Babbar Magana: Ana Neman Kwankwaso Ya Durkusa Ya ba Tinubu Hakuri
- Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya ce babu wata wariya a rabon ayyukan tituna tsakanin Arewa da Kudu a gwamnatin Bola Tinubu
- Ya ce zargin Sanata Rabiu Kwankwaso na cewa Kudu ta fi samun tituna ba gaskiya ba ne, ya kira hakan da yaudara ga mutanen yankin Arewa
- Umahi ya bukaci Kwankwaso da ya janye maganarsa tare da ba Tinubu hakuri yayin da ya ce 'yan Arewa sun fi cin moriyar wasu ayyukan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja - Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, ya mayar da martani kan kalaman Sanata Rabiu Kwankwaso game da gwamnatin Bola Tinubu.
Umahi ya bayyana cewa zargin da tsohon gwamnan Kano ya yi cewa gwamnatin Tinubu tana fifita Kudu wajen rabon ayyukan tituna ba gaskiya ba ne kuma yaudarar al’umma ne.

Kara karanta wannan
An ja layi tsakanin Kwankwaso da Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi wa Madugu raddi

Source: Twitter
A sakon da Bayo Onanuga ya wallafa a X, David Umahi ya ce gwamnatin Tinubu na aiki da gaskiya da adalci wajen aiwatar da manyan ayyukan tituna a fadin kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Tinubu na aiki da adalci' — Umahi
Ministan ya ce kalaman Kwankwaso suna nuna kokarin kawo rarrabuwar kai a tsakanin 'yan Arewa da sauran sassan Najeriya, yana mai cewa kalaman na da hadari ga hadin kan kasa.
A cewar Umahi:
“Zargin da Sanata Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin Tinubu tana fifita Kudu ba gaskiya ba ne.
"Gaskiyar ita ce, a cikin manyan ayyuka guda huɗu na wannan gwamnati, Arewa tana da kaso 52, yayin da Kudu ke da 48.”
Ya bayyana cewa titin Sokoto zuwa Badagry da ke Arewa yana da tsawon kilomita 756, yayin da titin Lagos zuwa Calabar a Kudu ke da tsawon kilomita 350.
Umahi ya lissafa titunan da ake a Arewa
Umahi ya lissafa wasu daga cikin manyan ayyuka da ake gudanarwa a Arewa ciki har da:
- Titin Sokoto - Zamfara - Katsina - Kaduna mai tsawon kilomita 750
- Abuja - Kaduna - Kano mai tsawon kilomita 700
- Titin Bypass a Kano mai tsawon kilomita 49
- Titi a Borno mai tsawon kilomita 110
- Hanyar Malando a Kebbi mai tsawon kilomita 76
- Titi a jihar Benue mai tsawon kilomita 500
Ya ce yawancin wadannan ayyuka an gaje su ne daga gwamnatin da ta gabata amma Tinubu ya ci gaba da su domin amfanin kasa.
Ministan ya kuma bayyana ayyukan da ke gudana a Kudu, kamar ginin hanyoyi da gyaran gadoji a Legas, Oyo, Ogun, Anambra, Delta, da Rivers.

Source: Facebook
An nemi Kwankwaso ya ba Tinubu hakuri
Umahi ya ce kalaman Kwankwaso suna neman bata sunan shugaban kasa ne da kuma jefa mutane cikin rudani.
Ya ce:
“Ina bukatar Sanata Kwankwaso ya janye kalamansa kuma ya nemi afuwar Shugaba Tinubu bisa wannan mummunan zargi.”
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da aiki don ci gaban dukkan sassan kasar nan cikin gaskiya da adalci.
APC ta ce za ta iya karbar Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar APC ta bayyana cewa za ta iya tafiya tare da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso.

Kara karanta wannan
"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci
Jam'iyyar ta ce ba Kwankwaso kawai ba, dukkan wanda ya ke son shiga cikinta, kofofinta a bude suke a ko da yaushe.
Legit ta rahoto cewa sabon shugaban APC da ya maye gurbin Abdullahi Ganduje ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
