Zamfara: An Shiga Tashin Hankali bayan Samun Gawar Malamin Musulunci a Mugun Yanayi

Zamfara: An Shiga Tashin Hankali bayan Samun Gawar Malamin Musulunci a Mugun Yanayi

  • Mutanen garin Dansadau sun wayi gari cikin wani irin yanayi marar dadi bayan samun gawar wani malamin Musulunci
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an samu gawar sanannen malamin addini, Malam Danladi Boss a wajen gari
  • An gano gawar a safiyar Talata 22 ga watan Yulin 2025 ba tare da wata alama ta fada ba, abin da ke nuni da yiwuwar kisa ne da gangan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gusau, Zamfara - Al'ummar garin Dansadau da ke jihar Zamfara sun wayi garin ranar Talata da abin takaici a yankin.

Mutanen garin da ke Maru a Jihar Zamfara sun tashi da labarin tsintar gawar Malam Danladi Boss.

An tsinci gawar malamin Musulunci
An samu gawar malamin Musulunci a Zamfara. Hoto: Dauda Lawal.
Source: Facebook

Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa marigayin malamin addini ne kuma shugaba a unguwar Asibitin Elejah.

Kara karanta wannan

Zamfara: Ƴan bindiga sun harbe shugaban PDP, an sace ɗan siyasa da wasu mutum 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan bindiga suka matsawa al'umma a Arewa

Jihar Zamfara da sauran jihohi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na fama da hare-haren yan bindiga babu kakkautawa.

Dalilin hare-haren miyagun ana rasa rayuka da kuma asarar duniyoyin al'umma duk da kokarin rundunar sojoji domin kawo karshen matsalar.

Duk da haka, rundunar sojoji tana ta bugun kirji cewa tana samun galaba kan maharan, lamarin da ke fusata jama'a duba da irin mugayen hare-haren da suke fuskanta a kullum.

Mutane sun firgita bayan samun gawar malami
Ana cikin firgici bayan tsintar gawar malamin Musulunci a Zamfara. Hoto: Legit.
Source: Original

An yaba da halayen kirki na malamin Musuluncin

An tsinci gawarsa a wajen gari cikin yanayi mai ban tsoro da alamar kisan gilla wanda ya kara jefa tsoro a zukatan al'umma a yankin da ke fama da hare-haren yan bindiga.

Wasu mazauna yankin da suka fara ganin gawar da misalin karfe 7:05 na safe sun ce alamar ta nuna an kashe shi ne da dare.

Sun bayyana cewa marigayin mutumin kirki ne kuma yana da natsuwa da son zaman lafiya inda suka koka kan dalilin yi masa kisan gilla babu hujja.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun dimauce da aka kai musu hari da dare, an sace shanu

Wani daga cikin mazauna yankin, ya ce:

“Shi mutum ne mai nutsuwa da zaman lafiya, ba mu san dalilin da zai sa a kashe shi ba."

Mutane sun shiga firgici bayan samun gawar malam

Labarin mutuwar Malam Danladi ta bazu cikin sauri, inda ya jefa al’ummar Dansadau cikin jimami da dimuwa matuka saboda kisan mutumin kirki a yankin.

Ko da yake Dansadau na daya daga cikin wuraren da ake fama da ta’addancin 'yan bindiga, kisan nan ya kara tsoratar da al’umma.

Yan bindiga sun harbi shugaban PDP a Zamfara

A wani labari mai kama da wannan, wasu yan bindiga sun kai mummunan hari a hanyar Manyaci zuwa Bukkuyum da ke jihar Zamfara a Arewa maso Yammacin Najeriya.

Yayin harin, yan bindigan sun bude wuta kan wata mota dauke da shugaban PDP na karamar hukuma, Hon. Muhammad Sala Wuta a hannu da kafa wanda yanzu haka a asibiti domin karbar kulawar gaggawa.

An sace mutane uku ciki har da Hon. Mu’azu Zannan Gwashi a yayin harin, lamarin da ya girgiza al’ummar Bukkuyum da kewaye, suke ta yi masa fatan alheri da samun lafiya cikin gaggawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.