Duniya kenan: Gwamna Ya Ji ba Daɗi, Hadiminsa kuma Tsohon Ɗan Majalisa Ya Rasu

Duniya kenan: Gwamna Ya Ji ba Daɗi, Hadiminsa kuma Tsohon Ɗan Majalisa Ya Rasu

  • Gwamna Inuwa Yahaya na Gombe ya bayyana jimaminsa kan rasuwar hadiminsa na musamman a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Marigayi Mamman Alkali ya rasu a yau Laraba 23 ga watan Yulin 2025 a Gombe bayan gajeriyar rashin lafiya da ya sha fama da ita
  • Inuwa ya ce Mamman Alkali mutum ne mai amana, hazikin dan siyasa kuma dan dimokuradiyya na gaskiya da ya sadaukar da kansa wajen hidimar jama’a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar wani tsohon dan majalisa kuma hadimin gwamna na musamman.

Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana alhini da jimamin rasuwar hadiminsa na musamman kan harkokin majalisa.

Hadimin gwamna ya rasu a Gombe
Gwamna Inuwa ya yi jimamin mutuwar hadiminsa. Hoto: Isma'ila Uba Misilli.
Source: Facebook

Yaushe 'dan siyasar Gomben ya rasu?

Bayanin na cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan, Isma'ila Uba Misilli ya wallafa a shafin Facebook a yau Laraba 23 ga watan Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya yi zarra, Abba ya ƙara samun lambar gwarzon gwamnoni a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta tabbatar da cewa marigayin Hon. Mamman Alkali, JP ya rasu a yau Laraba 23 ga watan Yulin 2025 bayan fama da jinya na wani lokaci.

Gwamna Inuwa ya ce marigayin ya kasance jajirtaccen ma’aikaci, amintaccen aboki kuma dan siyasa mai gaskiya wanda ya yi hidima da kishi da tawali’u.

A cikin sanarwar, Gwamna Inuwa Yahaya ya ce:

“Mamman Alkali aboki ne na hakika, gogaggen dan majalisa kuma dan dimokuradiyya mai kwazo da halin nutsuwa. Zamu yi rashin sa matuka.”

Gwamna ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan mamacin

Gwamnan ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa, ’yan siyasa da kuma al’ummar Bangunji da ke karamar hukumar Shongom.

Ya yi addu’ar Allah ya jikansa, ya ba iyalan marigayin hakurin jure wannan babban rashi da ta girgiza jihar baki daya.

Gwamna ya kadu bayan mutuwar hadiminsa
Gwamna Inuwa ya jajanta da hadiminsa ya rasu. Hoto: Muhammadu Inuwa Yahaya.
Source: UGC

Mukaman da marigayin ya rike a baya

Hon. Mamman Alkali ya taba rike mukaman siyasa da dama ciki har da Kansila da shugaban masu rinjaye a majalisar dokoki ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Bayan mutuwar Buhari, tsohon gwamna ya ji kunya kan kalamansa gare shi da Fulani

Ya rike mukamin mataimakin shugaban ma’aikata ga Gwamnan Gombe, kuma ya kasance mamba a hukumar makamashi ta kasa a 2019.

Baya ga haka, ya kasance mamba a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben shekarar 2023 da ta gabata.

Dangin marigayin sun bayyana cewa za a yi jana’izarsa ranar Asabar 26 ga Yulin 2025 a garin Bangunji da ke karamar hukumar Shongom.

Gombe: Jigon PDP ya riga mu gidan gaskiya

Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar PDP a Gombe ta yi babban rashi bayan rasuwar tsohon sakataren yankin Arewa maso Gabas, Kabiru Bappah Jauro a birnin Abuja.

Farfesa Isa Ali Pantami ya yi jimamin rasuwar Bappah Jauro inda ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin tare da yi masa addu'ar fatan samun rahama.

Marigayin ya rasu a wani asibiti na Turkiyya da ke Abuja bayan fama da doguwar rashin lafiya, PDP ta ce rasuwar ta yi matuƙar taba ta duba da gudunmawar da ya ba ta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.