Mutuwa Ta Jijjiga Arewa, Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau Ya Rasu
- Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da rasuwar mai martaba Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello da safiyar yau Juma'a
- Sarkin, wanda ya shafe kimanin shekaru 10 a kan karagar mulki, ya rasu yau, 25 ga watan Yuli, 2025 yana da shekaru 71 da haihuwa
- Gwamna Lawal ya yi alhinin wannan babban rashi da jihar Zamfara, Arewa da ma Najeriya gaba ɗaya suka yi, yana mai Addu'ar Allah gafarta masa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau (Sarkin Gusau) da ke jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya, Dr. Ibrahim Bello ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotannin da muka samu sun nuna cewa Sarkin Gusau ya rasu ne da safiyar yau Juma'a, 25 ga watan Yuli, 2025, yana da shekaru 71 da haihuwa.

Kara karanta wannan
Sarkin Gusau: Rasuwar basarake ta gigita Tinubu, ya fadi alherin da ya shuka a ƙasa

Source: Facebook
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da rasuwar basaraken a wani gajeren saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Zamfara ta sanar da rasuwar Sarkin Gusau
Gwamnan ya yi addu'ar Allah Ya gafartawa Marigayi Dr. Ibrahim Bello kuma Ya sanya shi a gidan Aljannatil Firdausi.
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un. Allah Ya jiƙan Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello.
"Allah Ya gafarta mishi, Ya kyautata makwancinshi, Ya yi mishi makoma da Aljannah Firdausi. Aameen."
- Gwamna Dauda Lawal.
DCL Hausa ta tattaro cewa a shekarar 2016, an yaɗa labarin cewa Sarkin Katsinan Gusau, Dr. Ibrahim Bello ya rasu amma daga bisani aka gano ba gaskiya ba ne.
An naɗa Alhaji, Dr. Ibrahim Bello a matsayin Sarkin Gusau ranar 16 ga watan Maris, 2015 a zamanin mulki tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari.
Tun wannan lokacin yake jagorantar masarautar Gusau har zuwa yau da Allah ya karɓi ransa, ya shafe kimanin shekaru 10 kenan a karagar mulki.

Kara karanta wannan
An sanya lokacin da za a yi jana'izar marigayi Sarkin Gusau, Mai martaba Ibrahim Bello
Gwamna Dauda Lawal ya yi ta'aziyya
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sulaiman Idris Bala, ya fitar, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yabawa halaye da nagartar marigayi Sarkin Gusau.
Ya bayyana Dr. Ibrahim Bello a matsayin shugaba nagari mai biyayya da ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidima da ci gaban Jihar Zamfara, rahoton Vanguard.
“Na samu labarin rasuwar ubanmu, Mai Martaba Dr. Ibrahim Bello, Sarkin Gusau, da matuƙar baƙin ciki. Marigayin Sarkin ya kwashe shekaru 10 yana sarauta tun bayan naɗa shi Sarkin Gusau na 15 a ranar 16 ga Maris, 2015.
“Na rasa uba kuma abokin shawara wanda hikimarsa ta kasance haske gare ni da sauran shugabanni. Allah ya gafarta masa, ya sa Aljannah Firdaus ce makomarsa.”
- Dauda Lawal.

Source: Facebook
Kafin hawansa sarauta, Dr. Ibrahim Bello ya yi aikin gwamnati, inda ya kai matsayin Babban Sakataren Gwamnati a tsohuwar Jihar Sakkwato, sannan daga baya a Zamfara.
Wakilin Sardaunan Bauchi ya kwanta dama

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya fitar da bayanai da mutane ke son sani kan rasuwar Sarkin Gusau
A wani rahoton, kun ji cewa Wakilin Sardaunan Bauchi, Alhaji Abubakar Jafaru Ilelah ya riga mu gidan gaskiya bayan taƙaitacciyar jinya.
Marigayi Abubakar Jafaru gogaggen manomi ne kuma ƙwararren masani a harkar ci gaban noma, wanda ya bayar da gudummawa matuƙa.
Kafin rasuwarsa, an nada Alhaji Jafaru Ilelah kwanan nan a matsayin Mataimaki na Musamman ga Gwamna Bala.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng