'Yadda Buhari Ya Ki Karbar Kyautar Jirgin Sama da Aka Yi Masa', Garba Shehu
- Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Garba Shehu, ya bayyana yadda Muhammadu Buhari yake da halin ƙin abin duniya
- Garba Shehu ya bayyana cewa akwai lokacin da aka yi wa Buhari kyautar jirgin sama amma sai ya ƙi karɓa
- Hakazalika ya ƙara da cewa marigayin ya ce ba zai karɓi kyautar ba saboda shi aka yi wa, amma da gwamnatin Najeriya ce aka ba da ya amsa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana wasu halayen ƙanƙan da kai na marigayi Muhammadu Buhari.
Garba Shehu ya ce tsohon shugaban ƙasan ya ƙi karɓar kyaututtuka masu tsada da aka yi masa, ciki har da agogon hannu na lu'u-lu'u da kuma jirgin sama na ƙashin kansa.

Source: Twitter
Garba Shehu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da Laolu Akande a shirin 'Inside Sources' na tashar Channels tv a ranar Juma'a, 25 ga watan Yulin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Muhammadu Buhari na gudun abin duniya
Tsohon hadimin shugaban ƙasan ya bayyana wasu lokuta biyu da Buhari ya ƙi karɓar abubuwa masu tsada, ɗaya daga wani mashahurin mai tsara kaya daga Najeriya, ɗaya kuma daga Sarkin Abu Dhabi a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).
Ya ce hakan ya nuna cikakkiyar amana da Shugaba Buhari ke da ita a lokacin da yake mulki.
"An kawo masa agogon hannu mai lu'u-lu'u daga wani mai tsara kaya daga Najeriya wanda ya yi fice a duniya."
"Wannan bawan Allah yana ƙaunar Shugaba Muhammadu Buhari, ya ƙera masa wannan agogon hannu wanda aka ƙawata da lu'u-lu'u. An yi masa ƙira ta musamman har da hoton shugaban ƙasa a jikinsa. Sai ya kawo masa."
- Garba Shehu
Amma Garba Shehu ya ce Buhari ya ƙi karɓar wannan kyauta kai tsaye.
"Shugaban ƙasa ya duba agogon, ya ce, ‘Agogo mai lu’u-lu’u? Ba zan iya sawa ba. Da fatan za a gaya wa wannan matashin ɗan Najeriya cewa yana sa kansa da ƙasarsa alfahari."
"'Ƙoƙarinsa abin a yaba ne. Za mu ci gaba da ƙarfafa masa gwiwa. Amma agogon ku mayar masa da shi. Ba zan iya amfani da shi ba'."
- Garba Shehu
Meyasa Buhari ya ƙi karɓar kyautar jirgin sama?
Garba Shehu ya ƙara da cewa irin wannan matsaya ta Buhari ta ƙin abin duniya ta zarce iyakokin Najeriya.

Source: Twitter
Ya bayar da misali na wani lokaci a cikin 2016, lokacin wata ziyara a hukumance zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa, inda Sarkin Abu Dhabi (wanda shi ne shugaban ƙasar) ya yi masa wani tayin ban mamaki.
"A lokacin da muka je UAE a 2016, a Abu Dhabi, wanda shi ne babban birnin ƙasar, Sarkin Abu Dhabi ya tambayi shugaban ƙasa wane jirgi yake so? Ya yi masa tayin jirgin sama."
"Amma Buhari ya ƙi karɓar wannan kyauta bayan ya fahimci cewa an yi niyyar bayar da ita ne domin amfanin kansa, ba na gwamnatin Najeriya ba."
"Shugaban ya ce, ‘Idan don ƙasata ne, zan karɓa.’ Amma Sarkin ya ce: ‘A’a, kai ne nake nufi da ita kai tsaye, domin ka riƙa amfani da ita har bayan ka sauka daga mulki.’"

Kara karanta wannan
Gaskiya ta ƙara fitowa, an ji babban abin da ya hana Buhari korar wasu ministoci a mulkinsa
- Garba Shehu
"Kwankwaso zai maye gurbin Buhari" - Jigon NNPP
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar NNPP, ya bayyana ɗan siyasan da zai maye gurbin Muhammadu Buhari.
Malam Aminu Ringim ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso ne zai maye gurbin marigayi tsohon shugaban ƙasan.
Ya nuna cewa tsohon gwamnan na Kano yana da halayen tausayin talakawa irin na marigyi Muhammadu Buhari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

