi shugabanni daban-daban a hukumomin tarayya, wanda hakan ke tabbatar da jajircewar gwamnatinsa ga tsarin shugabanci da wakilcin yankuna, kamar yadda wata sanarwa a shafin gwamnatin tarayya ta nuna.
Muhimman mukamai da Tinubu ya nada a 2025
Legit Hausa ta tattaro jerin akalla mutane 86 da suka rabauta da manyan mukaman gwamnati a karkashin Bola Tinubu:
1. Hon. Hillard Eta (Cross River) – Shugaban NYSC a ma'aikatar bunkasa matasa.
2. Prof. Bolaji Akinyemi (Lagos) – Shugaban cibiyar nazarin harkokin kasashen duniya (NIIA).
3. H. E. Abdullahi U. Ganduje (Kano) – Shugaban hukumar kula da filayen jirgin sama (FAAN).
4. Sen. Surajudeen Bashiru Ajibola (Osun) – Shugaban majalisar bunkasa samar da sukari (NSDC)
5. H. E. Sulaiman Argungu (Kebbi) – Shugaban kamfanin dillancin lantarki na Najeriya (NBET)
6. Sen. Magnus Abe (Rivers) – Shugaban hukumar NAGGW.
7. Barr. Festus Fuanter (Plateau) – Shugaban cibiyar malamai ta kasa (NTI).

Kara karanta wannan
An ja layi tsakanin Kwankwaso da Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi wa Madugu raddi
8. Raji Kazeem Kolawole (Oyo) – Darakta-Janar, hukumar kula da fasahar zamani (NBTI)
9. Chief Victor Tombari Giadom (Rivers) – Shugaban cibiyar tsare-tsaren ilimi ta Najeriya (NIEPA)
10. Comrade Mustapha Salihu (Adamawa) – Shugaban hukumar rajistar malamai ta Najeriya (TRCN).
11. Hon. Hamma Adama Ali Kumo (Gombe) – Shugaban asusun ba da horo na masana'antu (ITF).
12. Donatus Enyinnah Nwankpa (Abia) – Shugaban cibiyar fasahar dakunan gwaje-gwaje ta Najeriya (NISLT)
13. Sen. Abubakar Maikafi (Bauchi) – Shugaban cibiyar kimiyya da fasaha ta Sheda (SHESTCO).
14. H. E. Nasiru Gawuna (Kano) – Shugaban Bankin Rance na tarayya (FMBN).
15. Sen. Tokunbo Afikuyomi (Lagos) – Shugaban ofishin samarwa da bunkasa fasaha na kasa (NOTAP).
16. Chief D. J. Kekemeke (Ondo) – Shugaban kamfanin wasiku na Najeriya (NPS).
17. Hon. Musa Sarkin Adar (Sokoto) – Shugaban hukumar kula da hanyoyin ruwa na kasa (NIWA).
18. Prof. Abdulkarim Kana Abubakar (Nasarawa) – Shugaban majalisar karafa ta kasa (NSC).
19. Hon. Garba Datti Muhammad (Kaduna) – Shugaban hukumar kula da dokokin muhalli ta kasa (NESREA).
20. Mu’azu Bawa Rijau (Niger) – Shugaban hukumar kula da tsaron halittu ta kasa (NBMA).
21. Hon. Yahaya Bello Wurno (Sokoto) – Shugaban hukumar ci gaban kogin Sokoto-Rima.
22. Hajiya Zainab A. Ibrahim (Taraba) – Shugabar asibitin koyarwa na tarayya, Gombe.
23. Dr. Kayode Isiak Opeifa (Lagos) – Babban darakta, hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC).
24. Aare (Hon.) Durotolu Oyebode Bankole (Ogun) – Shugaban asibitin koyarwa na tarayya, Ido-Ekiti.
25. Mr. Abdullahi Dayo Israel (Lagos) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Abeokuta.
26. Dr. Mrs. Mary Alile Idele (Edo) – Shugabar cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Asaba.
27. Nze Chidi Duru (OON) (Anambra) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Lokoja.
28. Hon. Emma Eneukwu (Enugu) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Owerri.
29. Manjo Janar Jubril Abdulmalik (mai ritaya) (Kano) – Sakatare, hukumar CDCFIB.
30. Mr. Uguru Mathew Ofoke (Ebonyi) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Umuahia.
31. Barr. Felix Chukwumenoye Morka (Delta) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Yenagoa.

Kara karanta wannan
Cacar baki ta kaure tsakanin Akpabio da Barau da aka zo tantance wani tsohon sanata
32. Alh. Bashir Usman Gumel (Jigawa) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Yola.
33. Dr. Ijeoma Arodiogbu (Imo) – Shugaban asibitin koyarwa na jami'ar tarayya ta David Umahi, Ubuhu, jihar Ebonyi.
34. Chief Edward Omo-Erewa (Edo) – Shugaban hukumar gano da magance zubar man fetur ta kasa (NOSDRA).
35. Yusuf Hamisu Abubakar (Kaduna) – Shugaban hukumar kula da ruwa da ba da kariya ta Najeriya (NIMASA).
36. Hon. Ali Bukar Dalori (Borno) – Shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Nnamdi Azikiwe, Nnewi, jihar Anambra.
37. Hon. Lawal M. Liman (Kaduna) – Shugaban asibitin koyarwa na jami'ar Ahmadu Bello, Shika, Zaria, jihar Kaduna.
38. Dr. Abubakar Isa Maiha (Katsina) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Katsina.
39. Isa Sadiq Achida (Sokoto) – Shugaban majalisar bincike da ci gaban kayayyakin da ake sarrafawa (RMRDC).
40. Dr. Mohammed Gusau Hassan (Zamfara) – Shugaban cibiyar kiwon lafiya ta tarayya, Birnin Kudu.
41. Hon. Duro Meseko (Kogi) – Shugaban cibiyar binciken gine-gine da hanyoyi ta Najeriya.
42. Amb. Abubakar Shehu Wurno (Sokoto) – Shugaban hukumar ci gaban kogin Sokoto-Rima.
43. Augustine Chukwu Umahi (Ebonyi) – Shugaban asibitin koyarwa na Aminu Kano.
44. Engr. Babatunde Fakoyede (Ekiti) – Shugaban hukumar bayar da tallafin karatu ta tarayya (FSBN).
45. Hon. Shola Olofin (Ekiti) – Shugaban asusun inshorar jama'a na Najeriya (NISTF).
46. Dr. Iyke Orikpo (Delta) – Shugaban asibitin koyarwa na UniAbuja.
47. Muhammad Babangida (Niger) – Shugaban Bankin Noma (BoA).
48. Lydia Kalat Musa (Kaduna) – Shugabar hukumar OGFZA.
49. Jamilu Wada Aliyu (Kano) – Shugaban majalisar bincike da ci gaban ilimi ta kasa (NERDC).
50. Yahuza Ado Inuwa (Kano) – Shugaban Hukumar kula da ingancin kayayyaki ta Najeriya (SON).
51. Sanusi Musa (SAN) (Kano) – Shugaban cibiyar zaman lafiya da warware rikici (IPCR).
52. Prof. Al-Mustapha Alhaji Aliyu (Sokoto) – Babban darakta, hukumara haɗin kan fasaha a Afirka (DTCA).
53. Sanusi Garba Rikiji (Zamfara) – Babban darakta, ofishin tattaunawar ciniki na Najeriya (NOTN).
54. Mrs. Tomi Somefun (Oyo) – Babbar darakta, hukumar ci gaban yankunan samar da wutar lantarki (N-HYPPADEC).
55. Dr. Abdulmumini Mohammed Aminu-Zaria (Kaduna) – Babban darakta, hukumar gudanar da albarkatun ruwa ta Najeriya (NIWRC).

Source: Twitter
Nadin manyan sakatarotin gwamnatin tarayya
56. Dr. Onwusoro Ihemelandu (Abia)
57. Philip Ebiogeh Ndiomu (Bayelsa)
58. Dr. Anuma Nlia (Ebonyi)
59. Chinasa Nnam Ogbodo (Enugu)
60. Dr. Kalba Danjuma Usman (Gombe)
61. Dr. Salihu Aminu Usman (Kebbi)
62. Patience Nwakuso Oyekunle (Rivers)
63. Engr. Nadungu Gagare (Kaduna)
Kwamishinonin RMAFC, FCC, da NPC
64. Nkechi Oti Linda (Abia) – Kwamishina, RMAFC.
65. Barr. Imo Efiong Akpan (Akwa Ibom) – Kwamishina, RMAFC.
66. Hon. Ekene Enefe (Anambra) – Kwamishina, RMAFC.
67. Prof. Steve Davies Ugbah (Benue) – Kwamishina, RMAFC.
68. Ntufam Eyo-Nsa Whiley (Cross River) – Kwamishina, RMAFC.
69. Aruviere Egharhevwa (Delta) – Kwamishina, RMAFC.
70. Henry Nduka Awuregu (Ebonyi) – Kwamishina, RMAFC.
71. Victor Otaigbe Eboigbe (Edo) – Kwamishina, RMAFC.
72. Hon. Barr. Omowumi Olubunmi Ogunlola (Ekiti) – Kwamishina, RMAFC.
73. Hon. Chief Ozo Obumneme Obodougo (Enugu) – Kwamishina, RMAFC.
74. Mohammed Kabeer Usman (Gombe) – Kwamishina, RMAFC.
75. Kabir Muhammad Mashi (Katsina) – Kwamishina, RMAFC.
76. Hon. Adamu Abdu Fanda (Kano) – Kwamishina, RMAFC.
77. Prof. Olusegun Adekunle Wright (Lagos) – Kwamishina, RMAFC.
78. Aliyu Almakura Abdulkadir (Nasarawa) – Kwamishina, RMAFC.
79. Ibrahim Bako Shettima (Niger) – Kwamishina, RMAFC.
80. Akeem Akintayo Amosun (Ogun) – Kwamishina, RMAFC.
81. Dr. Nathaniel Adojutelegan (Ondo) – Kwamishina, RMAFC.
82. Hon. Sa’ad Ibrahim Bello (Plateau) – Kwamishina, RMAFC.
83. ESV. Madu-Aji Juluri (Yobe) – Kwamishina, RMAFC.
84. Bello Rabiu Garba (Zamfara) – Kwamishina, RMAFC.
85. Mr. Kayode Oladele – Kwamishina na tarayya, hukumar kula da halaye.
86. Pastor (Mrs) Iyantan Olukemi Victoria – Kwamishinar tarayya, hukumar kidayar jama'a ta kasa.
Abin lura: Legit Hausa za ta ci gaba da sabunta wannan rahoto domin sanya karin wadanda Shugaba Tinubu ya ba mukami a 2025 da hukumar da aka kai su.
Masari ya samu mukami a gwamnatin Tinubu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari a matsayin shugaban gudanarwan TETFund.
(Tsohon) Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya sanar da haka ranar Talata, 6 ga Agustar 2024, inda ya ce an naɗa mambobi 6 a hukumar tarayyar.
Tinubu ya buƙaci sababbin mambobin hukumar da su maida hankali wajen sauke nauyin da ke kan hukumar TETFund na tallafawa makarantu.
Asali: Legit.ng




