Musulunci Ya Samu Ƙaruwa a Najeriya, Mawaƙi Ya Ja Ra'ayin Ɗiyar Ojo Ta Karɓi Shahada
- Mawaƙi Juma Jux ya bayyana yadda ya samu nasarar jawo hankalin matarsa, Priscilla Ojo har ta musulunta bayan aurensu
- Ya ce ya yi amfani da shawarwarin da malamai suka ba shi wajen amfani da hikima yayin hira da matarsa kan addinin musulunci
- Ya ce ya ɗan sha wahala kaɗan amma abin farin cikin, daga bisani ta fahimta kuma ta karɓi addinin musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Fitaccen mawakin nan da ake danganta wa da ƙasashe biyu, Najeriya da Tanzania, Juma Jux ya bayyana yadda ya yi nasarar jawo matarsa zuwa addinin Musulunci.
Juma Jux, ya ce matarsa, Priscilla Ojo, ta musulunta tun kafin shagulgulan bikin aurensu da aka yi a watan Afrilu a jihar Legas.

Source: Twitter
A wata hira da ya yi kwanan nan, mawakin ya faɗi ƙalubalen da ya fuskanta wajen fahimtar da Priscilla addinin musulunci kafin ta musulunta, Tribune Nigeria ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matar mawaƙin dai ta kasance ‘yar fitacciyar jarumar masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya Nollywood, Iyabo Ojo.
Yadda mawaƙi Juma Jux ya jawo matarsa
Juma Jux, wanda musulmi ne ya ce ya sha wahala amma ya jajirce tare da hakuri, juriya, da taimakon malaman addinin musulunci har matarsa ta sauya addini.
Ya ce shawarwarin malamai da wasu musulmai sun taimaka masa wajen kwaɗaitar da Priscilla kyaun addinin musulunci kuma ta musulunta ba tare da tilasta mata ba.
Musulunci ya samu ƙaruwa a Najeriya
Da aka tambaye shi kan yadda ya musuluntar da matarsa, Jux ya bayyana cewa ya dogara da darussa daga shugabannin addini waɗanda suka ƙarfafa shi da ya tafiyar da lamarin cikin nutsuwa da tausayi.
Ya ce malamai ne suka riƙa koya masa yadda zai tattauna da Priscilla kan addinin Musulunci cikin hikima.
Wannan hanyar da take cike da hakuri da juriya, inji shi, ita ce ta taimaka wa Priscilla wajen fahimtar Musulunci sosai har ta amince ta rungumi addinin.

Source: Instagram
Jux ya sha wahalar musuluntar da Priscilla?
Da aka tambaye shi ko ya sha wahala wajen jawo matarsa ta shiga musulunci, mawaƙin ya ce:
"Eh kaɗan, amma a gefe guda, na rika ɗaukar darussa daga malamai da shugabannin addini sosai.
"Sun riƙa koya min yadda zan yi amfani da hikima wajen shawo kanta. Sun faɗa mani cewa, ‘Ka tafiyar da ita a hankali, ka koya mata wannan da wancan, ka gaya mata kaza da kaza.’ Na ɗauki lokaci, amma daga baya sai ta fahimta.”
The Nation ta ruwaito cewa Juma Jux da Priscilla Ojo sun yi aure a wani gagarumin biki da aka yi a Legas ranar Asabar, 19 ga Afrilu, 2025.
Me yasa musulmai ke yawan kara aure?
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Majalisar malamai ta Kano, Sheikh Ibrahim Khaleel ya taɓo batun ƙarin auren da musulmi ke yi.
Malamin addinin musuluncin ya bayyana cewa maza na da mabambantan dalilai da suke sanya su ƙara aure a rayuwarsu.
Shehin Malamin ya kuma nuna cewa a yanayin tsarin halittar maza, babu wanda aka yi domin ya zauna da mace ɗaya a rayuwarsa.
Asali: Legit.ng

