Sojoji Sun Dakile Mugun Shirin 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Mai Daukar Bidiyo domin Yada Karya

Sojoji Sun Dakile Mugun Shirin 'Yan Ta'adda, Sun Kashe Mai Daukar Bidiyo domin Yada Karya

  • Dakarun sojojin Najeriya sun sake yin galaba kan mayakan kungiyar ISWAP a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Sojojin sun kashe dan kungiyar ISWAP ɗin da ke ɗaukar bidiyo a yayin da suka dakile harin da aka kai Bitta, Gwoza
  • Sojoji sun kwato na’urar daukar bidiyo mai ƙarfi daga hannun ‘yan ta’addan da suke shirin yaɗa farfaganda

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Dakarun sojoji a Najeriya sun samu gagarumar nasara kan mayakan kungiyar ta'addanci ta ISWAP.

Sojojin sun samu galaba a fagen yaƙi da ta’addanci bayan sun kashe ɗan bindiga da ke daukar bidiyo.

Sojoji sun hallaka mayakan ISWAP a Borno
Sojoji sun samu galaba kan mayakan ISWAP a Borno. Hoto: HQ Nigeria Army.
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa harin ya afku ne a garin Bitta da ke karamar hukumar Gwoza.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Boko Haram ke kai hare-hare a Borno

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga a Neja, an samu asarar rayuka

Wannan nasara ya biyo bayan ta'asa da yan kungiyar Boko Haram ke yi a Borno ba dare ba rana.

A yan kwanakin nan yan ta'adda da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun yi aika-aika a jihar Borno inda suka yi garkuwa da wasu mutane a kan hanya.

Miyagun sun tare wata motar inda suka yi awon gaba da wani jami'in gwamnati lokacin da yake tsaka da tafiya tare da wasu mutane.

An ce bayan sace jami'in gwamnatin dai, an tura jami'an tsaro domin bin sawun ƴan ta'addan da yiwuwar ceto shi.

An kashe mayakan ISWAP a Borno
Sojoji sun yi nasaar dakile harin yan kungiyar ISWAP. Hoto: Legit.
Source: Original

An kwato na'urar bidiyo daga kungiyar ISWAP

Majiyoyi sun gano cewa sojojin ba sun dakile harin ba ne kawai, har ma sun kwato na’urar bidiyo mai muhimmanci daga hannun ‘yan ta’addan.

Wasu majiyoyi na tsaro sun tabbatar cewa ‘yan ta’addan sun shirya amfani da harin don samar da bidiyon.

Ana sa ran bayan yan ta'addan sun yi nasara za su yi amfani da bidiyon domin razana mutane da yaɗa ƙaryar nasarar farmakin.

An hallaka mai daukar bidiyon ISWAP

Kara karanta wannan

Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu

An gano mai daukar bidiyon ISWAP ne ta hanyar kayan da ke jikinsa yayin da ake cigaba da arangama a fagen daga.

Daga cikin abin da aka kwato har da na’urar bidiyo mai inganci da jaka na kayan daukar hoto wanda aka shirya domin yada farfaganda game da tsaro.

An kashe shi a tsakiyar musayar wuta, kuma an gano bidiyoyin da ke cikin na’urar da za a yi amfani da su wajen binciken bayanan sirri.

Sojoji sun hallaka yan ta'adda a Borno

Mun ba ku labarin cewa dakarun sojojin Najeriya sun kai hare-hare kai maɓoyar yan ta'addan Boko Haram da ISWAP a jihohin Adamawa da Borno.

Jami'an tsaron sun samu nasarar hallaka yan ta'adda da dama a hare-haren da suka kai musu wanda ya kara musu kwarin guiwa kan yaki da yan ta'adda.

Hakazalika an tabbatar da cewa sojoji sun kwato makamai, babura, kekuna da sauran kayayyaki daga hannun yan ta'addan a yankin da ake fama da matsalar tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.