Matasa 50,000 za Su Samu Aiki a Hadakar Noman da Dangote Ya Yi da Neja
- Gwamnatin Neja da Aliko Dangote sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Naira tiriliyan 1.8 domin bunkasa noman shinkafa
- Yarjejeniyar da aka kulla na kunshe da samar da gonakin shinkafa da tallafa wa manoma 50,000 a fadin jihar Neja
- Alhaji Aliko Dangote ya ce jihar Neja ta shiga sahun jihohin da kamfaninsa ke gina injunan casar shinkafa a Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Niger - Gwamnatin jihar Neja ta cimma yarjejeniya da kamfanin Dangote domin samar da shinkafa da kuma sayar da ita cikin tsari.
An sanya hannu kan wannan yarjejeniya ne a ofishin shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote da ke birnin Lagos.

Source: Facebook
Legit ta samu bayanai kan yarjejeniyar ne a cikin wani sako da hadimin gwamnan Neja, Balogi Ibrahim ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamfanin Niger Foods Security Systems and Logistics ne zai wakilci gwamnatin jihar Neja a wannan hadaka da ta kai darajar Naira tiriliyan 1.8.
Neja, Dangote za su samar da ayyuka 50,000
Shugaban kamfanin Niger Foods, Sammy Adigun, ya bayyana cewa jihar Neja za ta fara noma shinkafa a filaye masu fadin hekta 25,000 tare da tallafa wa manoma 50,000.
Ya bayyana cewa hadakar za ta gudana ne na tsawon shekaru 10, inda za a samar da ayyukan yi kai tsaye har guda 50,000 a fadin jihar.
Dangote ya bayyana amfanin yarjejeniyar
Shugaban kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya ce yarjejeniyar ta biyo bayan tattaunawa da dama domin ganin an bunkasa noma da wadatar abinci a kasar nan.
Ya ce kamfaninsa ya zuba jari sosai a bangaren injunan casar shinkafa da gonaki a jihohi da dama don samar da aikin yi da tallafawa manoma.
Dangote ya bayyana cewa jihar Neja yanzu ta zama cikin jihohi shida da kamfaninsa ke gina injunan casar shinkafa domin inganta sarrafa amfanin gona.
Ya bukaci karin hadin gwiwar ‘yan kasuwa da gwamnati a fannin noma don bunkasa tattali, yana mai cewa kashi 90 ta tattalin kasar na hannun 'yan kasuwa masu zaman kansu.
Yarjejeniyar za ta amfani manoma a kasa
Dangote ya ce hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu za ta taimaka wajen rage matsalolin tattalin arziki da na zamantakewa ta hanyar samar da ayyuka.
Ya yaba wa Gwamna Mohammed Umaru Bago bisa kokarinsa a fannin noma, musamman yadda ya dukufa wajen noman zamani a jihar.

Source: Facebook
Gwamnan Neja ya yi alkawarin ciyar da kasa
Gwamna Mohammed Umaru Bago ya bayyana farin cikinsa da wannan yarjejeniya, yana mai cewa jihar Neja na da isasshen ruwa da filaye da za su kawo sauyi a bangaren noma.
Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da amfani da wannan dama wajen habaka tattalin arziki, kara samar da ayyuka da kuma ciyar da Najeriya gaba baki daya.
Za a samar da ayyuka ta noman waken suya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta kaddamar da shiri na musamman kan noman waken suya.
Ministan noma, Sanata Abubakar Kyari ya bayyana cewa ana fatan shirin zai samar da ayyuka ga matasa miliyan 1 a jihohi.
Gwamnan jihar Benue da ya halarci taron ya bayyana cewa jihar sa ce ke kan gaba wajen noman waken suya a fadin Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


