Ana Sa Ran Ruwan Sama Zai Sauka a Katsina, Kano da Jihohin Arewa 17 Ranar Alhamis

Ana Sa Ran Ruwan Sama Zai Sauka a Katsina, Kano da Jihohin Arewa 17 Ranar Alhamis

  • Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu tsawa da ruwan sama mai ƙarfi a jihohin Arewa a ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025
  • Jihohin da za a samu saukar ruwan saman sun hada da Taraba, Bauchi, Yobe, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Borno, Gombe, da Adamawa
  • Hukumar ta gargadi jama'a da su yi taka tsantsan da ambaliya, sannan su guji yin tuki yayin da ake ruwa don gudun hatsari

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Hukumar Kula da Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen saukar ruwan sama na yau Alhamis, 24 ga Yulin 2025.

Kamar kullum, a yau ma, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama mai karfi da tsawa a jihohi daban-daban na ƙasar.

Hukumar NiMet ta ce za a iya samun ruwan sama da iska a sassan Najeriya a ranar Alhamis
Ruwan sama mai karfi tare da iska na sauka a wasu sassan Arewacin Najeriya. Hoto: Sani Hamza / Staff
Source: Original

NiMet ta fitar da wannan hasashen ne a daren ranar Laraba, 23 ga Yulin 2025 a shafinta na X, inda ta ce hasashen na ranar 24 ga Yulin 2025 ne.

Kara karanta wannan

Manoma na cikin tashin hankali, ambaliyar ruwa ta yi barna a garuruwa 7 na Kebbi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen yanayi a jihohin Arewa

Da Safiyar Alhamis, ana sa ran samun tsawa da ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Katsina, Jigawa, Kaduna, Kano, Zamfara, Kebbi, Bauchi, Borno, Yobe, da Adamawa.

Daga maraicce zuwa dare kuwa, ana sa ran samun tsawa tare da ruwan sama mai ƙarfi a jihohin Arewa kamar Taraba, Bauchi, Yobe, Sokoto, Kebbi, Kaduna, Borno, Gombe, da Adamawa.

Harilayau, a safiyar Alhamis din dai, NiMet ta ce akwai yiwuwar ruwan sama marar karfi zuwa mai karfi a sassan Abuja da jihohin Neja, Benuwe, Kogi da Nasarawa.

Da yammaci zuwa dare kuwa, ana sa ran ruwan sama mai dan ƙarfi zai sauka a sassan Abuja da jihohin Plateau, Nasarawa, Kogi, Benuwe, da Neja.

Hasashen yanayi a jihohin kudancin Najeriya

Da safiyar Alhamis, NiMet ta yi hasashen samun hadari amma da hudar rana a wasu jihohin Kudancin Najeriya.

Amma akwai yiwuwar samun ruwa da safiyar ranar a sassan jihohin Rivers, Bayelsa, Cross River, da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

'Ku shirya': Kano, Bayelsa da jihohi 33 da za a sheka ruwa da iska mai karfi

Da yamma zuwa dare kuwa, za a iya samun ruwan sama mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Oyo, Ondo, Imo, Abia, Enugu, Ebonyi, Anambra, Delta, Bayelsa, Rivers, Cross River, da Akwa Ibom.

Hukumar NiMet ta ce za a samu saukar ruwan sama marar karfi a wasu sassan jihohin Arewa da Kudu
Iska mai karfi na kadawa yayin da ruwan sama ke sauka a wasu sassan Arewacin Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Shawarwarin da NiMet ta bai wa jama'a

A cikin sanarwar, NiMet ta bayyana cewa

"Ruwan sama na iya zuwa da iska mai ƙarfi; ku kasance masu lura da hakan tare da ɗaukar matakan kariya.
"Akwai bukatar direbobi su guji tuƙi a lokacin ruwan sama mai yawa domin kauce wa haɗurra. Sannan a guji neman mafaka karkashin bishiya don gudun faduwar rassa.
"Ana so kamfanonin jiragen sama su nemi bayanan yanayin da suka shafi filayen jiragen sama daga NiMet domin tsara zirga-zirgar su."

Jihohi 8 da za su iya fuskantar ambaliya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, NiMet ta yi gargaɗin yiwuwar ambaliya a wasu sassan Najeriya yayin da aka shiga tsakiyar damina a watan Yuni 2025.

Jihohin da ke cikin barazanar ambaliya sun haɗa da Kano, Kaduna, Neja, Nasarawa, Kwara, Sokoto, Filato da babban birnin tarayya Abuja, inda ake sa ran ruwan sama mai ƙarfi zai sauka.

NiMet ta shawarci manoma da su ɗauki matakan kariya, ta hanyar share magudanar ruwa da kuma amfani da sababbin hanyoyin noma da suka dace da yanayi domin kauce wa asara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com