2027: Shugaba Tinubu Ya Hada 'Yan Hadaka a Wuri Guda, Ya Yi Musu Saukale
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taɓo batun haɗakar ƴan adawa da ke ƙarƙashin jam'iyyar ADC
- Mai girma Bola Tinubu ya yi shaguɓe ga ƴan haɗakar waɗanda ke da burin ganin sun raba shi da mulki a zaɓen 2027
- Shugaban ƙasan ya kuma nuna cewa ƙofar jam'iyyar APC a buɗe take ga duk ƴan siyasan da ke son shigowa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi shaguɓe ga ƴan haɗaka da ke ƙarƙashin jam'iyyar ADC.
Shugaba Tinubu ya bayyana haɗakar a matsayin 'haɗakar ruɗaɗɗu'.

Source: Twitter
Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a taron zartaswa na ƙasa (NEC) na APC karo na 14 a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaba Tinubu ya ce ba laifi ba ne idan aka bar jirgin da ke neman nutsewa.

Kara karanta wannan
Damagum: Shugaban PDP ya fito fili ya fadi wadanda suka assasa matsalolin jam'iyyar
Bola Tinubu ya godewa Abdullahi Ganduje
Ya kuma gode wa tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bisa gudunmawar da ya bayar.
Ya bayyana cewa ya ba shi aikin kafa jam'iyyar ci gaban ra’ayin dimokuraɗiyya kuma ya cika aikin da aka ba shi.
"Na ba shi aikin ƙirƙiro cibiyar ci gaba, sakataren ƙasa na jam’iyya zai yi aiki tare da sabon shugaban jam’iyya domin farfaɗo da ita."
"Har yanzu za mu iya ɗaukar Ganduje a matsayin masani wanda zai ba da shawarwari ga sabon shugaban jam’iyya wajen cimma hakan."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya kuma bayyana cewa canza ranar gudanar da zaɓukan jam’iyya daga matakin jihohi, ƙananan hukumomi da gundumomi zuwa watan Disamba, na da nufin ba da dama ga sababbin mambobin da ake sa ran shigowarsu jam’iyyar
Wane shaguɓe Tinubu ya yi wa ƴan ADC?
A wani shaguɓe na kai tsaye kan jam’iyyar adawa ta PDP da ADC, Shugaba Tinubu ya yi kira ga sauran ƴan adawa da su rungumi jam’iyyar APC mai mulki.
Ya ce babu laifi a bar jam’iyyun da ke fuskantar durƙushewa da ruɗani su dawo jam’iyyar da ke kan madafun iko.
“Babu laifi a bar jirgin da ke nutsewa, sannan a guji shiga cikin haɗakar ruɗaɗɗu."
- Shugaba Bola Tinubu

Source: Facebook
Shugaban ƙasar ya kuma tarbi gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori da gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno, waɗanda kwanan nan suka sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
"Bisa ƙofar da muka buɗe don bai wa masu son shiga APC dama, ƙofofinmu a buɗe suke, kuma za mu karɓe su da cikakken farin ciki."
- Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan jam’iyyar APC ta bayyana ministan harkokin jinƙai, Farfesa Nentawe Yiltwada, a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na ƙasa.
Hakeem Baba-Ahmed ya soki Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hakeem Baba-Ahmed ya soki Shugaba Bola Tinubu kan mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima.
Tsohon mai ba shugaban ƙasan shawara kan harkokin siyasa ya caccaki Tinubu ne kan shirun da ya yi dangane da batun ajiye Shettima kafin zaɓen 2027.
Ya nuna cewa ya kamata shugaban ƙasan ya fito musanta jita-jirar idan har da gaske babu ƙamshin gaskiya a cikinta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
