UNIMAID: Karrama Buhari Ya Jawo Rigima, Tinubu Ya Sake Shiga Matsala kan Lamarin
- ASUU reshen jami'ar Maiduguri (UNIMAID) da ke jihar Borno ta shirya shiga kafar wando daya da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Kungiyar ta ce za ta kai gwamnati kotu saboda sauya sunan jami’ar zuwa 'Muhammadu Buhari University' ba tare da tuntubar ta ba
- Malaman sun bayyana sauya sunan a matsayin rashin girmama ikon jami’a, rashin tuntuba da cin zarafin tarihin shekaru 50 na jami’ar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Kungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU), reshen Jami’ar Maiduguri (UNIMAID), za ta shiga kotu da gwamnatin tarayya.
Kungiyar ta ce za ta kai gwamnatin Bola Tinubu kotu kan sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University.

Source: Facebook
UNIMAID: ASUU za ta shiga kotu da Tinubu
Hakan na cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Juma’a 25 ga watan Yulin 2025 wanda jaridar Tribune ta samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Abubakar Mshelia da Mataimakin Sakataren, Peter Teri sun sanya hannu domin amincewa da matakin.
Sanarwar ta bayyana cewa an cimma wannan matsaya ne bayan wani taron gaggawa da aka gudanar ranar 24 ga Yuli, 2025, da wakilan dalibai da masu ruwa da tsaki.
Kungiyar ta ce:
"Bayan tattaunawa mai zurfi, kungiyar ta yanke shawarar kin amincewa da kuma sukar sauya sunan jami’ar zuwa Muhammadu Buhari University.
“Kungiyar na ganin duk wani yunkurin canza sunan jami’ar Maiduguri, bayan shekaru 50 da kafuwa, cin zarafi ne ga ikon jami’a da al’adar ilimi.”

Source: Facebook
ASUU ta caccaki Tinubu kan canza sunan UNIMAID
ASUU ta bayyana matakin gwamnatin tarayya a matsayin wanda babu tsari, an nuna ƙarfin iko da danniya kuma babu tuntuba da goyon bayan al’umma.
Ta kara da cewa wannan lamari na nuna rashin mutunta tsarin da ya kamata a bi da kuma sakaci da ra’ayoyin masu ruwa da tsaki a sha’anin mulki.
Sanarwar ta ce an ba shugabannin ASUU na UNIMAID umarnin neman mafita ta doka domin kalubalantar sauya sunan da kare asalin martabar jami’ar.
Kungiyar ta kuma bukaci sauran rassan ASUU da na kasa su shiga cikin lamarin tare da tuntubar 'yan majalisa, kungiyoyin fararen hula da dalibai, cewar BusinessDay.
“Kungiyar na bukatar a mutunta ikon da darajar jami’o’in gwamnati ba tare da katsalandan na siyasa ba.
- Cewar sanarwar
Wannan mataki da Tinubu ya dauka ya jawo martani mabambanta duba da yadda wasu ke sukar lamarin duk da cewa akwai wasu da ke ganin hakan abin alfahari ne.
Legit Hausa ta yi magana da dalibin UNIMAID
Tun bayan sauya sunan jami'ar ake ta ce-ce-ku-ce kan lamarin inda mafi yawa ke sukar matakin da Bila Tinubu ya dauka.
Wani dalilibi a tsangayar karantar halayen dan Adam, Bukar Shettima Adam ya ce abin bai masa dadi ba ko kaɗan.
Ya ce:
"Dalibai da wasu malamai da dama har ma kungiyar ASUU sun soki matakin duba da shura da sunan UNIMAID ta yi a fadin Najeriya."
Adam ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake duba kan lamarin yayin da kungiyar ASUU da tsofaffin dalibai suka yi korafi kan haka.
Buhari: An fadi dalilin sauya sunan jam'iar Maiduguri
Kun ji cewa ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa ya yi magana game da sauya sunan jami'ar Maiduguri saboda marigayi tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Alausa ya bayyana cewa an canza sunan UNIMAID don girmama gudunmawar Buhari wajen habaka ilimi a Najeriya lokacin mulkinsa daga 2015 zuwa 2023.
Ya ce wannan matakin na nuna Buhari da Bola Tinubu na ganin ilimi a matsayin tushen cigaba da ci gaban ɗan adam a kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


