Sojoji Sun Fatattaki Zugar 'Yan Ta'adda, An Aika kusan 95 ga Mahaliccinsu

Sojoji Sun Fatattaki Zugar 'Yan Ta'adda, An Aika kusan 95 ga Mahaliccinsu

  • Sojojin sama sun yi nasarar ragargaza wasu ‘yan ta’adda da yawansu ya kai akalla 95 a wani hari da suka kai a kauyukan Ragada da Warari
  • Tun farko, bayanan sirri ne suka sanar da sojojin cewa an hango zugar 'yan ta'adda da babura akalla 108 a jihar Neja bayan sun taso daga Zamfara
  • Mazauna yankin sun nuna farin ciki da godiya ga gwamnatin tarayya bisa kokarinta na kawo karshen ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta samu nasarar hallaka akalla ‘yan ta’adda 95 a wani hari da jami'anta suka kai jihar Neja.

An kai samamen ta sama yayin da 'yan ta'addan ke wuce wa ta kauyukan Ragada da Warari da ke karamar hukumar Rijau ta jihar Neja.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga a Neja, an samu asarar rayuka

Sojojin 'kasar nan sun samu nasara
Sojoji sun fatattaki 'yan ta'adda Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

The Guardian ta wallafa cewa jiragen yaki na NAF sun tarfa ‘yan ta’addan ne da misalin 3.00 na rana a ranar Talata, yayin da suke kan hanyarsu daga jihar Zamfara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun rugurguza 'yan ta'adda

21st Century Chronicle ta wallafa cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa ‘yan bindigar na kan hanyarsu daga yankin Zamfara ne zuwa jihar Neja ta hanyar Kebbi.

Binciken sirri da aka gudanar ya nuna cewa ‘yan ta’addan suna tafe ne da babura 108, tare da makamai masu hadari, kuma sun nufi yankunan Warari da Rijau na jihar Neja.

Wata majiya ta bayyana cewa:

“Jiragen yakin NAF sun kai musu hari a tsakanin kauyukan Ragada da Warari, a cikin karamar hukumar Rijau.”

Sojoji sun yi nasara kan ‘yan ta’adda

Rahotanni sun tabbatar da cewa daga cikin ‘yan ta’adda 108 da ke kan babura, babura 13 kacal ne suka tsere, sauran kuma an halaka su a harin sama.

Kara karanta wannan

Za a samar wa matasa miliyan 1 ayyuka ta hanyar noma a jihohi 22

sojojin Najeriya sun kai samame Neja
Sojoji sun samu labarin wucewar 'yan ta'adda a Neja Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa:

“Mazaua kauyukan Makuku, Warari da Ragada da ke karamar hukumar Rijau sun nuna farin ciki da godiyarsu ga gwamnatin tarayya bisa dagewar da take yi wajen yaki da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuffuka a yankin Arewa maso Yamma.”

Majiyoyi daga fannin leken asiri sun tabbatar da sahihancin bayanan da suka kai ga kai harin da ya yi sanadin wannan babban nasara.

'Yan ta'adda sun mika wa sojoji cin hanci

A baya, kun ji Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa dakarunta sun nuna jarumtaka ta hanyar ƙin karɓar cin hanci na Naira miliyan 13.7 da wasu ‘yan ta’adda suka ba su.

Mai magana da yawun hedikwatar, Manjo-Janar Markus Kangye, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin wani taron manema labarai da aka shirya domin bayani kan nasarorin da sojoji ke samu a fadin ƙasar.

A cewar Kangye, dakarun rundunar sun samu kiran gaggawa ne a ranar 9 ga Yulin 2025, dangane da wani abu da ake zargin yana da nasaba da ayyukan ta’addanci a hanyar Jos zuwa Sanga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng