An Ja Layi tsakanin Kwankwaso da Tinubu, Fadar Shugaban Kasa Ta Yi wa Madugu Raddi
- Fadar shugaban kasa ta karyata ikirarin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na cewa Bola Tinubu ya yi watsi da yankin Arewa
 - An lissafo manyan ayyukan da gwamnatin shugaba Tinubu ke aiwatarwa a Arewa da suka shafi hanya, noma da kiwon lafiya
 - Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare, ya ce Tinubu ya nuna jajircewa wajen bunkasa Arewa cikin shekara biyu da ya yi
 
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi watsi da ikirarin da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi na cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ware yankin Arewa.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin sadarwa, Sunday Dare, ya fitar, ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta aiwatar da muhimman ayyuka da dama a Arewa.

Kara karanta wannan
"An yi watsi da Arewa," Kwankwaso ya soki Gwamnatin Tinubu, ya faɗi kalamai masu daci

Source: Twitter
Cikin ayyukan da Sunday Dare ya lissafa a shafinsa na X akwai hanyoyi, asibitoci, ayyukan noma da makamashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a cikin shekaru biyu kacal, Shugaba Tinubu ya bayar da fifiko sosai wajen cigaban yankin Arewa, tare da bayyana wasu daga cikin manyan ayyukan da ke gudana.
Martanin Dare ga ikirarin Kwankwaso
Sunday Dare ya ce gwamnatin Tinubu na gudanar da ayyuka da dama a Arewa irinsu gina manyan hanyoyi kamar Abuja–Kaduna–Kano, da Sokoto–Badagry da Sokoto–Zamfara–Katsina.
Ya bayyana cewa wadannan hanyoyi na da matukar amfani ga sufuri da cinikayya a yankin Arewa.
A fannin aikin noma, ya ce gwamnatin ta aiwatar da shirye-shirye irin su shirin noma na $158m jihohi tara na Arewa.
Haka kuma, ya ce ana aiwatar da shirin ACReSAL domin farfado da filayen noma da magance matsalolin sauyin yanayi.
Tinubu: Ayyukan lafiya da aka yi a Arewa
A fannin lafiya, an ambaci gyaran asibitoci kamar asibitin jami'ar ABU Zariya, asibitocin koyarwa na jami'o'in Katsina da Jos tare da inganta kimanin cibiyoyin lafiya 1,000 a Arewa.

Source: Twitter
Haka kuma, an ambaci hanyoyin mota fiye da 20 da ake ginawa ko gyarawa, ciki har da Kano–Kongolam, Zaria–Funtua–Gusau–Sokoto da kuma Adamawa–Taraba da Kaduna–Jos.
Magana kan makamashi a Arewa
Dare ya ce gwamnati na aiki kan bututun iskar gas daga Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano, da kuma tashar wutar lantarki a Gwagwalada, da fara aikin samar da hasken rana a Kaduna.
Ya ce an fara aikin jirgin kasa daga Kaduna zuwa Kano da kuma daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar.
Haka kuma ya ce gwamnatin Tinubu ta ware Naira biliyan 100 domin samar da jirgin kasa a cikin garin Kaduna.
Fadar shugaban kasa ta ce duk wadannan ayyuka sun faru ne a karkashin shekaru biyu kacal na mulkin Shugaba Tinubu, abin da ke nuna cewa gwamnatin ba ta yi watsi da Arewa ba.
APC ta ce za ta yi maraba da Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa sabon shugaban jam'iyyar APC ya ce suna shirye wajen karbar Sanata Rabiu Kwankwaso idan ya sauya sheka.
Shugaban ya bayyana cewa dukkan tsofaffin 'yan APC da suka koma wasu jam'iyyun siyasa za su iya dawowa gida.
Ya yi magana ne yayin da aka masa tambaya kan yaushe Rabiu Kwankwaso zai koma APC yayin hira da manema labarai a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
    
