Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga a Neja, an Samu Asarar Rayuka

Sojoji Sun Gwabza Kazamin Fada da 'Yan Bindiga a Neja, an Samu Asarar Rayuka

  • Sojojin haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun dakile harin 'yan ta’adda a Neja, inda suka kashe miyagu da dama a artabun
  • Dakarun sun kaddamar da harin ne bayan samun bayanan sirri, tare da goyon bayan rundunar sama da kuma kwato makamai
  • Duk da wannan nasarar, soja guda ɗaya ya rasa ransa, yayin da rundunar ta sha alwashin ci gaba da yaki da ta’addanci a yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Neja - Sojojin haɗin gwiwa na Operation Fansan Yamma sun dakile wani hari da 'yan ta’adda ke shirin kaiwa a ƙaramar hukumar Rijau da ke jihar Neja.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kakakin rundunar Operation Fansan Yamma, Kyaftin David Adewusi, ya ce sojoji sun fafata da 'yan ta'addar ne a ranar 22 ga Yulin 2025.

Kara karanta wannan

Sojoji sun fatattaki zugar 'yan ta'adda, an aika kusan 95 ga mahaliccinsu

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda da dama a wani samame da suka kai jihar Neja, Zamfara da Kebbi
Sojojin Najeriya a kan motar sulke da wadda ba ta sulke ba suna rangadi a Arewa maso Gabas. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'adda a Neja

Channels TV ta rahoto Kyaftin David Adewusi yana cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Dakarun sojin sun murkushe wani gungun 'yan ta’adda da suka taso daga yankin Baban Doka na ƙaramar hukumar Maru a jihar Zamfara, suna kokarin kai hari ƙauyukan Ragada da Warari a ƙaramar hukumar Rijau.”

Ya ƙara da cewa sojojin haɗin gwiwa daga sassan Mariga da Zuru sun kai hari cikin tsari a kusa da ƙauyen Inana da ke Rijau, inda suka gwabza kazamin fada da 'yan ta’addan.

“A lokacin fafatawar, rundunar sojin sama ta OPFY ta bayar da bayanan leƙen asiri da kai hare-haren sama don tallafawa sojojin ƙasa, wanda ya haifar da gagarumin nasara.”

- Kyaftin Adewusi.

Sojoji sun kwato makamai da kayayyaki

A cewar Kyaftin Adewusi, an kashe wasu 'yan ta’adda da dama, an kuma kwato babura masu tarin yawa da na’urorin sadarwa.

Kayan da aka kwato sun haɗa da bindigogi kirar AK-47 guda biyu, gidan harsasai ɗaya mai dauke da harsasai kirar 7.62mm, da babura 18 tare da wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta yunƙuro, za a ɗauki mutane 2,500 aiki a kowace ƙaramar hukuma a Najeriya

Adewusi ya ce wannan harin ya dakile 'yan ta’addan daga cimma burin su na farmakar mutane da sace dabbobi a yankin. Sai dai ya ce wani soja guda ɗaya ya rasa ransa a fafatawar.

“OPFY ta kuduri aniyar kawar da 'yan ta’adda da masu aikata laifuffuka da ke addabar yankin Arewa maso Yamma da sassan Arewa ta Tsakiya."

- Kyaftin Adewusi.

Sojojin Najeriya sun kwato makamai da kayayyaki bayan sun fafata da 'yan ta'adda a Zamfara, Neja
Sojojin Najeriya tsaye a karkashin bishiya a wani dauki da ake zaton sun kai cikin garuruwan Arewa. Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda a Zamfara

A wani ci gaba kuwa, sojojin Operation Forest Sanity III sun kaddamar da sintiri daga ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara, ta Kaboro da Sangeko zuwa Makuku da Dankolo a jihar Kebbi, bisa bayanan leƙen asiri da suka samu a ranar 22 Yuli, 2025.

Sun haɗu da sojojin da ke FOB Rijau da Warari a jihar Neja, inda suka yi artabu da 'yan ta’adda, suka kashe da dama, sannan suka lalata babura 18.

A wani saƙo da rundunar soji ta wallafa a shafinta na X a ranar Laraba, ta bayyana cewa an kwato bindigogin AK-47 da gidajen harsasan su, sai dai soja ɗaya ya rasa ransa.

Sojoji, 'yan sanda sun fafata da miyagu

Kara karanta wannan

Tanka makare da fetur ta yi hatsari, ta kama da wuta kusa da gidan man NNPCL

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an tsaro sun hallaka akalla ’yan bindiga 30 a Faskari, yayin musayar wuta da suka yi da daruruwan ’yan ta’adda da suka kai farmaki.

Rahotanni sun nuna cewa fadan ya auku ne yayin da jami’an tsaro ke kokarin dakile hare-haren da aka kai kauyukan Kadisau, Raudama da Sabon Layi.

Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa sojoji biyu, ’yan sanda uku da wani farar hula sun rasa rayukansu a wannan artabu da ya yi sanadiyyar hasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com