Gwamnatin Tinubu Ta Kayyade Mafi Ƙarancin Shekarun Shiga Sakandare a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Kayyade Mafi Ƙarancin Shekarun Shiga Sakandare a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta kayyade shekarun da ya kamata daliban da ke shirin shiga sakandare su kai kafin karbarsu
  • Gwamnatin ta sanya shekara 12 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru na shiga aji na JSS1 bayan kammala karatun firamare
  • Sabuwar dokar da ta fito daga ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa dole ɗalibai su fara firamare a shekara 6 su gama a shekara 12

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta sake sanya doka game da shekarun shiga makarantun sakandare.

Gwamnatin ta gabatar da sabon tsarin da ke ƙayyade shekara 12 a matsayin mafi ƙanƙantar shekaru na shiga JSS1 a sakandare.

Gwamnati ta saka doka game da shekarun shiga sakandare
Gwamnatin tarayya ta sanya mafi ƙarancin shekarun shiga sakandare. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Umarnin gwamnatin Tinubu kan tsarin ilimi

Vanguard ta ce hakan zai tabbata bayan dalibi ya kammala shekaru shida na makarantar firamare da ake da su.

Kara karanta wannan

Dakarun tsaro da mafarauta sun hada hannu, an yi fata fata da 'yan ta'adda

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan umarni yana cikin wata sabuwar takardar manufofi da aka fitar kan makarantun da ba na gwamnati ba, wacce Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta ƙaddamar a makon da ya gabata.

Manufar ta bayyana yadda waɗannan makarantu ke ƙara muhimmanci wajen isar da ilimi a faɗin Najeriya, kodayake akwai bambance-bambancen ƙwarai a inganci da tsarin karatu a cikinsu.

Tsare-tsaren shekarun karatu da aka bayyana

Ma’aikatar ta gabatar da tsari bisa shekaru don ci gaban ilimi daga tushe, inda ta ce:

“Ilimin yara ƙanana zai kasance na tsawon shekaru uku. Za a fara matakin 'Nursery' da zarar yaro ya kai shekara uku.
"Sai 'Nursery' aji biyu a shekara huɗu, sannan shekara guda ta tilas a matakin (Kindergarten) a shekara biyar, kamar yadda aka fayyace a Sashe na 2(17) na NPE, bugun 2013.”

Game da tsarin firamare da JSS, manufar ta ce:

“Ilimin tushe zai kasance na tsawon shekaru tara. Za a samu shekaru shida na firamare da shekaru uku na Junior Secondary School (JSS).

Kara karanta wannan

Janar Tukur Buratai ya tsage gaskiya, ya fadi abin da ke shigar da matasa ta'addanci

"Za a fara firamare aji daya da zarar yaro ya kai shekara shida. Kowane yaro dole ne ya kammala shekaru shida na firamare. Za a fara JSS1 ne bayan kammala wannan mataki, a kusan shekara 12.”
Gwamnatin Tinubu da sake tsari game da shekarun shiga sakandare
Gwamnatin Tinubu kakaba shekaru 12 a matsayin mataki da dalibi zai shiga sakandare. Hoto: Federal Ministry of Education.
Source: Twitter

Gwamnatin Tinubu ta sauya shekarun shiga jami'a

Wannan yana nufin za a kammala sakandare a kusan shekara 18, wanda ya yi daidai da shekarun da aka taɓa warewa don shiga jami'a.

Tsohon Ministan Ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya taɓa bayyana shekara 18 a matsayin mafi ƙarancin shekarun shiga jami'a, amma sabon Minista, Dakta Tunji Alausa, ya dawo da shekaru 16.

Bayanai daga 'Nigeria Education Digest 2022' sun ƙara nuna yadda makarantu masu zaman kansu ke ƙara rinjaye, musamman a matakin JSS, Punch ta tabbatar da zancen.

Gwamnati za ta biyan daliban makarantun fasaha

Mun ba ku labarin cewa gwamnatin tarayya ta sanar da shirin karatu kyauta, samar da abinci da alawus na N22,500 a kowane wata ga ɗaliban makarantun fasaha.

Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a taron ƙaddamar da shirin horar da matasa kan sana’o’i (TVET) a Abuja.

An tsara shirin ne domin jawo hankalin matasa da rage zaman banza ta hanyar koya musu fasahohin da za su amfanar da kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.