Gwamnati Ta Yunƙuro, Za a Ɗauki Mutane 2,500 Aiki a Kowace Ƙaramar Hukuma a Najeriya

Gwamnati Ta Yunƙuro, Za a Ɗauki Mutane 2,500 Aiki a Kowace Ƙaramar Hukuma a Najeriya

  • Ma'aikatar harkokin gidaje da raya birane ta ƙirƙiro shirin da zai samawa ƴan Najeriya sama da miliyan 2 ayyukan yi a kananan hukumomi 774
  • Ministan harkokin gidajen, Arc Ahmed Ɗangiwa ne ya bayyana hakan a wani taro da kwamitin Majalisar Wakilai a Abuja
  • Ya ce gwamnatin tarayya za ta gina gidaje 100 a kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 774 da muke da su a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan harkokin gidaje da raya birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na da shirin samar da guraben ayyukan yi masu yawa.

Ɗangiwa ya ce gwamnatin ta tsara samar da ayyukan yi akalla miliyan biyu domin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa ta hanyar shirin Samar Gidajen ga Jama’a na Renewed Hope.

Kara karanta wannan

"An kusa fara ganin saƙon kudi," Gwamnatin Tinubu za ta fara biyan ƴan N Power kuɗinsu

Ministan harkokin gidaje da raya birane, Arc Ahmed Musa Dangiwa.
Gwamnatin Tarayya ta shirya samawa matasa miliyan 2 ayyukan yi a Najeriya Hoto: @Arch_Dangiwa
Asali: Twitter

Ya bayyana haka ne yayin wani taro da Ma’aikatarsa ta yi da Kwamitin Majalisar Wakilai kan Gidaje da Muhalli, a Abuja, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Ministan, Shirin Renewed Hope Social Housing an kirkiro shi ne domin samar da gidaje ga ƙananan ma’aikata masu ƙaramin albashi, marasa aikin yi, marasa galihu da kuma ‘yan gudun hijira.

Za samar da ayyuka a kowace ƙaramar hukuma

Ya bayyana cewa za a gina gidaje guda 100 a kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 774 da ke fadin ƙasar nan, wanda zai sama rda dubban ayyuka.

Ministan ya ƙara da cewa sama da ayyuka miliyan biyu za a samar a faɗin Najeirya.

Dangiwa ya ce za a biya kuɗin wannan shiri ne ta hanyar Asusun Raya Ababen More Rayuwa na Renewed Hope.

Haka nan kuma ya shaida wa kwamitin cewa za a basu cikakken bayani bayan Shugaba Bola Tinubu ya amince da takardun shirin NSHP, rahoton Tribune Nigeria.

Kara karanta wannan

Dangore ya fadi babban kalubalen da yake fuskanta a matatarsa

“Bayan fara aikin, za mu gabatar da kudiri a Majalisar Tarayya domin tabbatar da dorewar wannan shiri, ta hanyar kafa Asusun Gidajen Jama’a na Ƙasa,”
- inji shi.
Ahmed Ɗangita ya gana da ƴan Majalisa.
Ministan gidaje ya bayyana shirin gwamnati na samar da ayyukan yi a ƙasar nan Hoto: @Arch_Dangiwa
Asali: Twitter

Ɗangiwa ya faɗi matsalar da suke fuskanta

Ministan ya shaida wa kwamitin halin da ayyukan ma’aikatarsa ke ciki, yana mai cewa suna jiran kammala nazarin kasafin kudin 2025 daga Ofishin Kasafin Kuɗin Tarayya.

Ya bayyana cewa yawancin ayyukan biranen Renewed Hope Cities da gidaje sun kai matakin ƙarshe, inda ya tabbatar da cewa da zarar an saki kuɗi, za a kammala su a cikin wata biyu don miƙa su a hukumance.

Majalisa za ta haɗa kai da ma'aikatar gidaje

A nasa bangaren, Shugaban Kwamitin Gidaje da Muhalli na Majalisar Wakilai, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, ya jaddada kudurinsu wajen warware matsalolin ma'aikatar gidaje yadda ya kamata.

Ya tabbatar wa Ministan cewa duk matsalolin da ke akwai za a magance su nan ba da jimawa ba.

Kara karanta wannan

Ana rade radin zai shiga jam'iyyar APC, an hango Kwankwaso a fadar shugaban kasa

Kofa ya yi alƙawarin cewa ƙofar kwamitinsu a buɗe take ga ma’aikatar, kuma za su yi aiki tare cikin haɗin kai domin tabbatar da cewa ayyukansu sun amfani ƙasar nan.

Wani matashi da ke aikin gini, Aliyu Hashim ya shaidawa Legit Hausa cewa abin da ya fahimta waɗannan ayyukan irin nasu ne na birkiloli da lebura.

A cewarsa, matukar matasa ba za su sa girman kai ba, ana samun alheri sosai a wannan sana'a tasu kuma yana maraba da yunƙurin gwamnati.

"Ba kowane matashi ne zai iya yin waɗannan ayyukan ba, musamman ƴan Boko, amma aiki gini wallahi ana samun alheri, muna fatan mu amfana da wannan tsari," in ji shi.

Gwamnatin Tinubu za ta biya ƴan N-Power

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin biyan duka haƙƙoƙin matasa masu cin gajiyar shirin N-Power daga nan zuwa karshen 2022.

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya jagoranci taron sasanta Gwamnatin Tarayya da wakilan ƴan N-Power da lauya Abba Hikima.

Barau ya ce tattaunawar ta yi armashi, kuma an cimma matsaya cewa nan ba da jimawa ba ƴan N-Power za su fara ganin saƙon haƙƙoƙinsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262