Gwamnan Kano Ya Yi Zarra, Abba Ya Ƙara Samun Lambar Gwarzon Gwamnoni a Najeriya
- Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo ta gwamnan da ya yi fice a tsakanin takwarorinsa a fadin 'kasar nan
- Karramawar ta biyo bayan yadda gwamnatin Kano ta mayar da hankali a bangaren ilimi, inda ta ware kudi mafi tsoka ga sashen a kasafin kudinta
- Gwamnan ya sadaukar da lambar yabo ga al’ummar Kano, yana mai cewa wannan karramawa shaida ce cewa ana ganin aikin da ake yi a fannin
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya samu lambar yabo a matsayin gwamnan da ya yi zarra a shekarar 2025.

Source: Facebook
Jaridar Blueprint ce ta karrama gwamnan yayin taronta na shekara-shekara kan muhimman harkokin jama'a da tasirin shugabanci da aka gudanar a dakin taro na Ladi Kwali a Abuja.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Ba Gwamnan Shawara ta Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Ibrahim Adam, ya fitar, shi kuma Sanusi Bature ya wallafa a shafin Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Kano ya zama gwarzon shekarar 2025
Sanarwar ta ce an baiwa gwamna Abba Kabir Yusuf lambar yabo ne sakamakon jajircewarsa wajen inganta bangaren ilimi, inda ya ware kaso mafi yawa na kasafin kudin jihar na 2025 ga sashen.
A cewar wadanda suka shirya taron, gwamnatin Kano ta fito fili wajen mayar da hankali kan ci gaban dan Adam ta hanyar gyaran makarantun gwamnati da suka lalace.

Source: Facebook
Sun kara da cewa gwamnan ya kuma dauki nauyin karatun dubbunnan ‘yan asalin Kano a gida da waje don 'karo ilimi, da kuma daukar malaman da suka cancanta domin kara inganta koyo da koyarwa.
Gwamnatin Kano ta ji dadin karrama Abba
Gwamna Yusuf bai halarci bikin kai tsaye ba, sai dai ya samu wakilcin mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Sauran wadanda suka wakilce sun sun hada da Dr. Haladu Mohammed, mai ba Gwamna shawara kan sauya fasalin ilimi.
Haka kuma akwai Dr. Bashir Abdu Muzakkari, Darakta Janar na Hukumar Ci gaban Fasahar Sadarwa ta Jihar Kano (KANO-ITDA) da kuma Shugaban Karamar Hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Danmaliki.
Da yake jawabi a madadin Gwamna, Sanusi Bature ya mika godiyar gwamnatin Kano ga jaridar tare da sadaukar da lambar yabo ga al’ummar jihar.
Ya ce:
“Wannan yabo shaida ne cewa ana lura da abin da muke yi, kuma ana yaba mana. Hakan ya kara mana kwarin gwiwa mu ci gaba da gudanar da mulki cikin gaskiya, rikon amana da kyakkyawan niyya."
Gwamnan Kano ya zama gwamnan gwamnoni
A baya, mun wallafa cewa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya samu lambar yabo ta Gwamnan Afirka na Shekarar 2025 kan kyakkyawan tsarin gudanar da mulki.
Mujallar African Leadership Magazine (ALM) ce ta karrama shi a bikin bada lambar yabo karo na 14 a birnin Casablanca da ke kasar Maroko, inda manyan shugabanni daga kasashen Afirka suka halarta.
Mujallar ta ce an karrama Gwamna Abba ne sakamakon jajircewarsa wajen shugabanci na gaskiya da rikon amana, da kuma gudanar da mulki ba tare da nuna wariya ko bambanci ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

