Karfin Hali: Shugaban Ƙaramar Hukuma a Niger Ya Maka Gwamna, NSIEC a Kotu

Karfin Hali: Shugaban Ƙaramar Hukuma a Niger Ya Maka Gwamna, NSIEC a Kotu

  • Shugaban karamar hukumar Chanchaga, Alhaji Aminu Yakubu-Ladan, ya shiga kotu da gwamnatin Niger
  • Yakubu-Ladan ya kai kara kotu ne kan yunkurin rage masu wa’adin mulki daga shekara huɗu zuwa uku
  • Ya bukaci kotu ta dakatar da NSIEC daga gudanar da zaɓe kafin wa’adin su ya ƙare, wanda aka shirya ranar 1 ga Nuwamba 2025

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Shugaban karamar hukumar Chanchaga da ke jihar Neja, Alhaji Aminu Yakubu-Ladan, ya maka gwamnatin jihar a kotu.

Yakubu-Ladan ya shiga kotu ne kan zargin rage wa’adin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli.

An maka gwamna Bago a mulki kan wa'adin ƙananan hukumomi
Shugaban ƙaramar hukuma ya maka gwamna Bago a kotu. Hoto: Abu Abul Fadi Khaleel, Umaru Mohammed Bago.
Source: Facebook

Zaben kananan hukumomi: An maka gwamna a kotu

Hakan na cikin wata takardar kara da Yakubu-Ladan ya shigar a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yakubu-Ladan ya nemi a dakatar da hukumar zaɓe ta jihar Neja (NSIEC) daga gudanar da zaɓen kananan hukumomi har sai wa’adinsu ya cika.

Kara karanta wannan

'Kungiyoyi na tururuwa zuwa INEC, masu neman zama jam'iyyu sun kai 144

Majiyoyi sun ruwaito cewa NSIEC ta sanya ranar 1 ga Nuwamba domin gudanar da zaɓen kananan hukumomi a fadin jihar.

Sai dai a cikin ƙarar, wanda Yakubu-Ladan ya shigar, ya sanya Lauyan Gwamnatin Jihar Neja, Majalisar Dokoki ta jihar, NSIEC, INEC da Sufeto Janar na ‘yan sanda a matsayin wadanda ake ƙara.

Shugaban karamar hukumar na kalubalantar dokar jihar ta 2001 da ke ƙoƙarin rage wa’adin shugabanni da kansiloli daga shekaru huɗu zuwa shekaru uku.

Yakubu-Ladan ya shigar da ƙarar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1370/2025, wadda aka rubuta ranar 10 ga Yuli, aka shigar da ita ranar 11 ga Yuli, ta hannun lauya Chris Udeoyibo.

An maka gwamna Bago na Niger a kotu
Shugaban ƙaramar hukuma ya maka gwamna Bago a kotu kan wa'adin mulki. Hoto: Umaru Mohammed Bago.
Source: Facebook

Buƙatar Yakubu-Ladan a gaban kotu

Shugaban ya bukaci sanin ko gwamnatin jihar na da ikon aiwatar da dokar da ta sabawa kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yiwa gyara fuska) da kuma dokar zaɓe ta 2022.

“Ya kamata a bayyana Sashe na 29 (2) na dokar Niger a matsayin sabawa tsarin mulki da dokar zaɓe ta 2022."

- Cewar Yakubu-Ladan

Ya nemi kotu ta tabbatar da cewa shekara huɗu ne aka tanadar wa shugabannin kananan hukumomi da kansiloli bisa tsarin mulki da dokar zaɓe.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon aikin da Ganduje zai yi wa APC a matakin kasa

Ƙarar ta kuma kalubalanci shirin NSIEC na gudanar da zaɓen kananan hukumomi ranar 1 ga watan Nuwamba mai zuwa, Daily Post ta ruwaito.

Don haka, Yakubu-Ladan na neman kotu ta dakatar da masu ƙara daga gudanar da zaɓen har sai an kammala wa’adin shekara huɗu.

Ƙarar ta kuma nemi kotu ta hana INEC da Sufeto Janar na ‘yan sanda bayar da goyon bayan tsaro ko na aikin gudanar da zaɓen.

Niger: Ana zargin kwamishina da cin zarafin matarsa

Kun ji cewa tsohuwar matar kwamishina a jihar Niger ta taso shi a gaba kan zargin cin zarafi da barazana da yake yi mata.

Hadiza Ali-Musa ta zargi tsohon mijinta, kwamishinan muhalli, Yakubu Kolo, da barazana da tsoratarwa bayan sun rabu.

Hadiza ta ce a aurensu na shekara tara ta sha fama da cin zarafi, yanzu kuma yana kokarin hana ta kula da ‘ya’yanta biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.