Dukan Islamiyya Ya Jawo Babbar Matsala, Fitaccen Ɗan TikTok Ya Bar Addinin Musulunci

Dukan Islamiyya Ya Jawo Babbar Matsala, Fitaccen Ɗan TikTok Ya Bar Addinin Musulunci

  • Fitaccen ɗan TikTon, Habeeb Hamzat wanda aka fi sani da Peller ya tabbatar wa mabiyansa cewa ya bar addinin musulunci da yake kai a baya
  • Peller ya bayyana cewa dukan da ya wuce ƙima da azabar da aka masa a makarantar Islamiyya ne suka tunzura shi ya koma kiristanci
  • Wannan dai na nuna illar dukan yara fiye da ƙima a makarantun Islamiyya da na Boko, domin ya kan sa su kara kangare wa maimakon gyara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Shahararren mai amfani da kafar sada zumunta ta TikTok, Habeeb Hamzat ya tabbatar da cewa ya yi ridda daga addinin musulunci.

Kara karanta wannan

An sake neman dalibai kusan 100 an rasa bayan hari a makarantar Neja

Habeeb, wanda aka fi sani da Peller ya bayyana abubuwan da suka faru da shi marasa daɗi, waɗanda suka tunzura shi ya canza addini daga Musulunci zuwa Kiristanci.

Fitaccen ɗan TikTok, Peller.
Dan TikTok, Peller ya nuna ɓacin rana kan abin da aka masa a makarantar Islamiyya Hoto: @Peller
Source: Instagram

A rahoton da Tribune Nigeria ta tattaro, Peller ya ce ba zai manta irin azabtarwa da dukan da ya wuce ƙima da aka masa a makarantar Islamiyya ba tun yana yaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗan TikTok ya faɗi dalilin barin Musulunci

A yayin wani taron kai tsaye da ya yi tare da mabiyansa, Peller ya ba su labarin lokacin da yake zuwa makarantar Islamiyya, wadda ake kira Ile Kewu a jihar Legas.

Ya ce a wannan makaranta, malaman da ke koyar da su karatun Alƙur'ani da sauransu sun rika dukansa tare da azabtarwa iri-iri, wacce ya ga ba zai iya jurewa ba.

Ya tabbatar wa mabiyansa a shafin TikTok cewa ko da kuwa ba duka malamai ke haka ba, shi dai ya bar addinin Musulunci ya koma Kiristanci.

Peller ya ce:

“Ni ba Musulmi ba ne, ni Kirista ne a yanzu domin ina zuwa coci. Na sha duka sosai a lokacin ƙuruciyata a makarantar Islamiyya. Wannan ne ya sa na daina zuwa.”

Kara karanta wannan

Sace dalibai: Atiku da Kwankwaso sun fadawa Tinubu matakan da ya kamata ya dauka

Peller ya tuna abin da ya faru da shi a Islamiyya

Ya bayyana cewa makarantar da ake sa ran za ta koya masa tarbiyya da ƙaunar addini ta zama wata hanya ta tsangwama da firgita shi, abin da a ƙarshe ya tilasta masa barin addinin Musulunci.

Peller ya ce raunukan da ya samu a wancan lokaci na rayuwarsa sun taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar komawa Kiristanci, rahoton PM News.

Dan TikTok ya sauya addini a Legas.
Peller ya nuna damuwa kan yadda aka azabtar da shi a yarinta Hoto: @Peller
Source: Instagram

Ya ƙara da cewa irin azabar da ya fuskanta tun yana yaro ya sa ya nisanci karatun addini gaba ɗaya, kuma hakan ya taka rawar gani a shigarsa addinin Kirista daga bisani.

Abin lura: Masana suna ganin cewa dukan ƙananan yara fiye da ƙima a makarantun boko da Islamiyya ba ya haifar da ɗa mai ido, domin maimakon gyara sai dai ya sa yara ɗaukar matakin da bai dace ba.

Matar mawaƙi ta Musulunta a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa mawaƙi Juma Jux ya bayyana yadda ya samu nasarar jawo hankalin matarsa, Priscilla Ojo har ta musulunta bayan aurensu.

Kara karanta wannan

Asiri ya bankadu: An kama magidanci yana neman sulalewa da gawar matarsa a babur

Fitaccen mawaƙin ya faɗi ƙalubalen da ya fuskanta wajen fahimtar da Priscilla addinin musulunci cikin hikima da dabaru kafin Allah ya nuna mata ta dawo hanyar shiriya.

Ya ce malamai ne suka riƙa koya masa yadda zai tattauna da Priscilla kan addinin Musulunci cikin hikima, kuma ta haka ne ya samu nasara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262