Matashi Ya Tono Gawar Kakarsa don Ya Yi Kuɗi, Ya Tsinci Kansa a Gagarumar Matsala

Matashi Ya Tono Gawar Kakarsa don Ya Yi Kuɗi, Ya Tsinci Kansa a Gagarumar Matsala

  • Wani matashi ɗan kimanin shekara 31 ya jefa kansa a matsala a ƙoƙarin yin tsafin kuɗi a jihar Neja da ke Arewa ta Tsakiya
  • Ƴan sanda sun kama matashin, wanda ya tono gawar kakarsa ta wajen uwa kuma ya sare kanta domin kai wa boka
  • Rundunar ƴan sanda ta bayyana cewa matashin ya amsa laifinsa, kuma ya yi bayanin yadda lamarin ya faru tun farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Jami'an ƴan sanda sun kama wani matashi dan shekaru 31 da haihuwa a jihar Neja bisa zargin tono gawar kakarsa ta ɓangaren uwa.

Rahotanni sun bayyana cewa matashin ya tono gawar, sannan kuma ya sare kanta da nufin yin tsafin da boka ya ce masa zai samu maƙudan kuɗi.

Matashi ya tono gawar kakarsa.
Yan sanda sun kama matashin da ya tono gawar kakarsa a jihar Neja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton Aminiya ya nuna cewa jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ’yan sanda na jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata mata, Hadiza Mamuda ta kashe mijinta kan abin da yake kawo mata kullum

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matashi ya tono gawar kakarsa a Neja

Ya ce sun cafke matashin tare da wasu abokan aikinsa a wani otel da ke garin Bida a ranar 19 ga Yuli, 2025.

Kakakin ƴan sandan ya ce, wanda ake zargin ya amsa cewa ya dauki wannan matakin ne don ya samu kuɗi da zai biya bashin da ake binsa wanda haura Naira miliyan 2.

A cewar Abiodun, wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samu shawarar yin tsafin kuɗi ne daga wani boka wanda ya umarce shi da ya samo ƙoƙon kai na mace tsohuwa domin aikin.

Ya ce ya je kabarin kakarsa, wadda ta rasu kusan shekaru biyu da suka gabata tana da shekaru sama da 90, ya tono ta sannan ya sare kanta.

Yadda matasahin ya jefa kansa a matsala

"Bayan ya kasa cika sharuddan da bokan ya gindaya masa, sai ya ajiye kan a wurinsa na tsawon shekaru biyu.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

"Daga baya, wasu abokansa guda biyu suka nuna sha’awar sayen kan don yin nasu tsafin, suka saye shi N100,000 amma suka fara da biyan N40,000 a matsayin kafin alƙalami.
"Suka tafi wurin wani boka da ya karɓi N500,000 domin gudanar da aikin tsafin, haka suka rika biyan kuɗin a hankali. Bayan kammala tsafin, bokan ya umurce su da kada su buɗe gangar da aka aje tsafin har sai ya ba su izini."

- Inji SP Wasiu Abiodun.

Yan sanda sun kama wasu matasa a Neja.
Yadda neman kudin tsafi ya jefa wasu matasa a komar yan sanda a Neja Hoto: Nigeria Police
Source: Getty Images

Ƴan sanda sun kama matashin da abokansa

Ya ƙara da cewa bayan makonni sun shude ba tare da wani sauyi ko alamar kuɗi ba, sai suka nemi bokan a gidansa, amma sai ya shawo kansu da su haɗu a wani otel a garin Bida domin karɓar kuɗinsu.

"A can ne kuma ’yan sanda suka rutsa su suka kama su baki ɗaya," inji Abiodun.

Matar aure ta kashe mijinta a Yobe

A wani rahoton, kun ji cewa ƴan sanda sun damƙe wata mata, Hadiza Mamuda bisa zargin kashe maigidanta kan abinci a jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa matar ta zama ajalin mijin ne sakamakon saɓanin da ya shiga tsakaninsu har suka yi faɗa da doke-doke.

Rundunar ƴan sanda ta ce wannan mummunan al'amari ya faru ne a ƙauyen Garin Abba da ke yankin ƙaramar hukumar Fika a jihar Yobe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262