Sarkin Gusau da Wasu Manyan Sarakuna da Suka Rasu cikin Wata 1 a Najeriya

Sarkin Gusau da Wasu Manyan Sarakuna da Suka Rasu cikin Wata 1 a Najeriya

Gusau, jihar Zamfara - A watan Yulin 2025 da ke dab da ƙarewa, Najeriya ta rasa manyan sarakuna masu ƙima a sassa daban-daban na ƙasar nan.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

A ranar Juma'a, 26 ga watan Yuli, 2025 aka samu labarin rasuwar Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau (Sarkin Gusau), Dr. Ibrahim Bello bayan fama da jinya.

Sarkin Gusau da sarakunan da suka rasu a watan Yuli.
Sarakuna 3 da Allah ya karɓi ransu a watan Yuli, 2025 Hoto: Dauda Lawal, Ibrahim Kalilula
Source: Facebook

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara da tabbatar da wannan babban rashi na uba da aka yi a wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro maku manyan rasakuna uku da Allah da ya karɓi ransu a wannan wata da ya fara mana bankwana watau Yuli, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi ta'aziyya ga al’ummar jihar kan rasuwar Sarkin Gusau, Mai Martaba, Dr. Ibrahim Bello, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sarkin Gusau: Rasuwar basarake ta gigita Tinubu, ya fadi alherin da ya shuka a ƙasa

Legit Hausa ta ruwaito yadda wannan basarake mai daraja ta ɗaya ya rasu da safiyar ranar Juma’a, 25 ga Yuli, yana da shekaru 71, a wani asibiti da ke Abuja bayan ya jima yana fama da rashin lafiya.

Sarkin Gusau, Dr. Ibrahim Bello.
Allah ya yiwa Sarkin Gusau rasuwa ranar Juma'a, 25 ga watan Yuli, 2025 Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Gwamna Lawal ya bayyana rasuwar Sarkin a matsayin babban rashi gare shi, yana mai cewa marigayin uba ne kuma shugaba nagari wanda ya sadaukar da kansa wajen inganta jihar Zamfara.

An nada marigayi Sarkin Gusau a ranar 16 ga Maris, 2015, lokacin mulkin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari.

Ya gaji ɗan uwansa, Muhammad Kabiru Danbaba, wanda shi ma ya rasu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Abuja a ranar 5 ga Maris, 2015.

2. Sarkin Ijebu, Sikiru Adetona

Mai martaba Sarkin Ijebuland, Oba Sikiru Kayode Adetona, ya rasu a ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025.

An samu labarin rasuwar basaraken mai shekaru 91 jim kaɗan bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari.

Gwamnatin jihar Ogun ce ta tabbatar da rasuwar Sarkin Ijebuland ta bakin Gwamna Dapo Abiodun, cewar rahoton Daily Trust.

Marigayi Oba Sikiru na jihar Ogun.
Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya tabbatar da rasuwar Oba Sikiru Hoto: Prince Dr. Dapo Abiodun
Source: UGC

An naɗa Oba Adetona a matsayin Sarkin ƙasar Ijebu a ranar 2 ga Afrilu, 1960, wanda hakan ya sanya shi ɗaya daga cikin sarakunan da suka fi dadewa kan karagar mulki a Najeriya.

Kara karanta wannan

An sanya lokacin da za a yi jana'izar marigayi Sarkin Gusau, Mai martaba Ibrahim Bello

Ya shahara a faɗin ƙasa ba wai kawai saboda daɗewa a sarauta ba, har ma saboda ƙwazo da halayensa da suka zama abin koyi. Oba Adetona ya fito ne daga gidan sarautar Anikinaiya.

3. Sarkin Ibadan, Olakulehin

Olubadan na Ibadanland, Oba Owolabi Olakulehin, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar Litinin, 7 ga Yuli, 2025.

An haifi basaraken mai daraja ta farko a ranar 5 ga Yuli, 1935, kuma ya rasu kwana biyu bayan cikar sa shekaru 90 da haihuwa.

Rahoton jaridar Tribune Nigeria ya nuna cewa Olakulehin shi ne Olubadan na Ibadan da ke jihar Oto na 43 a tarihi.

Marigayi Sarkin Ibadan, Oba Olakulehin.
Olubadan na ƙasar Ibadan na ɗaya daga cikin sarakunan da suka rasu a watan Yuli, 2025 Hoto: Ibrahim Kalilula
Source: Twitter

An haifi Marigayi Olakulehin a ranar 5 ga Yuli, 1935, iyayensa sune Pa Ishola-Okin Owolabi da Hajiya Adunola Aweni Ope Ajilaran Omoyoade Owolabi.

An haife shi ne a kauyen Okugbaja da ke yankin Ita Baale kusa da Akanran, wanda ke cikin karamar hukumar Ibadan ta Arewa maso Gabas a jihar Oyo, Kudu maso Yammacin Najeriya.

Wakilin Sardaunan Bauchi ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa Wakilin Sardaunan Bauchi, Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Sheikh Pantami ya fitar da bayanai da mutane ke son sani kan rasuwar Sarkin Gusau

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana mamacin a matsayin gwarzon ɗan jarida, kuma gogaggen ɗan siyasa mai ƙwarin gwiwa wajen jawo jama'a daga tushe.

Gwamnan ya yi addu’ar samun rahamar Allah ga marigayin, tare da roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya sa shi a gidan Aljannah.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262