Ana Halin Matsi, Tinubu Zai Karɓo Bashin $347m, Ya Fadi yadda Zai Kashe Su
- Shugaba Bola Tinubu na neman amincewar majalisa domin ɗaukar karin bashi na $347m don aikin titin bakin teku
- Ya ce karin kuɗin aikin daga $700m zuwa $747m ne ya sa ake buƙatar sabon bashi don cika tsarin bashin 2025-2026
- Majalisar wakilai ta tura bukatar zuwa kwamitin hada-hadar bashi domin duba cancanta kafin daukar mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya aike da wasika zuwa majalisar wakilai yana neman amincewa da karin wani bashi.
Shugaba Tinubu na neman amincewar majalisar domin karbar bashin $347m daga waje domin cike gibin wasu ayyuka.

Asali: Twitter
Musabbabin neman bashi da Tinubu ke yi
Wannan bashi zai kasance cikin sabon tsarin daukar bashi na shekarar 2025 zuwa 2026 da gwamnatin tarayya ke shirin aiwatarwa, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban majalisar wakilai, Abbas Tajudeen, ne ya karanta wasikar Shugaban kasa a zaman majalisar na ranar Laraba, 23 ga Yulin 2025.
Tinubu ya bayyana cewa karin kudin da ake bukata don aikin titin bakin teku na Lagos zuwa Calabar ne ya haddasa wannan bukata.
Aikin titin, wanda da farko aka kiyasta da $700m, yanzu yana bukatar $747m, karin kuɗi har $47m kenan.
Amfanin da bashin zai yi ga cigaban kasa
Shugaban ya ce an zabi wannan aikin ne bisa tsarin tantancewa na tattalin arziki da tasirinsa ga ci gaban kasa baki daya.
Ya kara da cewa, aikin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunkasa fasaha, tallafa wa kasuwanci da kuma rage talauci a kasar.
Tinubu ya ce saka aikin cikin tsarin sabon bashi zai taimaka wajen kammala tsarin kudi da aiwatar da aikin cikin lokaci
Abin da majalisa ta yi kan neman bashi
Majalisar wakilai ta tura bukatar shugaban kasa zuwa kwamitin hadin gwiwa kan kudi, tallafi, lamuni da sarrafa basussuka.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2
Kwamitin zai duba hujjoji na fasaha da na kudi kafin ya mika rahoto ga dukan majalisar wakilai domin daukar matsaya.
Tun da farko, a watan Nuwamba 2023, Tinubu ya nemi amincewar bashi na $7.8bn da Yuro miliyan 100 don manyan ayyuka.

Asali: Facebook
Majalisa ta amincewa Tinubu karbar bashin $21bn
A watan Maris 2025, ya sake neman bashi na waje har $21.5bn da kuma fitar da takardun lamuni na gida na N757.9bn.
Majalisar dattawa ta amince da wannan sabon tsarin daukar bashi a zaman da ta yi a watan Maris din da ya gabata.
Hukumar kula da bashi ta kasa (DMO) ta bayyana cewa, zuwa Maris 2025, jimillar bashin Najeriya ya kai ₦121tr.
Ko da yake akwai fargaba kan yadda ake ci gaba da karbar bashi, gwamnati na cewa bashin na da saukin biya kuma yana da amfani.
Gwamnati ta ce karbar bashin yana taimakawa wajen cike gibi a ayyukan ababen more rayuwa da kuma farfado da tattalin arziki.
Tinubu ya biya bashin $.4m na Buhari
Kun ji cewa Gwamnatin Najeriya karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta tabbatar da kammala biyan bashin asusun ba da lamuni (IMF).
Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa, Mohammed Idris ne ya sanar da hakan da yake hira da manema labarai.
A kwanakin baya ne IMF ya cire sunan Najeriya a jerin kasashe masu tasowa da yake bi bashin kudi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng