An Rufe Majalisa a Karshen Zaman da Aka Kusa Yin Rigima, Tajudeen Abbas Ya Ja Hankali
- Bayan kammala zaman ranar Laraba, 23 ga watan Yuli, 2025, Majalisar Wakilai ta tafi hutun shekara shekara na tsawon watanni biyu
- Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce an amince da tafiya hutun ne bayan gabatar da kudiri, mara masa baya da amincewa da shi
- Ya ja hankalin ƴan Majalisar tarayyar da su yi amfani da wannan dama wajen kusantar da kansu ga al'umma da warware matsalolinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Majalisar Wakilai ta Najeriya ta tafi hutun shekara-shekara, inda ta dakatar da dukkan ayyukanta na dokoki har zuwa ranar Litinin, 23 ga watan Satumba, 2025.
Wannan mataki ya zo ne a karshen zaman majalisa da aka gudanar a ranar Laraba, 23 ga Yuli, 2025 a zauren Majalisar Dokoki da ke babban birnin tarayya, Abuja.

Source: Twitter
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, ne ya bayyana hakan bayan ya kammala jawabinsa jiya Laraba, kamar yadda The Nation ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar Wakilai ta tafi hutun shekara
Ya ce za su tafi hutun ne bayan da aka gabatar da kudurin, aka mara masa baya, sannan kuma duka ƴan Majalisa suka amince da shi ba tare da wani sabani ba.
Wannan hutu na wata biyu na cikin tsarin kalandar shekara na ayyukan Majalisar Dokoki ta Najeriya.
Kakakin Majalisar ya bayyana cewa hutun ba kawai hutu ne na jiki ba, har ila yau dama ce ga ‘yan majalisa su koma mazabunsu domin ƙara kusantar da kansu ga al’umma.
Tajudeen Abbas ya ja hankalin ƴan Majalisa
Haka zalika ya ja hankalin abokan aikinsa da su rika tattaunawa da shugabanni da kungiyoyin al'umma na mazaɓunsu don warware matsaloli da bukatun gaggawa da suka taso a yankuna.
Tajudeen ya buƙaci ƴan Majalisa su sa ido kan yadda ake aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya da aka kawo yankunansu domin yana cikin haƙƙokin da suka rataya a kansu.
“Wannan lokaci ne da zai bai wa kowane dan majalisa damar karfafa dangantaka da jama’arsa da kuma duba ainihin halin da ake ciki a mazabunsa,” in ji Kakakin Majalisar.

Source: Twitter
Yadda aka yi zaman ƙarshe kafin tafiya hutu
A zaman ƙarshe da Majalisar Wakilai ta yi ranar Laraba ta tattauna kan batutuwa masu muhimmanci da suka shafi tattalin arziki, tsaro, da walwalar jama’a.
Idan baku manta ba, ƴan Majalisa uku daga jihohin Edo da Osun sun sanar da sauya sheka daga PDP zuwa APC, lamarin da ya kusa tayar da rigima a zaman jiya.
Bayan kammala duka abubuwan da aka gabatar a Majalisar ne Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ayyanan tafiya hutun shekara na tsawon watanni biyu, rahoton Leadership.
Majalisar za ta koma aikinta a ranar 23 ga Satumba 2025, tare da ci gaba da nazari da amincewa da kudurori da sauran batutuwan da suka shafi cigaban Najeriya.
Abin da Buhari ya faɗawa Kakakin Majalisa
A wani rahoton, kun ji cewa Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya tuna nasihar da marigayi Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari ya masa.
Tajudden ya ce ya haɗu da Buhari a Birtaniya bayan ya zama kakakin Majalisar wakilai, kuma ya yi masa nasiha yar gajera amma mai matuƙar amfani.
Ya ce ya ɗauki Buhari a matsayin shugaba, abokin shawara, jagora wanda ya taimaka masa wajen tafiyar da harkokin jama'a yadda ya dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


