'Yan Najeriya Sun Yi wa NNPCL Dirar Mikiya duk da Ragin Farashin Litar Fetur
- Wasu ƴan Najeriya sun ce rage farashin fetur zuwa N910 da kamfanin NNPCL ya yi na wani matakin da za a yi alfahari da shi ba ne
- Wannan na zuwa a matsayin martani ga murnar da kamfanin NNPCL ke yi na cikar sabon shugabanta, Bayo Ojulari kwana 100 a bakin aiki
- Daga cikin nasarorin da kamfanin ya ce Ojulari ya cimma akwai haɗin gida matatar Ɗangote da sauran ayyukan haɓaka samar da fetur
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Ƴan Najeriya da dama sun bayyana fushinsu da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) bayan da ya sanar da rage farashin litar fetur zuwa N910.
Jama'a na ganin rage farashin litar man fetur zuwa N910 bai wadatar ba duba da halin ƙuncin tattalin arzikin ƙasar nan ke ciki.

Source: Getty Images
Wannan ya zo a matsayin martani ga sakon da NNPCL ya wallafa a shafin X da ke nuna ci gaban da sabon shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ya samu a cikin kwanaki 100 da fara aiki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya faɗi nasarorin Bayo Ojulari
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa NNPCL ya fitar da sanarwa a ranar 23 ga Yuli, 2025, inda ya bayyana wasu daga cikin nasarorin da Ojulari ya samu.
Daga cikin nasarorin ta ce akwai haɗin gwiwa da Matatar Dangote da kuma hangen nesa na ganin Afrika ta dogara da kanta wajen tace man fetur.
Har ila yau, NNPCL ta ce tana shirin ƙara yawan fitar da danyen mai zuwa ganga miliyan biyu a rana nan da shekarar 2027 da kuma jawo jarin $30bn zuwa 2030.
Amma jama’a da dama na ganin NNPCL ya kauce wa manyan matsalolin da ke addabar ɓangaren makamashi a ƙasar nan.
Jama'a sun caccaki kamfanin NNPCL
Duk da nasarorin da NNPCL ya ce an samu a cikin kwanaki 100 da samun sabon shugaba, jama'ar ƙasar nan ba su gamsu da iƙirarin kamfanin ba.
@EnergyWatchNG ya ce:
“NNPCL na murnar kwanaki 100 da jarin nasarori, amma mutane na cigaba da tsayawa layi suna sayen fetur a N910. Ina bunƙasa makamashi da aka yi alkawari? Matatun mai na kasa ba sa aiki, har yanzu muna shigo da mai daga waje."

Source: Getty Images
@LagosAnalyst ya ce:
“Yayin da NNPCL ke cewa ta cimma nasarori, majalisar dattawa na binciken Naira tiriliyan 210 da ba a bayyana inda suka shige ba. Ta yaya za a yi murna idan ba a iya bada bayanin inda kuɗin suka tafi ba?
NNPCL ya rage farashin litar fetur
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin mai na ƙasa ya sake rage farashin litar fetur a gidajen man da ke ƙarƙashinsa a babban birnin tarayya Abuja.
Wannan sauyin farashi ya zo ne mako guda bayan makamancinsa da aka yi a baya, yayin da jama’a ke ci gaba da koka wa kan tsadar fetur a Najeriya.
Rahotanni sun ce an rage farashin litar fetur zuwa N890 a wurare da dama da suka haɗa da rukunin gidajen gwamnatin tarayya da ke Kubwa da Wuse Zone 3, a Abuja.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

