Musulunci Ya Yi Babban Rashi, Sheikh Dalha Konduga Ya Rasu
- Allah ya yi wa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Dr Muhammad Abubakar (Dalha Konduga), rasuwa a daren Asabar
- Rahoto ya nuna cewa malamin ya rasu ne asibitin UMTH a Maiduguri, inda danginsa suka tabbatar da mutuwar shi
- Manyan malamai da Musulmi daga sassa daban-daban sun aika da sakonnin ta’aziyya da addu’o’i ga iyalan marigayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr. Dalha Konduga, ya riga mu gidan gaskiya a daren Asaba a birnin Maiduguri, jihar Borno.
Wannan babban rashi ya girgiza al’ummar Musulmi, musamman daliban da suka tasirantu da irin gudunmawar da marigayin ya bayar.

Source: Facebook
Iyalan marigayin ne suka tabbatar da rasuwarsa a wani gajeren jawabi da suka fitar a Facebook, inda suka bayyana cewa ya rasu ne a asibitin koyar da aiki na UMTH da ke Maiduguri.

Kara karanta wannan
Zamfara: An shiga tashin hankali bayan samun gawar malamin Musulunci a mugun yanayi
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun bukaci jama’a da su ci gaba da yi masa addu’ar samun rahama da gafara bayan sanar da lokacin masa jana'iza.
Tuni dai aka fara tura sakonnin ta’aziyya daga mashahuran malamai a Najeriya da ma kasashen waje, suna rokon Allah ya sanya marigayin a Aljannar Firdausi.
Dalha Konduga ya shahara da wa'azi
Dr. Dalha Konduga ya kasance daga cikin fitattun malamai a yankin Arewa maso Gabas da ke koyar da ilimin addini cikin tsantsar tsoron Allah da hikima.
An san shi da karantarwa, wa’azi da tashi tsaye wajen gyaran al’umma ta hanyar isar da saƙonnin addinin Musulunci.
Yayin da yake bayyana alhininsa, Malam Ahmad Wakil ya wallafa a Facebook cewa:
“Hakika rasuwarsa babban rashi ne ga al’umma, musamman a fannin ilimi da wa’azi. Sheikh Dr. Abubakar Dalha ya sadaukar da rayuwarsa wajen yada addini da tarbiyyar al’umma.”
Malam Wakil ya kuma kara da cewa yana rokon Allah Ya gafarta masa, Ya raya zuriyarsa cikin imani da tsoron Allah.

Source: Twitter
An yi wa Dr Dalha Konduga addu’o’i
Daga lokacin da labarin rasuwar Dr. Dalha Konduga ya bazu, mutane daga sassa daban-daban na Najeriya da ma kasashen waje suka ci gaba da yi masa addu’a tare da yin ta’aziyya ga iyalansa.
Wasu malamai daga jihar Borno da Abuja sun bayyana cewa marigayin ya bar babban gibi da wuya a cike, duba da irin tasirinsa wajen da’awah da gyaran tarbiyyar matasa.
Suna rokon Allah Ya saka masa da aljanna, ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan babban rashi.
Yanzu haka a shafin Facebook, ana ta wallafa karatuttukan malamin, musamman wadanda ya yi a karshe-karshen rayuwarsa.
An kafa sabuwar kungiyar malamai
A wani rahoton, kun ji cewa an kafa wata sabuwar kungiyar malaman addinin Musulunci a kasar Yarabawa.
Rahotanni sun bayyana cewa an kafa kungiyar ne domin farfado da ilimi da darajar addinin Musulunci.
Taron kaddamar da kungiyar ya samu halartar manyan malamai a Kudu maso Yamma da wasu jihohin Kudancin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
