Minista Ya Fadi yadda Najeriya Ke Tafka Asarar Naira Tiriliyan 21.1 duk Shekara
- Ministan kuɗi, Wale Edun ya bayyana cewa Najeriya na asarar dala biliyan 15 duk shekara sakamakon karkatar da kudaden haraji
- Edun ya ce hakan na hana gina asibitoci, makarantu, hanyoyi, da rage talauci, inda ya bukaci a dakile fitar da haramtattun kuɗaɗe
- Gwamnatin Bola Tinubu na gyaran haraji don gina tattalin arziki na cikin gida, ba da dogaro da bashi ba, inji Edun a taron IFFs a Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - A ranar Talata, ministan kuɗi da tsare-tsaren tattalin arziki, Mista Wale Edun, ya bayyana cewa Najeriya na asarar kusan $15bn (N21.1trn) a duk shekara.
Ya ce ana rasa wannan kuɗi ne sakamakon dabarun kaucewa biyan haraji da sauya wurin bayyana riba da manyan kamfanonin waje da ke kasuwanci a cikin ƙasar ke yi.

Kara karanta wannan
Gudumar majalisa za ta hau manyan gwamnati, za a hana su zuwa makarantu da asibitin kuɗi

Source: Facebook
Ana karkatar da harajin Najeriya zuwa waje
Arise News ta rahoto cewa kamfanoni na ƙasa da ƙasa na rage nauyin harajin da ke kansu ta hanyar matsar da ribarsu zuwa ƙasashe masu ƙarancin haraji ko wuraren ɓoyon haraji a irin wannan tsari.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministan ya bayyana hakan ne yayin buɗe taron ƙasa kan fitar da haramtattun kuɗaɗe (IFFs) da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Mista Wale Edun ya ce ana karkatar da kuɗaɗe masu yawa daga cikin ƙasar, lamarin da ke hana gwamnati samun damar amfani da waɗannan albarkatu wajen cika bukatun jama’a kamar samar da aiyukan jinƙai.
Tun da fari, shugaban hukumar FIRS, Dakta Zacch Adedeji, ya ce karkatar da kudade zuwa waje (IFFs) na ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke barazana ga zaman lafiyar kuɗin Najeriya.
Yadda Tinubu ke kokarin gyara tattalin arziki
A kan hakan, ministan kudin ya ce wannan matsala ta haifar da ƙarancin asibitoci, makarantu, hanyoyi da gadoji, da kuma ci gaban ‘yan sanda; har ma da shafar ƙoƙarin samar da ayyukan yi da rage talauci.

Kara karanta wannan
Ta faru ta kare, majalisa ta amince Tinubu ya kinkimo bashin Naira tiriliyan 32.2
Yayin da ya samu wakilcin karamar ministar kuɗi, Dakta Doris Uzoka-Anite, Wale Edun ya ce gwamnatin Bola Tinubu na aiwatar da gyare-gyaren kuɗi da suka shafi tattalin arziki.
Edun ya bayyana cewa gyare-gyaren na Tinubu na nufin gina tattalin arzikin da zai dogara da samar da kuɗi daga cikin gida, ba daga bashi ko taimako ba.
Ya ce fitar da haramtattun kuɗaɗe na daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban ƙasar da kuma kawo cikas ga ikon tattalin arziki na Najeriya.

Source: Twitter
Illar karkatar da haraji da kamfanoni ke yi
Yayin da ya jaddada bukatar kare dukiyar da ake samarwa a cikin gida, Edun ya bayyana fitar da kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba a matsayin “rumbun ɓoyon arzikin ƙasa”.
A cewarsa:
“Wannan al’amari na rage samun kuɗin shiga, yana lalata tushen haraji, yana karfafa cin hanci da rashawa, sannan yana rage kuɗaɗen da ya kamata a yi amfani da su wajen zuba jari a fannin lafiya, ilimi, ababen more rayuwa da kare marasa galihu.”
Ya ƙara da cewa amincewar Shugaba Tinubu da sababbin dokoki huɗu na haraji da aka gabatar kwanan nan wani ci gaba ne da bai taɓa faruwa ba a baya.
Edun ya ce dokokin sun shafi sauƙaƙe tsarin haraji, cire gibin dokoki, da kuma dawo da amincewar masu biyan haraji.
Najeriya ta yi asarar N13trn a shekaru 3
A wani labarin, mun ruwaito cewa, an kiyasta gwamnatin Najeriya ta yi asarar N13.2trn sakamakon aiwatar da tsarin tallafin musayar kudin waje a cikin shekaru uku.
Rahoton Ci Gaban Najeriya (NDU) da Bankin Duniya ya fitar ya bayyana cewa asarar ta wakana ne tsakanin shekarar 2021 zuwa 2023.
Tun da fari, ministan kuɗi, Wale Edun, ya sanar da cewa gwamnati ta daina bayar da tallafin fetur da kuma na musayar kuɗaden ƙasashen waje don takaita assarar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
