Dakarun Sojoji Sun Hallaka Jagororin 'Yan Ta'adda 3 da Suka Addabi Jama'a
- An rage mugun iri na jagororin ƴan ta'adɗa bayan dakarun sojoji sun yi musu kwanton ɓauna a jihar Sokoto
- Dakarun sojojin na rundunar Operation Fansan Yanma sun yi nasarar hallaka fitattun ƴan ta'addan ne a ƙaramar hukumar Sabon Birni
- Bayan tura ƴan ta'addan zuwa barzahu, jami'an tsaron sun kuma ƙwato makamai da babur na hawa a hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma (OPFY) sun samu nasara hallaka jagororin ƴan ta'adda guda uku a jihar Sokoto.
Dakarun sojojin sun yi nasarar hallaka fitattun shugabannin ƴan ta’addan ne yayin wani samame da suka kai cikin nasara a ƙaramar hukumar Sabon Birni ta jihar Sokoto.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kashe jagororin ƴan ta'adda
Dakarun sojojin sun kai samamen ne a ranar Juma'a, 25 ga watan Yulin 2025, tsakanin ƙauyukan Mallamawa da Mazau da ke yankin Tsamaye/Mai Lalle na ƙaramar hukumar.
A yayin samamen, sojojin sun kashe ƴan ta’addan da aka bayyana sunayensu da Kachalla Nagomma, Gurmu da Ali Yar Daribiyar, inda suka ƙwato bindigogin AK-47 guda uku tare da gidan harsasansu da kuma babur ɗaya.
Majiyoyi sun bayyana cewa ƴan ta’addan da yaransu sun shiga yankin ne domin karɓar kuɗin fansa da kuɗaɗen harajin da suka tilasta wa mazauna yankin kafin sojoji su yi musu kwanton ɓauna.
Majiyar ta ce kisan ƴan ta'addan ya jawo farin ciki da walwala a tsakanin mazauna ƙauyukan Mai Lalle, Tsamaye, Rimaye da sauran yankuna da ke cikin ƙananan hukumomin Sabon Birni da Goronyo.
"Waɗannan ƴan ta’addan sun daɗe suna gallaza wa al’umma ta hanyar kisa, sace-sace da karɓar kuɗaɗe da ƙarfi, don haka wannan nasara babban ƙarfafawa ne ga mutane."

Kara karanta wannan
Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum
- Wata majiya
Sojojin sun ci gaba da ƙarfafa ayyukan suna amfani da ƙarfi da dabaru tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da kuma ƴan sa-kai na cikin gida.
Rundunar sojin ta buƙaci al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai cikin lokaci don taimakawa wajen ci gaba da murkushe ƴan ta’adda da sauran masu aikata laifuffuka.

Source: Original
Nasarar abin a yaba ce
Wani mazaunin Sokoto, Dalha Yusuf ya shaidawa Hausa cewa nasar da dakarun sojojim suka samu abin a yaba me.
"A gaskiya irin wadannan labaran suna yi min dadi sosai domin mu a kullum burinmu a ragargaji 'yan ta'adda.
"Nasarar ta su abin a yaba ce kuma muna yi musu fatan ci gaba da samunta a kan 'yan ta'adda."
- Muhammad Dalha
Karanta wasu labaran kan dakarun sojoji
- Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga a Neja, an samu asarar rayuka
- Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu
- Karshen alewa: Sojoji sun kashe babban kwamandan Boko Haram da mayaka masu yawa
Sojoji sun kashe ƴan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya ta bayyana nasarar da ta samu kan ƴan ta'adda a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Rundunar ta bayyana cewa dakarunta sun sami nasarar hallaka ƴan ta'adda masu yawa bayan sun fafata artabu da su.
Sojojin sun kuma yi nasarar cafke mutanen da ake zargi da aikata laifukan satar jama'a tare da sauran miyagun ayyuka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

