Bayan Hana Ta Komawa Majalisa, Sanata Natasha Ta Gamu da Cikas wajen Ficewa Najeriya

Bayan Hana Ta Komawa Majalisa, Sanata Natasha Ta Gamu da Cikas wajen Ficewa Najeriya

  • Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gamu da tsaiko lokacin da ta yi niyyar barin Najeriya zuwa birnin Landan
  • Jami'an hukumar shige da fice sun ƙwace fasfo ɗin ta a filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da ke birnin tarayya Abuja
  • Ƙwace fasfo ɗin ya kawo mata tsaiko wajen shiga jirgin da zai tafi zuwa birnin Landan da safiyar ranar Alhamis

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi.

FCT, Abuja - Jami’an hukumar shige da Fice ta Najeriya (NIS) da ke filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, sun ƙwace fasfo ɗin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Jami'an na hukumar shige da ficen sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ne da safiyar ranar Alhamis.

An kwace fasfon Sanata Natasha a Abuja
Jami'an hukumar shige da fice sun ƙwace fasfon Sanata Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa lamarin ya auku ne lokacin da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, take ƙoƙarin shiga jirgin British Airways zuwa birnin Landan.

Kara karanta wannan

Damagum: Shugaban PDP ya fito fili ya fadi wadanda suka assasa matsalolin jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ƙwace fasfon Sanata Natasha a Abuja

Ganau a filin jirgin sun bayyana cewa Sanatar ta iso tashar jirgin na ƙasa da ƙasa ne tare da mijinta, Cif Emmanuel Uduaghan, amma sai jami’an shige da fice suka dakatar da ita tare da ayyana ta a matsayin “barazana ga tsaron ƙasa.”

Lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis, 24 ga Yuli, 2025, kafin a fara shiga jirgin da zai tashi zuwa Landan.

Fasinjoji sun ce Sanata Natasha ta kasance cikin nutsuwa da kwanciyar hankali duk tsawon lokacin da aka tsare ta, inda ta nace cewa jami’an ba su da hurumin riƙe fasfonta.

Ta riƙa gaya musu cewa kotu ba ta ba su hurumin riƙe mata fasfo ba, rahoton jaridar Premium Times ya tabbatar.

“Kotu bata ba ku wannan dama ba. Ba ku da ikon rike fasfona"

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Babu wani ƙarin bayani na hukuma da aka bai wa Sanatar a lokacin da aka kwace fasfon, lamarin da ya ƙara hura wutar zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya yi murabus daga PDP a zungureriyar wasikar shafi 9

An hangi mijinta, Cif Uduaghan, yana ta kiran waya cikin gaggawa yayin da tsaikon ke ci gaba da ɗaukar lokaci.

An kwace fasfon Sanata Natasha a Abuja
Jami'an NIS sun dawo da fasfon Natasha Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Original

An dawo da fasfon Sanata Natasha

Bayan ƴan mintuna, an dawo mata da fasfonta ba tare da wani ƙarin bayani ba, lamarin da ya ba ta damar wucewa cikin gaggawa har ta samu shiga jirgin kafin a rufe ƙofa.

Lamarin ya tayar da ƙorafi da fargaba a tsakanin wasu daga cikin fasinjojin, inda masu kallo suka bayyana shi a matsayin abin kunya da kuma yiwuwar amfani da iko wajen wuce gona da iri.

Hukumar shige da fice ta ƙasa da kuma ofishin shugaban majalisar dattawa, har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba.

Natasha ta caccaki shugaban majalisar dattawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi kalamai masu kaushi kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.

Sanatar ta soki Akpabio ne bayan jami'an tsaro sun hana ta komawa bakin aiki a majalisar dattawa.

Ta gargaɗi shugaban majalisar dattawan cewa ya daina ɗaukar kansa a matsayin wanda ya fi ƙarfin kundin tsarin mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng