Yayyafi Ranar Juma'a: NiMet Ta Lissafa Kano da Jihohin da Za Su Samu Ruwan Sama
- NiMet ta yi hasashen saukar yayyafi da ruwan sama mai ƙarfi a sassan Arewa da Kudancin Najeriya ranar Juma’a, 25 ga Yuli, 2025
- Jihohin Arewa kamar Kano, Katsina, Bauchi, Borno da Taraba na fuskantar tsawa da ruwan sama, yayin da Kudu za su sha yayyafi
- NiMet ta shawarci jama’a da su guji tuki yayin ruwan sama, kada su fake karkashin bishiya kuma a rika bibiyar hasashen yanayi
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na yau Juma'a, 25 ga Yulin 2025.
NiMet, ta bayyana cewa akwai yiwuwar a samu guguwa da ruwan sama mai ƙarfi a sassa daban-daban na ƙasar nan, musamman a Arewa.

Source: Original
Rahoton hasashen yanayin na ranar Juma'a na kunshe ne a cikin sanarwar da NiMet ta fitar a shafinta na X a daren ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025.

Kara karanta wannan
An sanya lokacin da za a yi jana'izar marigayi Sarkin Gusau, Mai martaba Ibrahim Bello
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hasashen yanayin NiMet a Arewa
NiMet ta bayyana cewa za a samu haduwar hadari da kuma hudowar rana daga safe zuwa rana a Arewacin Najeriya.
Sannan ana sa ran yayyafi da guguwa a sassan jihohin Jigawa, Gombe, Katsina, Kaduna, Kano, Zamfara, Kebbi, Bauchi, Borno, Yobe da Adamawa.
Amma daga yammaci zuwa dare, ana hasashen ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi zai sauka a Taraba, Bauchi, Yobe, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Borno, Gombe, Zamfara, Katsina, Kano da Adamawa.
A shiyyar Arewa ta tsakiya kuwa, NiMet ta ce za a tashi da hadari da yayyafi a wasu yankunan jihohin Neja, Binuwai, Kogi, Kwara, Abuja da Nasarawa.
Hasashen yanayi na Kudancin Najeriya
Amma daga yamma zuwa dare, za a fuskanci hadari, tsawa da ruwan sama mai dan karfi a sassa Abuja da jihohin Filato, Nasarawa, Kogi, Binuwai da Neja.
A Kudancin Najeriya kuwa, ana sa ran hadari da yayyafi a sassan jihohin Cross River da Akwa Ibom a safiyar Juma’a.
Sannan za a samu yayyafi da ruwan sama a sassan Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Delta, Edo, Bayelsa, Rivers, Cross River da Akwa Ibom daga yammaci zuwa dare.

Source: Original
Shawarwarin NiMet ga Jama’a
NiMet ta shawarci jama'a da su ci gaba da yin taka tsantsan game da yiwuwar ambaliyar ruwa, iska mai ƙarfi, da kuma katsewar al'amuran yau da kullun.
An kuma shawarci direbobi su guji tuki yayin ruwan sama mai yawa don kaucewa haɗurra sannan Kada a fake a karkashin bishiyoyi yayin guguwa don gujewa fadowar reshe.
Hukumar ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su nemi rahoton yanayi na filin jirgin kafin tsara zirga-zirgarsu.
NiMet ta bukaci jama’a su ci gaba da samun sababbin bayanai daga shafinta: www.nimet.gov.ng domin tsare lafiya, rayuka da kuma dukiyoyinsu.
Ruwa mai karfi ya jawo ambaliya a Pakistan
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin Pakistan ta ce mutane 54 sun rasa rayukansu a cikin awanni 24 sakamakon ruwan sama mai karfi da ya haifar da ambaliya a kasar.
A cewar hukumomi, an samu ruwan sama kamar da bakin kwarya, wanda ya haddasa ambaliya mai tsanani da kuma rushe gidaje da ababen more rayuwa.
A halin da ake ciki, adadin wadanda suka mutu tun farkon daminar bana ya kai 180, yayin da gwamnatin kasar ke shawarci jama’a da su tanadi abinci, magunguna da kayan amfani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
