Jim Kadan da Nadin Shugabanta na Kasa, APC Ta Yi Sababbin Sauye Sauye a NWC

Jim Kadan da Nadin Shugabanta na Kasa, APC Ta Yi Sababbin Sauye Sauye a NWC

  • APC ta nada Abdulkarim Kana a matsayin mataimakin sakataren kasa, jim kadan bayan an nada Nentawe Yilwatda a matsayin shugaban jam'iyya
  • A taron jam'iyyar da ya gudana a ranar Alhamis, an nada Murtala Aliyu Kankia daga Katsina a matsayin sabon mai ba da shawara kan harkokin shari’a
  • Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodimma ne ya jagoranci kudirin sauya tsarin raba mukamai ga shiyyoyi don tabbatar da adalci a jam’iyya mai mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Jam’iyyar APC ta sanar da sababbin nade-nade a muhimman mukamai na kwamitin aiki na kasa (NWC).

Nadin ya zo ne bayan sauye-sauyen tsarin raba mukamai a tsakanin shiyyoyin kasar nan da aka amince da su a taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana sa ran zai bar NNPP, Kwankwaso ya bada kafa da ya karbi 'yan APC a Kano

Sabon shugaban APC na kasa, Yilwatda
APC ta yi sababbin nade-nade Hoto: @Imranmuhdz/Allah Progressives Congress
Asali: Twitter

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa FarfesaAbdulkarim Kana, tsohon mai ba da shawara kan harkokin shari’a na kasa, yanzu shi ne mataimakin sakataren jam’iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Murtala Aliyu Kankia daga jihar Katsina zai kasance sabon mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyya mai mulki.

Jam'iyyar APC ta yi sababbin nade-nade

Rahoton ya bayyana cewa wadannan sauye-sauyen sun biyo bayan wani kudiri da gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC, Hope Uzodimma, ya gabatar.

A cewarsa, wadannan sauye-sauyen sun nuna jajircewar jam’iyyar wajen tabbatar da adalci da daidaito a cikin gida.

Ya ce:

“Zai zama abin farin ciki a gare ni na yi amfani da wannan dama wajen jagorantar gabatar da wannan kudiri.”

Ya gabatar da bukatar a mayar da kujerar mai ba da shawara kan harkokin shari’a daga Arewa ta Tsakiya zuwa Arewa maso Yamma.

Ita kuma kujerar mataimakin sakataren kasa da ke Arewa ta Tsakiya ta ci gaba da kasancewa a yankin.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito: An ji dalilan da suka jawo naɗa Ministan Tinubu a matsayin shugaban APC

Batutuwan da aka tattauna a taron APC

Kudirin ya kuma 'kunshi tsawaita wa’adin shugabannin mazabu, kananan hukumomi, jihohi da yankunan siyasa har zuwa 31 ga Disamba, 2025.

Shugaban majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas
Tajudeen Abbas ya goyi bayan kudirin nadin APC Hoto: Abbas Tajudeen
Asali: Facebook

Shugaban majalisar wakilai na kasa, Tajuddeen Abbas, ya goyi bayan kudirin, yana cewa:

“Ni na mara baya ga wadannan kudirori da suka hada da cike guraben kujerar mataimakin sakataren kasa da mai ba da shawara kan shari’a bisa sabon tsarin raba mukamai.”

Wadannan nade-nade sun biyo bayan nadin Nentawe Yilwatda, tsohon dan takarar gwamna a jihar Filato, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa.

'Yan APC sun sauya sheka zuwa NNPP

A wani labarin, mun wallafa cewa Yayin da ake cigaba da rade-radin cewa Rabiu Musa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, sai ga shi ya karbi dubunnan 'yan jam'iyya.

A ranar Alhamis, 24 ga watan Yuli, 2025, Kwankwaso ya tarbi wasu manyan magoya bayan APC, kwana guda kacal bayan jam’iyyar APC tace kofa a bude ta ke idan yana bukatar sauya sheka.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa tsarin shugabanci na gari da ake da shi a jihar Kano, da irin jagorancin siyasa na kwarai da NNPP ke nunawa, na ci gaba da jawo hankalin jama'a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel